MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

K’arfe 12 yasamu shigawo gida domin bai baro gombe da wuri ba,wanka yafara yi yasaka k’ananan kaya na bacci sannan yafita zuwa part din Hanan domin ganin yanda jikin nata yake tunda lokacin da umma ta kirashi awaya tace masa jikin Hanan din ya dan tsananta,

Kamar koda yaushe wani sanyayyen kamshi ne yafara yimasa maraba lokacin da yashiga falon nata,kai tsaye bedroom dinta yabude yashiga,tashinta kenan tana zaune tsakiyar gado ta jingina tana tunanin ta yanda zata sauka domin ta hado tea saboda yunwa kuma take ji,

Kamar wanda baya so haka ya karasa gaban gadon fuskarshi babu yabo babu fallasa, sunkuyar da kanta kasa tayi saboda tsoro da kwarjinin shi take gani,

“Ya jikin?” Taji ya fada yana tsaye yakama kugunshi ya rike,

“Da sauki…” Ta fada muryarta adashe sakamakon yawan kukan da tayi,

“Me yafaru naganki a zaune kuma?”

“Yanzu natashi tea nake son zan sha….”

Dan shiru yayi sannan ya kalleta,

“Zaki iya zuwa ki hado ne?”

Kai ta girgiza masa batare da ta kalleshi ba,

Juyawa yayi yafita ya sauka k’asa,tea din ya tsiyaya cikin cup ya hada mata yaji madara da milo sosai dan ba karamin kauri yayi ba sannan ya daukar mata snacks yakoma sama,har lokacin ta zaune kamar yadda take dazu,

Mika mata yayi ya nemi wuri ya zauna gefen gadon domin sai yaga ta rame sosai,to ko dama tajima tana zazzabin ne bai saniba? Harga Allah bata son tea dinnan da ya hado mata saboda yasaka madara ita kuma saboda zazzabin da take yi bata ko kaunar taji karnin madarar gashi yazuba da yawa da ace itace zata hada to da ruwan bunu zata hada tasha shi bak’i,daurewa tayi kawai tafara sha ahakan tana rintse idanu,tasha yakai rabi ta yunkura zata ajiye ya kalleta,

“Wa kika ragewa wannan din? Shanyeshi” 

Jin abinda yace yasata fasa ajiye cup din taci gaba da sha tana jin zuciyarta tana tashi amai yana taso mata, yunkurin amai ne ya addabeta har bata san lokacin da ta rikeshi ba saboda babu tazara sosai tsakaninsu,tare ta wankesu da aman wanda yaki karewa domin gaba daya tea din da ta sha sai da ta amayar dashi, lokacin da tagama aman jikinta duk ya saki babu karfi ko kadan,lagwaff ta sakeshi ta kwanta tana jin wani sabon zazzabi na shigarta,mikewa yayi yafita, bedroom dinshi yaje ya wanke jikinsa ya sauya kaya sannan yadawo tana nan kwance kamar yadda yatafi yabarta,

Baida zabin da yawuce ya gyara ta ya tsaftace wurin da ta bata, tunanin ta inda yadace yafara yayi nan yafara da kan gadon sannan ya dagata itama,tana son tayi masa gardama amma kuma tana tsoro domin yau akwai wani kwarjini na musamman akan fuskarshi,yar doguwar rigar jikinta ya cire ya goggoge mata jikinta sannan ya bude drawer dinta yaciro mata wata,tun dazu ya lura da ita sai faman kakkare kirjinta take yi tanata bobboyewa ko ta manta da yataba ganinta ahakane oho? Amma wanne dare ne wanda jemage bai ganiba ya furta hakan acikin ransa,yana gama saka mata rigar ta tukunkune taja bargo ta rufe jikinta tana rawar dari,

Sai da yagama tsaftace duk wurin da ta bata da aman sannan yafita zuwa sashensa, kwanciya yayi amma ba bacci yake ba,bayan kamar mintuna 30 yasake tashi yafita yaje ya dubata,bacci ya samu tanayi dan haka yakoma sashensa shima ya kwanta zuciyarshi cunkushe da tunani iri iri…………………………..鉁嶐煆?

_Wannan littafin na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎

8/14/20, 10:15 AM – Ummi Tandama: 47

***Haka yaci gaba da jinyarta amma koda yaushe fuskarsa ahade babu fara’a alhalin ita kuma bata san abinda tayi masa ba shikuma yaki yasanar da ita sai faman fushi yake yi,

Duk abinda tace tana so yana mutukar yin duk iya iyawarshi wurin nemo mata amma fa tsakaninta dashi babu sakin fuska dan komai yana yine kamar irin anyi masa dole dinnan,

Kwananta biyu akwance ta dan fara samun sauki,itama gaba daya acike take dashi sakamakon auren da taji zai yi kuma wai anty maamy zai aura,tana ta son ta kira abokan shawararta su dan tattauna su bata shawarar da ta dace amma babu waya a hannunta kuma tsoron tambayar Khalil take yi,rasa yanda zatayi tayi daga karshe sai umma barira ta samu da maganar lokacin ita kadaice adakinta tana sauraren fm radio shi kuma Aryan yatafi makaranta,tashi zaune umma tayi daga kishingiden da take sannan cikin alamun tausayawa da tausasa harshe tace,

“Kiyi hakuri Sa’adatu,tabbas kishiya nada ciwo kuma tana da zafi shiyasa ba kowacce mace ce take iya cin rabarta ba, da yawa mata a kishiya jarrabawar su take sai dai amma basu fiya cin wannan jarrabawar ba saboda gajen hakuri da kuma hawa dokin zuciya….. Idan akayi hakuri kuma aka kai zuciya nesa wallahi ba kishiya ba ita kanta rayuwar gaba daya mai wucewa ce,kina zaune mijin zai dawo ya sameki kuma har ma ki zama alkali atsakaninsu amma fa sai kin kai zuciyarki nesa, mutukar baki nutsu kin kama mutuncin kanki ba to a irin wannan gabar ne miji yake rainaki,danginsa suke rainaki,kishiya take rainaki,ke hatta sauran abokan arziki rainaki sukeyi mutukar baki ja girmanki kin yiwa fushinki da zuciyarki linzami ba,shi wannan zafin kishin da kan tasowa mata a lokaci guda shine ke sanadiyyar sasu aikata abinda zasu zo suna nadama da dana sani tsawon shekaru dan da yawan mata a wannan lokacin suke barin damarsu,miji yayita rarrashinsu amma suna fandarewa har shima yagaji yayi watsi dasu daga karshe idan ba ayi sa’a ba shikenan ansamu hanyar lalacewar zamantakewar da aka gina shekara da shekaru…..”

Sake gyara zama umma barira tayi sannan ta fuskanci Hanan,

“Shawarar da ni dai zan baki ‘yarnan shine….. Kishiya bata cinye uban kowa ba kuma kema bafa zata cinyeki ba,kiyi hakuri kici gaba da kyautatawa mijinki,nima na zauna da ita nasan zafinta kuma nasan ciwonta amma da nayi hakuri wallahi komai sai da ya zamto tarihi,to kema haka taki zata zama tarihi kamar ba ayiba…….” 

Jijjiga Kai Hanan tayi alamar gamsuwa da bayanan umman shiyasa neman shawarar manya amafi yawan lokuta take da dadi domin ko basu magance maka matsalarka ba zasuyi maka bayanin da kai kanka sai kaji dadi zuciyarka tayi sanyi,

“Nagode umma kuma insha Allah zanyi yanda kika ce……”

Cigaba da bata shawarwari umma tayi har tsawon wani lokaci kafin ta tashi ta shiga kitchen domin dorawa Khalil abinci ada tayi fushi tace bazata sake yimasa girki ba sai dai wacce zai auro din idan tazo ita taci gaba dayi masa amma kalaman da umma tayi amfani dasu wurin bata shawarwari sune suka sanyaya mata zuciya har taga rashin dacewar hakan ta sauya shawara,

Tasan daga shi har dan gaban goshin nasa zasuyi farin ciki da abunda zata girka musu yau shiyasa ta bada himma ta zage wurin ganin ta nuna kwarewarta a wannan fannin,

Zuwa yamma ta kammala komai nata suna tare da Aryan a falonta suna yin game,kokari takeyi taga tayi yaki da duk wani bacin rai tare da damuwa dake kokarin yiwa zuciyarta tsinke har yasamu wurin zama wannan dalilinne yasa take ta biyewa Aryan suka taru suka zama mashirmata.

 Tun kafin Khalil yadawo ta shirya masa table bayan ta gyare masa sashensa tsaf yasha turaren wuta dan sudan mai bala’in kamshi,bayan sallar ishah yasamu zarafin dawowa kasancewar yau yaje garin zamfara ya halacci wani taro,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button