MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

Kamar yadda yasaba wanka yafara yi yashirya cikin kananan kaya sannan yafito falo hancinsa na shakar kamshin turaren da Hanan ta saka masa sannan wani abun sha’awar shine yanda ta kawata table din sannan ta armasa shi da warmers masu kyau kanana,zama yayi yana budewa nan yaga funkaso ne yatashi sosai sannan yayi kyau sai miyar agushi tasha alayyahu itama tayi kyau sosai tun a ido gashi ta wadatu da naman kaji,sai lafiyayyen zobon da ta hada wanda yaji flavors daban daban ya wadatu da kankana da cucumber aciki,zuba funkason yayi yafara ci wanda yayi daidai da shigowar Aryan cikin falon, cinyarshi ya haye shima yasaka hannu yafara cin funkason wanda tunda aka sauke yake ci amma yakasa koshi gashi kuma baiyi wani auki sosai ba dan hatta umma ma saida ta bukaci kari akan guda hudun da Hanan ta zuba mata shi kansa Khalil din kwaya uku yasamu,

“Abba na ba kaci naka bane? Wannan fa nawane nima zanci…..”

Makale kafada Aryan yayi yaci gaba da ci yana surutu,

“Nima zan kara ci uncle…….”

Tare suka cinye sannan Aryan yafice,shikuma zama yayi nan falonshi aranshi yana tunanin to ko menene kuma yafaru da Abba Idris ke nemanshi? Dan dazu yayi masa text massage akan yaje gombe yana son ganinshi gobe yasan dai baya wuce maganar aurensu shida maamy,wayarshi yatashi yashiga bedroom dinshi yadauko yafito yasoma kiran layin maamy amma number busy,ajiye wayar yayi saboda yasan idan tagama zata kirashi amma kuma ga mamakinsa har ya kwanta bacci bata kirashi dinba shima kuma bai sake kiranta ba. Washe gari asubanci yayi yafita ta can office yawuce gombe domin amsa kiran Abba Idris wanda yake matsayin uba agareshi,

Bayani cikin nutsuwa abba Idris yayi masa akan maganar aurenshi da maamy cewa tsohon mijin maamyn wai yadawo yanata bibiya sai takoma d’akinta kuma dama tun farko matsalar ba daga gareshi bane daga mahaifiyar shi ne dan haka shi Khalil yayi hakuri yabarwa Abban jawad domin mammy takoma gidan tsohon mijinta,dama Khalil yasan za arina kuma za ayi haka dan tunda yaga take taken tsohon mijin mammy yasan da wata akasa,duk da baiji dadin abinda yaji ba amma godiya yayiwa Abba kuma yanuna baiji zafi ko ciwon abinda yafaru ba sai dai har acikin ransa baiji dadin boye masan da mammy tayiba shi baya son boye boye da nuku nuku cikin sha’aninsa koda yaushe yafi son mutum yazama open amma babu komai dan koba alaka ta so maamy ai yar uwarsa ce ta jini, sallama yayiwa abba yatafi batare da yashiga cikin gidanba.

Wannan al’amari shine sanadin rushewar maganar aurensa da maamy wanda ita Hanan bata saniba duk atunaninta maganar aure har yanzu tana nan daram shiyasa taci gaba da kyautata masa da yimasa duk wani abu wanda zai faranta ransa,ranar da aka daura auren mammy sai ranar Hanan tasan anfasa auren da Khalil dan abakin umma barira taji bayan umman sun gama waya da hajiyarsu Khalil,wani sanyi da annuri da farin cikine yarinka ratsa zuciyar Hanan da kuwa duk zuciyarta ta shiga cikin wani hali,babu bata lokaci ta shiga cikin kitchen domin jinta take yi awartsake yanzu,tuwon dai nasu na gado ta dora musu shida Aryan saboda basa gajiya dashi nan ta lailayashi tayishi lafiyayye miyar busasshiyar kubewa mai tsananin yauki wacce tasha kifi wadatacce,man shanu ta soya bayan ta sauke girkin,

Tun kafin Khalil din yadawo su umma ke santin wannan tuwon ita da Aryan ita dai Hanan dariya kawai tayi ta haura sama,bayan sallar magriba Khalil din yadawo daga gombe amutukar gajiye ga wata yunwa dake ciciyarshi,kayan jikinsa ya sauya daga manya zuwa kanana sannan yazo yahau table nan yafara kwasar girkin Hanan wanda ke barazanar cire masa kunne dan tsabar dadi,yana dab da kammalawa Hanan tashigo itada Aryan wanda ta sakoshi agaba wai ya tayata tambayar Khalil wayarta da yarike ya hanata tun sati biyu zuwa uku da suka gabata,

Ganin sun hade kai yasashi kallonsu yana cigaba da cin tuwonsa,

“Papa…..”

Kallon Aryan yayi sannan yakai laumar tuwon da ya debo,

“Menene?”

Kallon Hanan yayi sannan ya kalli Khalil,

“Mommy infada?”

Girgiza masa kai tayi,

“Kabari har sai yagama cin abinci tukunna”

“Kai fadi….. Menene?”

“Uncle mommy ce tace wai kabata phone dinta….”

Yaji abinda Aryan din yafada sarai amma sai bai kulasu ba kawai yaci gaba da cin abinsa har ya kammala lokacin tuni har lokacin sallar ishah yayi dan haka bai zauna a falonba yamike zuwa cikin bedroom dinshi hakan ya tabbatarwa da Hanan cewa bazai bata ba shiyasa kafin yafito ta tashi tafita shikuma Aryan yabishi zuwa cikin bedroom din tare sukaje salla suka dawo,itama sallar taje ta yi,bayan ta idar ta na zaune kan abin salla Aryan yashigo yace taje Daddy yana kiranta,tashi tayi batare da ta cire hijabin jikinta ba tabishi suka tafi,

Yana hakimce kan sofa ya dora kafarshi daya akan center table yana ta faman yimata bincike awayar tata,zama tayi akujerar dan nesa dashi kadan,

“Me kuke cewa dazu keda d’anki?” 

Taji yafada har lokacin idanuwanshi na kan wayarta yana ta faman yimata bincike ita dai fatanta Allah yasa kar ya kalle mata sirrin da ta ajiye a WhatsApp,dan duk ranar da hajja hasinah tayi posting din abu mai amfani starring dinsu takeyi ta adana bata gogewa,

“Baki jine?”

“Inaji….. Cewa nayi ka taimaka kabani wayata zanyi amfani da ita gida…..”

Bai amsa mata ba har tsawon mintuna biyu sannan cikin alamar tuhuma taji yace,

“Waye mujahid?”

Sosai tambayar tabata mutukar mamaki sannan lokaci guda saima ta nemi amsar da zata bashi ta rasa dan sai ta kasa gane wayema mujahid?

“Ina tambayar ki waye mujahid?”

Shirun taso sake yi amma kuma ganin ya tsareta da idanuwanshi mayalwata yasata yin kasa da kanta sannan tace,

“Dan makarantar mu ne…”

“Kar kiyi min karya dan already nasan gaskiya,kawai ina son sake tabbatarwa ne,wayeshi?”

Ji tayi yawun bakinta na neman kafewa,

“Ya taba cewa yana sona……”

“Tsohon saurayinki ne kenan?” Taji yafada bayan yaja wasu sakwanni,

“Uhmmm”

“Bai san kinyi aure bane?”

“Yasani…”

“Ok”

Daga nan cigaba yayi da tambayar contacts dinta kusan kowa sai ya tambayeta waye shi sai dai abinda yabata mamaki shine sam bai tambayeta waye wannan wanda yake turo mata text massage dinba ko bai ganiba? 

“Ita wannan hasinah din itace malamar ku kenan?” Taji yafada babu zato babu tsammani, sunkuyar da kanta kasa tayi tana jin kunyar duniya na lullubeta saboda tasan yaga abinda taketa addu’ar Allah yasa kar yagani,

Baiyi mata maganar ba ya mika mata wayarta bayan ya gama karanta duk abinda idonshi yasauka akai,

Hannu biyu tasa ta karba ta tashi tafita cike da murna tana zuwa part dinta ta saka wayar a charge tashiga wanka,bayan tafito tagama shirin bacci ta dauki wayar ta kunna data ta leka WhatsApp domin sosai tayi missing dinshi shiyasa har 12 saura takai yau a online,kai ashe waya ma rahama ce bata san da haka ba har saida Khalil ya kwace mata wayarta.

Washe gari Khalil yabar kasar yatafi k’asar Rwanda,tunda yatafi kuma ta shiga missing dinshi har ta kasa hakuri sai da ta tura masa massage,

Yana kwance adaki har yafara bacci yaga massage din nata murmushi yayi ya mayar mata da reply,

_Me kika fi missing atare dani?_

Itama murmushin tayi lokacin da taga tambayar da yayi mata saima ta rasa amsar da zata bashi dan haka tayi shiru kawai. Satinshi daya yadawo,aranar da yadawo bai shigo gidanba sai dare bayan duk sunyi bacci washe gari da safe yatafi gombe bayan yadawo da daddare yakira Hanan falonshi,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button