Labarai

Na Azurta Sama Da Mutum 2000 A Jihar Kogi – Yahaya Bello

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce gwamnatinsa ta maida aƙalla mutum 2,000 sun zama Miliyoniyoyi a jihar inda ta tsame su gaba daya daga talauci.

Ya yi wannan furucin ne a wurin taron ƙara wa juna sani game da manufofin sa a siyasar Najeriya karo na biyu wanda ke gudana a Abuja.

Yahaya Bello ya kuma bayyana shirinsa na zaɓar mace ta farko a matsayin mataimakiyar shugaban ƙasa idan APC ta lamunce masa ta bashi tutar takara a zaɓen 2023, kuma ta amince ya zaɓi wanda zasu tafi tare.

Yayin da yake amsa tambaya kan tsarinsa game da tattalin arziƙin kasar nan, wanda ya haɗa da alƙawarin maida yan Najeriya miliyan 20 miliyoniyoyi zuwa 2030 idan ya gaji Buhari, gwamna Bello ya ce:

“Mun maida mutane mafi ƙaranci mutum 2,000 sun zama Miliyoniyoyi a jihar Kogi.” Haka nan kuma game da wanda zai zaɓa su yi takara tare a matsayin mataimakin shugaban ƙasa, Bello ya ƙara da cewa: “Idan aka bani damar na zaɓa da kaina, ba zan kauce wa tsagin jinsin mahaifiya ta ba. Zan so na tafi da mace ta farko a matsayin mataimakiyar shugaban ƙasa a 2023.”

 

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button