NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Wannan yarinyan tana da kyau.. Ina kika sameta?…” Ta tambayi Hajiya Aisha, Dariya Hajiya Aisha tayi ta labarta mata yanda akayi ta samu dija,
“To alhamdulillah… Yanzu bari in baki address dinsu dukda gidansu ba boyayye bane a garin Kano…” Nan ta rubuta mata address, ta mika mata, Sannan tace
“Bari in dauko maki NA mai…” ta fada tana hayewa upstairs, dija dai kanta kasa gabanta ne Kawai ke faduwa saboda tsoro, few minutes later ta sauko da bandir din Dari biyu ta Bata,
“Wannan ai yayi yawa…” Inji Aisha, Dariya tayi
“Inafa…ai kinyi kokari…ki gaida manasu dukda muna da biki nan gidan…”
“Kanwar taki ce zata aurar?..” Kai ta girgiza mata
“Dan abokiyar zamanta ne zaiyi aure ….” Ta fada mata
“To Allah yasa ayi a saa… Bari mu tafi tunda muna da tafiya gaban mu…” Ta fada tana jefa kudin cikin bag dinta tare da mikewa. Nan sukayi sallama Sannan suka kama hanyan Kano
[3:14PM, 3/20/2018] 鈥�+234 806 125 0020鈥�: 馃挋馃挌馃挍馃枻鉂ゐ煉�
NA CUCE TA
馃挋馃挌馃挍馃枻馃挏鉂�
庐zuwairat(ummu Maryam)
7鈨�
Ko uffan dija batace ba har suka iso garin Kano,Hajiya kallon ta tayi ta fara Bata new advice har suka iso kofar wata katuwar gate, gaban dija kara faduwa yayi ta Dan leko da kanta tana kallon gate din da Hajiya ke horn a bakinta, wani ne ya leko ya kalli motan yaga mace ce da wata yarinya ya koma ciki Sannan ya bude gate din don ba kowa ake bari ya shiga gidan ba saboda tsaro, ahankali Hajiya shiga gidan itama tana mamakin girman gidan,
“Hmm gaba da gabanta…” Ta fada cikin ranta, ahankali tayi parking motanta a available space dake wurin ta fito tana kalle2, fadin girma da haduwan gidan is a waste of time amma ko motocin gidan Kawai are enough, Manyan gidaje six ke da akwai wurin, hakan yasa Hajiya Aisha ta rasa inda zata shiga, dija kam boyewa tayi bayan Hajiya tana kallon gidan, mai gadi me ya nufota da murmushi fuskan shi, gaidata yayi ta amsa sannan Hajiya tace
“Dan Allah bangaren Matan gidan zakanuna min…”
“Wacce daga cikin su?..” Mutumin ya tambayeta
“Karama matar…” Ta amsa mashi, nuna mata gidan dake middle yayi yace
“Nan ne…” Ya fada mata Sannan ya kokma duty post dinshi su Hajiya suka nufi inda aka nuna mata, ita kanta Hajiya Tasan tunda take kai yara gidan aiki Bata taba zuwa gidan da yayi Rabin wannan ba wajen girma da kyau, dija kam tafiya take amma tamkar an rike mata kafa, ahankali ta dinga takawa tana kare kanta da Hajiya Aisha dake gabanta, bakin kofan ta Hajiya ta tsaya ta danna wata bell, few minutes later wata budurwa ta bude ta gaidasu, amsawa Hajiya tayi Sannan tace
“Hajiya tana ciki?…”
“Eh…Ku shigo…” Yarinyan ta fada masu tana komawa gefe, cikin falon suka shiga sanyin ac ya bugi dija nan take taji kaman tana fever, tafiya ta dingayi a hankali don kar tiles ya kwaceta, Hajiya zama tayi dija ta zauna kasa kanta kasa heartbeat dinta NA kara highing by the minutes, Hajiya kam baki ta bude tana kallon ikon Allah tana mamakin yanda aka tara abun duniya waje daya, budurwan data bude kofan ce ta kawo drink da wasu elegant cups biyu ta ajiye Sannan tace
“Bari in kirawo ta….” Ta fada tana barin wurin, Hajiya kallon dija tayi
“Dija kinyi saa… Ban taba kai yarinya irin wannan gidan ba…sai kiyi ladabi ki bi doka ki ci arziki….” Ta fada mata kasa2 tana tsoron kar CCTV ya dauki maganar ta don tasan baa rasa sawa cikin irin wannan gidan. Bayan minti kaman biyar Yarinyan ta dawo tace
“Gatanan zuwa…” Ta fada masu Sannan ta bar falon. Sunfi minti goma shabiyar zaune Sannan Hajiya karama ta fito da faraa fuskan ta, gaisawa sukayi Sannan Hajiya karama tace
“Kece Hajiya Aisha?..” Ta tambaya
“Eh nice…Kuma wannan itace Yarinyan da kikace a samo maki….” Ta fada tana nuna dija dake lankwashe kasa, sai lokacin dija ta gaidata muryanta na rawa
Hajiya karama kura mata ido tayi tana kallon ta Kuma tana mamakin kyauwunta,
“Lafiya lau..Wallahi I thought she’s your daughter… Ah ina kika samo wannan beauty…” Tafada cikin raha kaman sun Dade da sanin juna da Hajiya Aisha, Dariya kawai tayi , Hajiya karama kallon yanda dija ke nonnokewa Kawai tayi ta saki Dariya
“Ya sunanki?…” Ta tambayi dija
“Kha…fi…ja…” Ta fada kanta kasa don ko sau daya Bata daga kai ba,
“Ah…ah…ah….sunan hajiyar mu gareki Ashe…kice NA samu sabuwar uwa….” Tafada cikin Dariya, itama Hajiya Aisha Dariya tayi hankalin ta kwance da Hajiya karama Bata nuna batason dija ba,
“Asabe!… ” ta kwala kira, sai ga yarinya data bude masu kofa ta dawo ta durkusa gaban Hajiya karama,
“Ga sabuwar mai taimaka maki an kawo…ki.tafi da ita dakinki…” Ta umarceta, Dariya jin dadi budurwa da bazata wuce shekara sha takwas ba tayi tana nuna jin dadinta karara da samun mai rage mata aiki,
“Taso…” Ta fadawa dija, ahankali dija ta mike jikinta na rawa, sai lokacin ta daga kai ta kalli Hajiya Aisha Kawai sai ta fara hawaye, don Kawai sai taji gidansu take so,
“Ah…ki bar kuka…nan ma gidanku ne kinji?..” Hajiya karama ta fadawa dija, da Sauri dija ta hadiye kukan ta fara takawa ahankali tana bin bayan asabe, Hajiya karama kallon ta kawai take don kallon yar gidan manya kawai take mata don ko kadan Bata kama da yar talakawa, saida suka bar falon Hajiya karama ta kalli Hajiya Aisha
“Amma wannan yarinyan zata Iya aiki kuwa?… Naga she’s a little bit dull…” Dariya Hajiya Aisha tayi Sannan tace
“Sosai kam Hajiya…Kawai yanzu kunya take ji..amma ina tabbatar maki.babu abinda bazata iyaba…”
“To shikenan.. Nawa ake biyan yaran da kike kaiwa gidan aiki?…” Hajiya karama ta tambaya, murmushi Hajiya Aisha tayi tace
“Ai duk yanda kika bada daidai ne…”
“To shikenan…masu aikin mu dubu talatin ake basu duk wata ga baki dayansu don haka zaa din biyanta….” Wani irin dadi Hajiya Aisha taji don tunda take kai yara gidan aiki babu inda ake biyan dubu ashirin balle talatin
“To shikenan… Hakan yayi sosai….” Inji Hajiya Aisha,
“To sai ki bada account number in bada a bawa manager kar a manta da albashinta…” Da Sauri Hajiya Aisha ta dauko Biro da paper ta rubuta ta mikawa Hajiya karama Sannan tace
“Ina yaran ne?..” Ta tambayeta
“Suna chan bangaren babban mominsu….bari in sa a hada maki wani abu naci….” Inji Hajiya karama,
“Na gode kwarai… Tafiya zanyi don inason in shiga kasuwa kafin in koma katsina….”
“Haba da wuri haka?… Haba ki bari sau gobe mana…” Injin Hajiya karama,
” sai in NA sake dawowa in Allah ya yarda…” Ta fada tana mikewa,
“Ina zuwa…” Hajiya karama ta fada mata Sannan ta bar falon bayan yan mintuna goma tadawo da wata katuwar Leda dauke da manyan atampa guda uku sai perfumes, sai kudi cikin envelope
“Gashi a rabAwa yan gida…” Hajiya karama ta fada tana mika mata ledan
“Har da wata hidima?… Gaskiya NA gode…Allah ya aka da alkhairi… Allah ya kara girma…nagode kwarai…” Ta fada cikin jindadi,
“Babu komai… Bari muje in kaiki gurin uwargidata Ku gaisa kafin ki wuce…” Hajiya karama ta fada tana shige mata gaba, bayanta Hajiya Aisha tabi har falon da yaran gidan ke wasa ita Kuma Hajiya babba zaune kan kujerana alfarma tana kallo zee aflam, da sallama suka shiga Hajiya karama ta shaidamata an kawo mai aikin. NaN suna gaisa Sannan Hajiya Aisha ta tafi bayan itama Hajiya babba ta Bata atampa da turare.
Dija baki ta bude tana tafiya ahankali tana waige2 har asabe ta bude dakinta suka shiga, dija tsayawa tayi tana kallon ikon rabbi don dakinta katuwa ne Sannan ga katon gadon da ko amaryan garinsu Bata isa ta mallakesu ba,