NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ki zauna mana…” Asabe ta fada mata amma dija bataji ba saboda yanda take kallon ceiling din dakin, kallon katon madubin dake jikin bango tayi ta tsaya tana kallon kanta, sai yanzu ta gan kanta sosai yanda take so, kallon kayan shafan dake kan mirror tayi ta dauke kanta ta kalli wata katuwar bag dake dakin

“Ki zauna mana..” Asabe ta fada tana Dariya,sai lokacin dija ra dawo hayyacinta ta kalli asabe dake dariya, sauke kanta kasa tayi tana murmushi,

“Ya sunanki?…” Ta tambayeta sounding friendly.

“Di…ja….” Ta amsa mata,

“Ni sunana asabe…sannunki da zuwa yaruwa…daga wane gari kike?…” Ta tambayeta,

“Baude….” Dariya asabe tayi

“Inane Baude?….” Dija dai shuru tayi don batasan abinda zata fada mata ba

“Ni yar dala ce…shekaranki nawa?…” Asabe ta sake tambayanta, shuru dija tayi kaman mai tunani Sannan tace

“Sha uku ko hudu…” Idanauwa asabe ta zaro

“Shine kike da tsawo haka?…wallahi nayi tunanin shekarunmu daya…Ashe ke yarinya ce…bari in dauko maki abinci….” Ta fada Sannan ta mike, fita tayi daga dakin dija ta kara mikewa ta nufi wajen split air conditioner, sai kallon abun take hannun ta ta kai wajen taji wani irin sanyi NA ratsa hannun ta, da Sauri ta dauke hannun ta takoma ta zauna har lokacin bata bar kalle2 ba. Rice and stew cike da kifi asabe ta shigo dashi ta ajiyewa dija sai ta bude Dan karamin fridge dake dakin ta dauko ruwa ta ajiye mata

“Bisimillah….” Asabe ta fada mata, da Sauri dija ta sauko kasa ta zauna ta fara cin abincin tana kara godewa Allah, daman dija Bata wasa da cikinta sai gata ta cinye abincin tas Sannan ta sha ruwa, asabe sai kallon ta tana murmushi don haka nan taji tana son dija. Sai da dija ta gama cin abincin Sannan asabe ta fara fada mata ayyukan da zasu dinga yi, itadai dija sauraron ta kawai take tana lumshe idanuwa saboda sanyin dake ratsata daman batayi bacci ba jiya

“Ko zakiyi bacci ne?..” asabe ta tambayeta da Sauri ta girgiza mata kai, Dariya asabe tayi

“In zakiyi bacci ki kwanta kafin…” Bata idaba wayanta ya fara ringing da Sauri tayi picking, shuru tayi tana sauraron abinda Hajiya karama ke fada mata

“To…” Ta amsa Sannan ta ajiye wayan ta kalli dija,

“Hajiya ta ce in kawoki bangaren Hajiya babba,…” Ta fada mata, da Sauri dija ta mike itama asabe ta mike suka fito zuwa part din Hajiya babba, sallama sukayi suka shiga kan dija kasa hannun ta rike da junansu duk yan yaran dake wasa Tare da yanmatan dake kallo kura mata ido sukayi. Durkusawa tayi ta gaidasu har da yanmatan, kallon juna sukayi suka tuntsure da Dariya suna kallonta with adorations, itama Hajiya Dariya take, rarrafawa tayi wajensu Hajiya ta kara gaidasu suka amsa suna Dariya

“Amma wannan yarinyan da abun Dariya take…” Inji Hajiya babba dake dariya, har lokacin dija na nan durkushe kasa itama asabe Dariya take, marzuq da Ameera ne suka ce

“Small mom wannan mai aikice?…” Ihsan ce ta buge masu baki, sukayi shuru don yana daga cikin tarbiyan yaran gidan basu raina maaikatansu,

“Ku koma…” Hajiya karama ta fada masu, sai lokacin dija ta mike suka koma part din Hajiya karama marzuq da Ameera NA biye dasu suna kallon dija kaman madubi don duk a masu aikin gidansu babu mai kyauwun ta, kitchen suka shiga tare dija ta bude baki, su Ameera NA biye dasu har cikin kitchen sai cewa tayi

“Tea zan sha….” Inji Ameera,Dariya asabe tayi tana cewa

“Sarauniyar shan tea…” Ta fadawa Ameera dake yar shekara 8 amma tana abu kaman yar shekara uku saboda sangarta, cup asabe ta dauko zata hada mata tea sai cewa tayi

“Bake zaki hadamin ba…ki bari ita ta hada min…” Ta fada tana nuna dija,

“To kinji da ke take…” Asabe ta fadawa dija, Dan matsawa dija tayi kusa da asabe Sannan tace

“Meye hakan?…” Ta fada cikin whisper, cup asabe ta mika mata, ta kaita ta zuba ruwa Sannan ta bude mata katon tin NA milk da Ovaltine, ta dauki spoon ta mikawa dija Sannan ta umarceta data hadasu cikin cup, yaran sai kallon su suke suna Dariya tana gamawa ta mikawa Ameera ta amsa Sannan suka bar kitchen din.

Hajiya Aisha NA fita ta duba envelope din da Hajiya karama ta Bata taga  mint na Dari biyar, dadi taji tana cewa

“This is what am taking about…” Tafada cikin jindadi. Kasuwa ta shiga tayi sayayya tare da siyan wasu atampa yan 3k guda uku don ta kaiwa ammi

[3:15PM, 3/20/2018] 鈥�+234 806 125 0020鈥�: 馃挏鉂ゐ煉氿煐ゐ煉涴煉�

NA CUCE TA

馃挍馃挋馃挌馃枻馃挏鉂�

庐zuwairat( ummu Maryam)

8鈨�

Daga kitchen dinning area asabe ta kai ta Sannan dakin daukan baki sai dakin su Ameera don dakinta Kawai take gyarawa sauran yaran suke gyara wurin su da Kansu,

“Ba wani aiki ke da akwai da yawa ba…Kawai dai baa sin gani kazanta ko kadan …” Asabe ta fada mata suna komawa dakinsu, dija dai sauraron ta kawai take don gurin ta dare yayi ta kwanta,

“Kiyi wanka mana kafin lokacin sallan magrib.. Bamu da girki yau don haka babu aikin da zamuyi saidai in Hajiya ta bukaci muyi mata wani abu…” Inji asabe,

“Ina zanyi wankan?…” Dija ra tambayi asabe cikin sanyin murya. Mikewa asabe tayi  ta bude kofan dake cikin dakin tace

“Taso ki  shiga….” Ta fada mata, ahankali dija ta mike ta shiga bathroom din tana kallon ikon Allah don babu abinda ta Iya amfani dashi a wurin tsaya kallon bathroom din, asabe jawo kofan ta farayi dija tayi Sauri rikewa

“Ban…Iya…ba…” Tafada muryan ta na rawa. Dariya asabe tayi Sannan ta shiga cikin bathroom din ta fara nuna mata amfanin shower da heater tare da bathtub, dija kura mata ido tayi Bata ko kaftawa har asabe ta gama Sannan tace

“Yanzu ki nuna min abubuwa dana koya maki…” Fada mata, nan itama dija  ta fada exactly abubuwan da ta fada mata, mamaki ne ya kama asabe cos she explained everything perfectly. Nan asabe ta fita ta barta tayi wankan sai lumshe idanuwa take saboda yanda take jin dadin kamshin sabulun wankan. Atakaice cikin kwana uku dija ta gane kan bangaren Hajiya karama, har da sunayen yan gidan gaba daya kaman yanda asabe ta fada mata Kuma ba karamin dadi take ji gidan ba don within that three days ta chanza cos ko fita batayi Kuma gashi da sun gama aiki kwanciya suke suyi bacci, yanzu kam dija ta bar tsayawa bathroom ta kalli kanta sai dai a gaban mirror dake dakin su amma sai in asabe Bata dakin sai ta tsaya ta kunshe towel dinta ta kalli jikinta da kanta tana kashewa kanta ido tana Dariya , yauma tana tsaye gaban katon mirror tana kallon kanta asabe ta shigo da plate din abinci, da Sauri dija ta gyara towel din tana kallon asabe, itama asabe kallon mamaki tayi mata,

“Me kikeyi haka?…” Asabe ta tambayeta cikin surprise, da Sauri dija tace

“Babu komai…”

“Kaman ya babu komai…”

“Aa… Kawai wanka NA fito….shine nake shafa mai….”  Tafada ahankali, asabe dai Bata kara cewa komai ba ra ajiye abincin suka fara ci,.

Yazed ne kwance yana bacci, alarm ne ya tadashi ya mike da Sauri tare da godiya ga Allah ya shiga bathroom yayi wanka Sannan ya fito daure da alwallah. Kaya ya saka yayi salla nan cikin dakin Sannan ya cire jallabiya dake jikinshi ya shirya cikin suit ya fashe kanshi da perfumes ya fito looking handsome than ever, kallon agogon hannun shi yayi yaga 6:15am

“I still have some time…” Yafadawa kanshi tare da fiddo wayanshi daga cikin aljihunshi, number Hajiya yayi dailing suka fara hira

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button