NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Son ka dawo haka nan mana…wai nan da abuja kake wannan abun kaman Wanda ke abroad?…” Dariya yayi

“Ai mom wahalan tuki nakeji…Kuma sauran sati daya hutuna…”

“To shikenan… An turo maka pic din gidan ?…”

“Yes mommy… It’s beautiful… Amma nan abuja zaa kawota….”.

Yafada yana naughty laugh

“Kaci gidanku…nan Kano zaa ajiyeta…” Turo baki yayi kaman yana gaban ta Sannan yace

“Mom NA….aikin fa?…”

“Ka dinga zuwa every weekend…” Idanuwa ya zaro, yayi shuru Kawai baice komai ba don kar Hajiya tace yana mata rashin kunya, haka suka gama hiran ya fita daga quarters din zuwa office.

Yau Hajiya Aisha ta koma gidansu dija din kai mata kayan data sayo mata, da sallama ta shiga cikin gidan, da Sauri ammi dake zaune ta rafka ban tagumi ta mike

“Ah..ah..Sannu da zuwa…” Inji ammi Tafada cikin murmushin karfin hali,

“Yauwa…” Sannan suka fara gaisawa,  ledan Hajiya ta mikawa ammi

“Gashi inji uwar dakinki dija….” Ahankali ammi ta bude ledan Bata wani yi murna kan kayan ba,

“Ya dija take… Ina Iya zuwa ganinta?..” Ammi ta fada har jikinta NA rawa, murmushi Hajiya Aisha tayi

“Ki kwantar da hankalin ki..diyarki tana gidan Hutu…Kuma albashinta dubu ashirin…” Da Sauri ammi ta kalleta,

“Wane irin aikine zatayi da zaa Bata dubu ashirin cikin kwana talatin?..” Ammi ta fada cike da mamaki.

“Ai NA fada maki yarki tana gidan manyan mutane… Yanzu karshen watan nan zan sayo maki waya sai ki dinga waya da yarki…” Inji Hajiya Aisha, dadi ammi taji har cikin ranta.

_A week later_

Yau yazid zai dawo sai shirya kayan dadi ake kala2 kaman sarki zaizo gidan mussanman Hajiya karama duk wata in yazid zai zo gida weekend haka zata dinga hidima ko kadan Bata gajiya don tana ji dashi tamkar ita ta haifeshi shima bai wasa daita.

Dija NA tsaye gefen asabe dake yankawa mai dafa abinci cabbage cos ba su ke dafa abinci ba,

“Wai me akeyi naga anata dafa abinci kala2?..” Dija ta tambayi asabe cikin kunnenta,

“Babban Dan gidan ne zaizo…” Ta amsa mata, kai Kawai dija ta karkata, haka suka yi aiki har suka gaba aka cika dinning da abinci dija kam sai mamakin yawan kayan take don gani take ko mutane goma abincin yayi masu yawa

“Kilan ci gareshi…” Ta fada cikin ranta. Sai wajen 12 suka gama komai suka koma dakinsu. Kwanciya tayi tana tunanin ammi da kannenta don she missing them beyond words, da tana tunanin it won’t matter amma she’s so wrong she miss them so much, at times in suna cin abinci da asabe sai tace

“Inama su ammi suna nan…” Take fada cikin ranta.

Around two yazid ya shigo gidan cikin wata beautiful and expensive car, da gudu yaran gidan sukaje bakin gate, shima da Sauri ya  fito ko parking baiyiba ya dauki Ameera hannun daya ya dauki marzuq da hannun daya, nishi ya farayi

“Wai …me kukeci….duk kunyi adding weight…” Tafada yana nishi kaman Wanda ya dauki buhun cement. Sauke su yayi   suna Dariya, hannun shi cikin nasu suka shiga part din Hajiya babba

Da gudu mimata da Zainab dake zaune falo suka nufoshi, bude masu hannuwanshi yayi yana murmushi, rungume su yayi

“Nayi missing dinku….” Ta fada masu

“Yaya bakayi missing dinmu ba…jiya dakayi waya da big mommy baka nememu ba…” Inji Zainab dake turo baki, Dariya yayi Wanda ya kara bayyana handsomeness dinshi

“To in ni ban nemeku ba Ku bazaku kirani ba?…”

“Ai bamu dakudi…” Inji mimata, kai ya girgiza yana cewa.

“Baku da kudi amma kullum kuna online…” Yafada tare da kama hanyan mini falon dake wurin, nan ya hangi Hajiya babba da Hajiya karama zaune fuskan su dauke da murmushi,  da Sauri ya karasa wurin su ya durkusa Sannan ya gaida su,

“Ji yanda ka wani koma…duk ka rame saboda rashin abincin kwarai…” Inji Hajiya karama, Dariya Kawai yayi Hajiya babba kam murmushi Kawai take tana kallon danta cikin so da kauna

“Ai gani yanzu sai ki bani mai dadi inci in yi adding weight kafin in koma….” Hararanshi Hajiya karama tayi tana cewa

“Kana zuwa kana maganar komawa….” Tafada kaman tana fushi, zama yayi kan hannun kujeran da take ya rungumota,

“Da wasa nake mommy….” Yafada yana manna mata kiss a cheek dinta, mikewa Hajiya karama tayi ta kama mashi hannu,

“Muje kaci abinci…” Tafada tana janshi, Dariya yayi yabi bayanta don in da sabo ya saba,

“Yaya ina sarabanmu?…” Marzuq ya tambayeshi,

“Ban sayo komai ba..Ku bari da yamma sai in kaiku eleganza,…” Tsalle yaran suka fara, suka fita Hajiya karama NA rike dashi kaman wani karamin yaro, gate aka bude motan shahid ya shigo, tun daga nesa ya hangi yazid da Hajiya karama, Dan karamin tsoki yaja yana cewa

“The fun killer is back…” Yafadawa kanshi yana parking motanshi, Fitowa yayi ya nufosu sanye da three quarters dake low waist a kugunshi, yazid tsayawa yayi yana kallon shi

“Yaya sannu da zuwa…” Ya fada mashi kanshi kasa, yazid bai amsa ba ya tsaya kallon dressing dinshi,

“Ki daga ina kake?…”

“Daga factory…”. Kallon up and down yayi mashi

” ina Sharif?….” Ya sake tambayan shi, hannun shi Hajiya karama ta kara rikewa

“Ka rabu dashi ..muje kaci abinci.. Don’t waste your precious time on those silly boys….” Ta fada mashi, kai kawai ya girgiza ya bi ta, shi Kuma shahid ya tabe baki ya nufi part dinshi da Sharif yana tafiya irin NA niggas wandonshi sai Neman kwalewa yake. Saida suka isa dinning Sannan ta saki hannun shi, zama yayi yana kallon jerin abincin

“Small mom ya zanyi da wannan abincin?…”

“Kaidai kaci Iya cinka ka bar sauran…” Ta fada tana dauko mashi ruwa daga cikin fridge dake wurin, ajiye mashi tayi Sannan ta bar wurin ta koma bangaren Hajiya babba.

Yazid zama yayi yana kallon abincin sai yaji ya koshi don ya rasa abinda zaici Kuma ko kadan baison bata mata rai, Ahankali ya bude warmer daya yacikaro da white rice ya diba kadan Sannan ya bude next warmer ya zuba thick stew dake ciki ya fara ci bayana ya debi dambun nama ya zuba akai, saida yaci ya koshi ya sha ruwa yayi relaxing nan yana waya da mufida. Kawai kaman daga sama sai yaga dija ta bude kofa ta fito asabe NA biye daita, Dan tsaya kallon ta yayi har saida muryan mufida ya dawo dashi hayyacinshi, itama daga idanuwanta tayi ta kalleshi tayi Sauri durkusawa

“Ina kwana?…” Ta fada da Sauri, sai kuma tace

“Aa.. Ina yini…” Ta fada muryanta NA rawa, Dariya asabe tayi yazid kam zaro idanuwa tayi yana kallon ta har lokacin waya NA kunnenshi, hade rai yayi ya daga mata hannu, da Sauri ta mike ta koma ciki, itama asabe gaidashi tayi itama ya daga mata hannu ya cigaba da wayanshi

Saida ya gama ya zauna nan yana tunanin wacece wacce ta fito daga dakin masu aiki, zama yayi nan ko zata Kara fitowa. Dija kam da Sauri ta zauna kan gado kanta kasa,

“Wai ya akayi kika rude?…ko baki taba ganin mutum mai kyauwunshi ba?…” Asabe ta tambayeta, dija dai kasa magana tayi saboda abinda ya makale mata a wuya,

“Ko kin taba ganin shi?..” Ta sake tambayanta,  da Sauri ta girgiza mata kai,

“Kinyi shuru…”

“Ba..bu…komai…” Ta amsa mata tana Dan kwantawa,

“Bazaki sha ruwan ba?… Tunda NA manta ba sa ruwa a fridge ba…”  asabe ta fada mata don diban ruwa suje amma ganin yazid yasa ta dawo don wani irin faduwan gaba taji data ganshi Sannan ko daidaida minti daya Bata fatan kara haduwa dashi don yayi mata kwarjini da yawa

“Anjuma zansha….” Tafada tana kara lafewa kan gadon,

“Kije ki debo mana…ko so kike in debo maki?…” Da Sauri dija ta girgiza mata kai

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button