NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Dan Allah ki.fadamin.. Me ya sameki bayan fitan mu?…” Ta tambayi dija, shuru tayi tana hawaye,

“Dan Allah ki gayamin…wani ya shigo nan?..” Ta tambayeta cos tana suspecting wani abu, kai dija ta girgiza mata, still not believing her ta sake cewa

“Ko su Sharif sun dawo bayan fitan mu…? don ita tasan with them anything is possible, kai dija ta kara girgiza mata

” to me ya sameki…” Ta tambayeta wannan Karin is a soothing tune,

“Babu komai… Gida zanje…Dan Allah.. Ki fadawa hajiya…ko basu bani…ko sisi ba…zan..tafi….” Tafada cikin kuka, asabe zamatayi bakin gadon tana kallon ta, Tasan something is really wrong,

“Ki tashi mu shiga kitchen..Hajiya tace mu hada tea musha kafin a gama abinci…” Asabe ta fada mata, da Sauri ta girgiza kai,

“Bansha…gida nakeso…”

“Waike me akayi maki?… Duk kin birkice min…Allah zan fadawa Hajiya inyaso ta tambayeki da kanta…”  asabe ta fada mata cikin fada,, kafa dija ta fara bubbugawa a kasa kaman yanda ta saba yi a gida tana cewa

“Nidai gida zani…” Tafada cikin kuka sosai, tana tunanin abinda ke faruwa, tana tunanin kilan ko Sharif ki shahid wani daga cikinsu yayi mata wani abu don tana ganin babu abinda basu Iya aikatawa mussanman yanda dija tafi Sauri yan aikin gidan kyau don su ma basu tsira ba don at times in Hajiya sun fita sukan kirata da mai aikin Hajiya babba suce suzo su gyara masu part dinsu daga nan su dinga tattaba su amma da sun nuna masu zasu fadawa Hajiya sai su koresu har da zagi,

“Hmmm to kilan fyade sukayi mata….” Ta fadawa kanta kasa2, ita dai dija kukanta ma ya isheta

“Kwantawa sukayi dake?…” Asabe ta tambayeta Ahankali, dija kara fashewa tayi da kuka ta girgiza kai,

“Babu abinda…akayi min…Kawai..gida…zani…” Tafada mata atakaice.

“Ke kika Sani…in ma wani abun akayi maki baki fada ba ke kika Sani…” Tafada tana mikewa deep inside tana aduan Allah yasa kar ace anyi mata wani abu don she’s too young for that,.

Fita tayi daga dakin ta shiga kitchen ta hado tea cup biyu ta dawo dakin ta  mikawa dija daya amma kememe taki amsa sai kuka take wai ita gida zata.

Yazid kam da kyar yayi sallan asr Sannan ya kwanta Kawai sai ya tsinci kanshi da murmushi Kuma sai ya fashe da kukan guilty yana ji yan gidan suka dawo amma bai Iya tashi saboda yanda duk joint dinshi ke ciwo, duk system dinshi felt empty ko Dan abinda bai tabayi bane oho, wayanshi ne ya fara ringing bai dauki wayanba balle yasan mai kira, shidai Kawai how he will find he’s way out of this, tunanin mufida yayi sai yace.

“It won’t be the case since am the man…” Ya fadawa kanshi, sai yayi tunanin abinda zai fadawa su Hajiya da alhaji for he’s sudden  decision, blanket ya rufe kanshi dashi yana jin yanda fever din ke hawa amma har lokacin bai sha magani ba, goshinshi ya Dan taba yajita very swollen, wayanshi ne ya fara ringing ya ziro hannu ya dauketa ya maida ta cikin blanket tare da kafa ta a kunnenshi, muryan mufida yaji, hiran was very brief don ya fada mata zai kirata later.

Har magrib su Hajiya basu ganshi ba, hakan yasan Hajiya babba ta kirashi don jin ko fita yayi nan ya shaida mata  yana nan

“To kazo muci abinci…” Ta fada mashi,

“Nakoshi…” Ya fada mata Ahankali, Hajiya dake zaune kusa da Hajiya karama dake zuba abinci a plate dinta tace

“Koshi Kuma?…be kaci zakace ka koshi?…” Ta tambayeshi,

“Na ci abinci dazun are eleganza…” Yayi mata karya,

“Ok..” Ta amsa mashi Sannan ta kashe wayanta.

Itama dija har lokacin bata bar kuka ba ita Kawai gida tun asabe NA rarrashin ta har ta gaji ta kyaleta don kanta haka lokacin cin abinci kiri2 dija taki cin abincin nan hankali asabe ya kara tashi taga ya zama dole ta fadawa Hajiya kar a samu matsala,

“Kizo kici abinci..in Hajiya ta dawo daga bangaren Hajiya babba zan fada mata…” Kai dija ta mata

“Banci …” Haka asabe taci kadan ita kadai saboda yanda dija ta tada mata hankali.

 

Har bayan sallan ishai dija bata bar kuka ba don gani take in bata bar gidan ba gani take zai dawo ya kara aikata the same thing don haka Tasha alwashin bazata  ko ruwan gidan bazata shaba har ta bar gidan. Sau wajen karfe 8pm bacci mai nauyi ya dauketa asabe zama tayi bakin gadon tana kallon yanda take sauke ajiyan zuciya.

Shima yazid yana Chan kwance har bayan sallan ishai bai fita ba duk a dakin yayi prayers dinshi, duk family sun hallara a falon dad kaman yanda suka saba duk dare amma bandashi nan ma kiranshi Hajiya babba ta karayi ya shaida mata bayajin dadi ne. Hajiya fadawa su dad abinda ya fada tayi

Da Sauri Hajiya karama ta mike itama Hajiya babba ta mike nan take dukkan yan falon suka mike banda dad, part din yazid suka nufa ga baki dayan su kaman zasu yaki, sallama Hajiya karama tayi a falon shi babu amsa da gudu marzuq yashiga bedroom din da yake ya ganshi kwance rufe da blanket

“Ku zo nan gashi kwance…” Ya fadawa su Hajiya, nan suka shigo yazid ya yaye blanket daga kanshi,

“Subhanallahi… Meya sameka?…” Hajiya karama ta tambayeshi tana kallon yanda for head dinshi yayi ja,

“Babu komai.. Kaina ne ke ciwo…” Ya fada Ahankali,hannu mom ta Dora a goshinshi taji zafi sosai, bata ce komai ba ta kalli  mimata

“Kije ki fadawa dad dinku jikinshi is serious a kirawo doc…” Bata idaba ya katseta dacewa

“No mom..am okay…Kawai ciwon kai ne…nasan zuwa morning zan samu sauki…” Yafada muryan shi NA rawa saboda yana tunanin don basu San abinda ya aikata ba don da sun Sani yasan halin family dinsu.

“No let them call the doc….” Inji Hajiya karama,

“Ga wacce take bukatan doc chan on attended…” Yafada cikin ranshi,

“No..am OK…bana bukatan doc…” Banza mom tayi dashi,

“Baki jina ne?..” Ta dakawa mimata tsawa da Sauri ta fita ta nufi part din dad ta sanar dashi abinda mom tace, nan ya kira doc Sannan shima ya tafi Chan part din, duk sunyi tsaye sai Hajiya karama Kawai ke zaune gefen shi, dad ma na shigowa yagan for head dinshi same question yayi mashi same answer ya bashi

“Don’t tell me nothing.. Baka ganin your for head is swollen?… I said what happened?…” Dad ya daka mashi tsawa, Ahankali ya Dora hannun shi kan goshinshi Sannan yace

“I mistakenly hit my head…” Yayi mashi karya,

“Kai ka Sani…” Dad ya fada Sannan ya bar dakin.

Yazid kam juya kwanciyan shi yayi yana tunanin halin da yasa yar mutane ciki, Kawai he wish he can see her before she goes to bed amma hakan is not possible, Kawai shi ji yake kaman yace  su tafi su barshi da abinda ya dameshi especially Hajiya karama da bata full minti biyar bata dafa goshinshi ba.

“In kawo maka abinci?…”  Hajiya karama ta tambayeshi, kai Kawai ya girgiza mata yana lumshe swollen eyes dinshi. Sai wajen karfe tara NA dare doc yazo yayi yan dube2 shi ya rubuta mashi magani bai fadi exactly abinda ke damunshi don shima baisan abinda ke damunshi ba. Sai wajen karfe 11 suka bar dakin sai lokacin yaji sakat ya kara fadawa duniyar tunani har lokacin bai bar searching Wanda zai fadawa ba,

“I have to tell someone… In ba haka ba this will hunt me for the rest of my life…” Yafada Ahankali, Kawai ji yake inama yana iya gano halunda yar mutane ke ciki.

Abangaren asabe kam jiran Hajiya tayi har karfe goma jin shuru bata dawoba yasa ta je ta kwanta gefen dija dake bacci amma tana firgita saboda nightmares .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button