NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ya Allah nagode maka…” Yafada Sannan ta kara mikewa dija kudin
“Ki rike inyi salla sai mu irga…” Da Sauri ita amshi kudin Kuma she felt so relieved da baa gane abinda akayi mata ba.
Salla ammi tayi itama tayi salla don jin kanta take kaman an bata award saboda she feels so happy don gani take no any harms will ever comes to her again.
Suna idar da salla suka zauna sukayi counting kudin inda duka ga dubu Dari da shabiyar kasancewan Hajiya babba ta bata 5k ita Kuma Hajiya karama ta bata 10k. Ammi dai har lokacin bata bar mamaki ba.
“Yanzu me zamuyi da wannan kudin?..” Ammi ta tambayeta,
“Nima ban Sani ba…” Tafada feeling relaxed,
“Wannan kudin Nada yawa sosai…ko mu dinga saida aja?.”” Ammi ta tambayi dija
“To amma bazamuyi talla ba ko?…” Ta tambayeta, Dariya ammi tayi
“Basai kinyi tallaba… Sai mu dinga bazawa nan kofar gida…” Ammi Tafada mata, ba karamin dadi dija taji ba don yanzu babu abinda take bukata kaman security don ita yanzu tsoron maza takeji fiye da tunanin mai karatu.
Cikin dare kam dija da bacci kawai sai taga kaman yazid ya taho sai ta fara kuka tana
“Kayi hakuri…kace…bazaka…karaba…kayi hakuri….” Amma duk rokon da takeyi mashi bai hanashi abinda yayi niyya ba ganin zai kara raping dinta yasa ta kwalawa ammi kira tare da farkawa daga nightmare din da take Itama ammi da Sauri ta mike ta kunna hasken touch taga dija zaune sai zufa take tana kuka, da Sauri ta rarrafa ta koma gaban ammi tana kalle2 cikin dakin don tabbatar babu kowa dakin don tamkar yana wajen take ji.
“Meke damunki?..” Ammi ta tambayeta tana haskwa face dinta fitila, kara matsawa daf da ammi tayi tace
“Tsoro nakeji…” Tafada tana waige2,
” tsoron me?..” Ammi ta tambayeta tana kallon yanda take sweating,
“Wani ne…” Tafada har lokacin bata bar waige2 ba Kuma tana kara shigewa jikin ammi,
“Me zaiyi maki?…”
“Nima ban Sani ba…ammi tsoro nakeji…” Tafada tare da rungume ammi Kawai sai ta fara kuka tana kama ammi gam,
“AI kece baki adua kafin ki kwanta…” Ammi ta fada tana kokarin kwanciya amma yanda dija ta riketa ya hanata kwanciya, da kyar ta samu tayi loosening grip din dija a jikinta ta kwanta dija ta kara riketa gam.
Shima yazid yana chan cikin dare sai mafarkin dija yake yana bata hakuri yana kuka nadama amma Sam bata bashi fuska ba balle yaga alaman ta yafe mashi, yana nan durkushe yana bata hakuri ta juya baya zata tafi yayi saurin tare gabanta
“Ki yafemin.. Ban karawa.. Dan Allah…” Ya dinga maimaitawa har ya farka daga Bacci, zama yayi kan gado tare da hada kai da gwaiwa don mafarkin looks so real.
Dija kwana tayi manne da ammi which was very surprising to ammi don abinda bai taba faruwa ba kenan. Da safe bayan sallan fajr saida ammi ta tambayi dija mafarkin datayi amma sai taki fadin gaskiya tayi mata karya kan actual dream don’t. Bayan kalaci ammi ta shirya sai cikin garin katsina inda ta shiga kasuwar yar kutungu kasancewan suna zuwa time to time tayi sarin kayan haja irin su turaren irin nasu na yan kauye, da atampopin roba da su powder da sauran kayan gayu irin na yan kauye sai su magi, gishiri da sauran kayan miya sai su klin da omo da sabulun wanki, har da kayan dinki da su zip, zare da sauransu atakaice da ammi ta dawo gida bayan sallan asr saida kusan dukkan mutanen kauyen suka fito don kallon kayan da aka kawota dashi cike da katuwar buhu sai wata karama buhu duk cike dam, data shiga gida mutane biyosu sukayi suna kallon kayan Kuma suna mamakin ina ta samu jalli har haka don duk kauyen babu mai shagon dake dauke da kayan mai yawan wannan daman shago biyu duk garin Kuma kayan su biyu basu kai yawan kayan da ammi ta sayo ba.
A wannan daran ma sai da dija ta samu same nightmare Kuma still ammi ta tambayeta amma same karya tayi mata. Wace gari suka baza kaya waje kan buhu nan kasuwa ta barke dija da siblings dinta ke zaune suna sayarwa amma sai tayi kusan minti talatin tana tunanin abinda yazid yayi mata. Yanzu abun biyu ya zamar mata saboda jiya danmusa mai nama ya sake zuwa inda ya fada mata shi yanason aurenta. .
Abangaren gidansu yazid kam an fara wedding events inda already gidansu yayi tatul da family and friends amma shi kanshi angon kullum karewa yake kaman kudin guzuri saboda yawan tunani Kuma the more days go by the more he keeps falling for her, gani yake if something is not done soon he will loose his mind. Salem kam yayi comforting dinshi har ya gaji amma nothing changes
Ita kam amarya tasan something is wrong don tun ranar da dija ta bar gidansu yazid, yazid bai kara fita ba balle yaje gidansu mufida Kuma in suna yawa he makes the conversation brief, sai yau da suka hadu a wajen till dawn party da Hajiya karama tada aka hada baki ta bude tana kallon yanda yazid ya koma kaman ba shiba, shima sultan coworker dinshi da suke aiki a CBN tare amma Dan plature wato jos yayi mamakin yanda ya koma don saida ya kirashi gefe yana tambayan shi what’s wrong amma murmushin karfin hali Kawai yayi ya amsa mashi da wedding stress, itadai mufida kallonshi Kawai take amma ta zama short of words, saida suka zauna ta Dan matsa kusa dashi ya kalleta ya sakar mata killer smile dinshi itama murmushin tayi
“Baby what’s wrong with you?..” Ta tambayeshi Ahankali, kurawa glowing face dinta ido yayi
“Me kika gani?..” Ya tambayeta tare da boye damuwanshi,
“You look pale..is it me?…” Ta tambayeshi, Ahankali ya daga hannun shi ya kama hannun ta abinda bai taba yiba kenan
“No is not…Kawai abubuwan ne is too much for me…don’t worry am OK…” Yayi assuring dinta. Ahaka akayi party ko karfe tara baiyi ba ya sa a maida mufida gida shi Kuma ya wuce gidan. Su kam sun San something is wrong with him don irin takuran da yake masu in ya dawo gida yanzu baiyi don in zasu kai shabiyun dare basu dawo gida ba bai tanka masu Hajiya babba kam ba damu sosai ba dukda bai fiya cin abinci ba amma Hajiya karama that is in charge na abincin shi tq damu Kuma ta tambayeshi har ta gaji sai ya amsa mata da stress ne.
Yau Saturday ne zaa daura auren yazid, yana kwance cikin blanket sai rawan sanyi yake dakin cike da big boys duk Wanda ka gani kasan yana ji da kanshi, kusan guys goma ne tsaye inda yazid ke kwance cikin blanket,
“Let’s call a doc..” Daya daga cikin guys din ya fada, Ahankali yazid yace
“No…yanzu…zanyi.. Wanka…” Yafada murya shi na rawa, Salem NA zaune kan kujera yayi tagumi yana kallon yazid shi tunda yake bai taba ganin inda guilty conscience yayi weighing mutum down kaman yanda yayi weighing yazid down ba, Ahankali yazid ya yaye blanket dinshi daga shi sai boxer ya ajiye pure white legs dinshi kasa yana tafiya Ahankali ya shiga bathroom, kallon madubi yayi Kawai sai ya fashe da kuka, yana hawaye yana wanka don ji yake kaman heart dinshi zai lalace saboda yanda yake ji. Sai da yayi kuka ya isheshi Sannan ya watsa ruwa ya fito, kayan da aka tanada saboda shi ya dauko ya saka pure white shadda babba riga ya saka looking so breathtakingly handsome. Gayu sai hailing dinshi suke amma ko daga kai baiyi ba balle ya amsa masu.
Around 12 aka daura auren su Sannan suka sake shiri don zuwa reception. Ba karamin kudi aka kashe wajen ba don manyan mutane sun hallara amma ango kan looks disturbed and it’s written all over him, around six suka koma gida inda aka wuce da amarya gidansu.