NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ga Dan akuyan….” Wannan maigadi dake zargin shi ya fada cikin ranshi yayin da yake bude masu gate. Ko gaidashi baiyi ba kaman yanda ya saba suka shiga ciki, ko parking kirki basuyi ba suka fito. Yasan dad dinshi bai gida a wannan lokacin so direct part din Hajiya babba suka shiga inda suka tarda almost kowa a nan harda Hajiya karama, Hajiya karama na ganin shi ta saki guda tana cewa
“Dana ya fara maida jikin shi.. Kai alhamdulillah..” Tafada, yazid kam Dariya yayi kanshi kasa, Hajiya babba kam kallon carbon copy dinta Kawai take tana jin dadi cikin ranta don gani take ta fi sonshi kan duk yaranta, durkusawa sukayi suka gaidasu suka amsa, duk yaran suna school don haka babu wata hayaniya falon. Zama sukayi mai aiki tayi serving dinsu da abun sha, yazid kam bai amsa ba ya zauna yana jiran Salem ya fara magana.
“Wai ina ka barta?…” Hajiya karama ta tambayeshi, Ahankali ya fara cewa
“Tana gida…”
“Why baka zo daita ba?…”
“Ai Salem ne yace in rakoshi yanason ganin ki…” Hajiya karama kallon Salem tayi
“You mean ni?..” Ta tambayeshi, Ahankali Salem ya gyada mata kai kaman gaske, gyara zama tayi
“Hope dai lafiya…”
“Eh Hajiya…wata alfarma ce nakeson kiyi min…” Salem ya fada kanshi kasa, shidai yazid ba haka yaso ba, Salem zai fara magana yazid yayi saurin cewa
“Bari inyi excusing dinku…” Yafada yana mikewa, gaban Mom dinshi yaje, ya kama mata hannu,
“Momcy muje muyi wata hira…” Ya fada mata, Ahankali ta mike kasancewan tana da Dan jiki, bedroom dinta suka shiga ya juyo ya kalli Salem yayi mashi sign din pls don’t fuck up.
Suna tafiya Salem ya kalli Hajiya karama Sannan ya fara cewa
“Daman Hajiya…last three weeks Dana zonan….naga wata yarinya…to so nayi tambaya aka fadamin yar aikin kice…” Baki Hajiya ta bude tana kallon shi don Sam bata gane inda ya dosa ba, Salem yacigaba dacewa
“To sai na tambaya akace min ta tafi…” Da Sauri Hajiya tace
“Pls I don’t understand what you are talking about… Me kake nufi?…” Ta tambayeshi impatiently,
“I am talking about khadija…” Sai lokacin Hajiya ta gane
“Ohhh…” Tayi exclaiming, Salem yacigaba dacewa
“Dan Allah address dinta nake nema ko Allah yasa kin Sani…” Ya karasa maganar yanajin kaman an cire mashi wani irin mountain daga kanshi saboda irin aikin da yazid ya saka shi, gashi yana son Maryam yar Hajiya karama amma gashi yazid ya tisa shi gaba kan yayi wannan karyan, Hajiya kam kallon shi Kawai take tana mamakin me yake nufi,
“Hmmm Ashe Kaine sanadiyan korarmin yar aiki… I know you confronted her shiyasa ta kasa zama cos kayi scaring dinta…in banda abinka me zakayi da yar yarinyan da bata wuce 15 years ba?… I think zan baka shawaran ka nemi class dinka kaman yanda bestie dinka yayi and stop wasting your time on little kids…” Ta fada calmly,
“What a disgrace… Yazid ka gama dani…” Ya fada cikin ranshi, Hajiya tacigaba dacewa
“And about her address gaskiya bani dashi don jiya2 nan NA goge number matar data kawo min ita… Pls don’t feel as if na hanaka address dinta…am sorry I can’t help..” Ta fada mashi Ahankali, da Sauri Salem da kunyan duniya ta isheshi yayi Sauri cewa
“Ba komai… Nagode…”
Yafada kanshi kasa Allah Allah yake yazid ya fito su tafi yaci uban shi, sunfi minti talatin zaune yazid bai fitoba suna cikin bedroom din mom dinshi suna labari daman mom dinshi tana mugun son samun time dashi kadai.sai hira suke amma yana aduan Allah yasa Salem ya samu address dinta.
Ganin flashing din Salem yasa shi mikewa itama mom dinshi mikewa tayi suka fito tare, ganin yanda Salem ya sadda kai kasa yasa shi giving up, yana fitowa Salem yayi ma su mom bankwana shima yazid ya fada masu zai koma gida Sannan suka fito tun basu kai wurin mota ba Salem ya fara cewa
“Wallahi ban taba jin kunya kaman yau ba…” Yafada sounding so furious
“Am so ashamed… Yanzu kallon mutumin banza su Hajiya zasu dinga yi min…” Yazid dai tafiya yake kanshi kasa gabanshi na faduwa don bai San halinda zai fada muddin bai samu address din dija ba,
“Pls me ta fada maka?…” Ya tambayeshi muryan shi na cracking tun kafin yaji result amma for sure yasan babu nasara.
“Tace tayi deleting number wacce ta kawo mata khadija… Could you believe tace in nemi mata kaman naka in aura in bar wasting time dina?…” Salem ya fada cikin takaici, yazid kam bai kara cewa komai ba tunda yaji Salem yace ta goge number yaji komai nashi ya tsaya, jingina yayi jikin mota sai hawaye Salem kam shiga yayi cikin motan yana jiran shigan shu su tafi amma yazid ya tsaya wurin sai kuka yake,
“Yanzu shikenan?…” Ya tambayi kanshi,
“Yanzu NA lalata mata rayuwa haka nan kenan?…” Yafada cikin kuka, Salem bude motan yayi ya sake fitowa ya kalli yanda yake kuka
“Haba yazid…kaman bakasan kaddara ba?…you know if she’s destined to be with you Allah zai kara hadaku…ps let’s go…try and forget about what happened… Many people have done worst…” Da Sauri yazid yace
“Am not many people… I am me…kan yanda mu yan north muke..in har ta auri wani kallon karuwa zaa dinga yi mata…” Hannu Salem ya daga mashi
“Pls is OK….after all the gal is just 13…kilan kafin tayi aure wurin zai koma normal…” Da Sauri yazid ya girgiza kai
“Not after what I did to her… NA shiga uku…ya Allah why me…” Yafada yana kuka not minding in wani Dan gidansu zai ganshi yana hawayen. Dariya Salem yayi
“Wato kayi mata dalla dalla kenan.. Well brother take heart…just go and ask for Allah’s forgiveness… Kawai shawaran da zan baka kenan…” Cikin kuka yazid yace
“What about her own forgiveness?… What about the love I have for her?…” Yafada cikin matsanacin kuka,
“Take that as the punishment of what you did to an innocent gal…and remember hausawa sunci in so cuta ne hakuri ne Maganin shi…so kayi hakuri nasan tunda kana da aure nan gaba kadan zaka manta ta…” Salem ya fada mashi in a comforting tune, zagayawa yayi ya bude driver seat ya shiga tare da zare keys daga hannu yazid. Ahankali yazid ya zagaya ya zaune amma har lokacin bai bar kuka ba. Har suka yi sallan zuhr yazid yana hawaye yana fadawa Allah damuwanshi dukda he’s feeling he’s not worthy Allah ya amshi aduan shi.
Kafin su kai gidan yazid was around 3 kuma by then idanuwanshi sunyi mugun kumburi da ja abinka da farin mutum. Salem na parking ya kalli yanda yake shessheka kaman wani Dan karamin yaro,
“Ni mamaki kake bani…kilan the gal in question ta mance da abinda ya faru amma kai kana nan zaka kashe kanka….” Da Sauri yazid yace
“Ina tausayawa kaina ne…sannan ina tausayawa khadija cos she will never forget she was molested for the rest of her life…and nasan duk lokacin data tuna sai ta tsine min…Salem ina zani da wannan alhakin?…” Ya tambayi Salem yana kara fashewa da kuka, duk jikin Salem mutuwa yayi don yanda yazid ya hada kai da gaban motan yana kuka, Kawai jw wish they is something he can do, he wish he van make him stop amma shima baisan abun yiba,
“Da kana da pic dinta da sai in tura katsina a nemota…”
“Bani dashi….” Yafada cikin kuka. Yafi additional minti talatin yana kuka Salem na rarrashin shi amma baiyi shuru ba sai saida yaji kanshi na wani sarawa Sannan ya fita tare da fadawa Salem ya tafi da motan daga baya ya kawo mashi tunda babu inda yake zuwa.