NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tsayawa yayi ya goge face dinshi bayan ya shiga compound dinshi don kar mufida ta gane yayi kuka.

Itama mufida tunda ya fita take kuka don gani take yana chan suna soyewa da budurwan shi, har karfe daya tana kuka, kwantawa tayi bacci yayi gaba daita, sai karfe 2:30 ta farka taga har lokacin bai dawo ba,  kuka ta farayi, itama idanuwanta sun kumbura saboda kuka. Sai da tayi mai isanta Sannan ta shiga bathroom tayi wanka tare da alwallah Sannan ta fito tayi salla. Ko mai bata shafa ba ta shirya cikin wasu material mai kyau da tsada. Falo ta dawo ta zauna, tana zama da minti biyar aka kawo lunch daga gidansu yazid, amsa tayi ta ajiye kan dinning tana tunanin yanzu duk abinda takeyi mashi bai wadatar ba kenan tunda har yana zuwa wurin wata, Kawai sai taji wani irin haushin shi, kuma still sonshi ya rinjayi tsanan da take mashi. Ahankali ta mike ta koma bedroom dinta ta kwanta tana tunanin abinyi don ko.a mafarki batason kishiya don she’s so afraid taga yazid dinta in the arms of another woman.

Hankali yazid ya shiga main falo yaga babu kowa. Direct part dinshi ya shiga ya sakarwa kanshi ruwa yana aduan Allah yasa jar ta gane don yasan har ga Allah mufida tana  kokari don haka ko kadan bai son ya dameta da matsalan shi. Fitowa yayi daure da towel har lokacin bai barjin ciwon kan ba. Shorts ya dauko ya saka Sannan ya ya dauko very light jallabiya ya saka don ko kadan baisan abu mai nauyi. Part dinta ya shiga yaga babu ita a falon, direct daya daga cikin bedroom dinta ya shiga yana ganta zaune kan gado looking depressed, Ahankali ya taka ya shiga da sallama muryan shi na rawa, da Sauri ta daga swollen eyes dinta ta kalleshi tare da mikewa, kallon yanda idanuwanta duka kumbura yayi, itama kallon nashi idanuwa take, hannuwanshi ya bude mata ta fada ciki tare da fashewa da kuka,

“Am sorry I made you cry…” Yafada yana shafa kanta, Kawai sai shima ya fashe da kuka

Mufida saurarawa tayi don jin is he really crying, daman idanuwanshi suna yi mata kama dana Wanda yayi kuka sai kuma tace kilan wani abun ya fada mashi cikin ido cos batasan abinda zaisa grown up man kaman shi kuka ba, sai taji yana kuka ya rungume ta gam, Ahankali ta daga kanta daga kan shoulder dinshi tana kallon, Ahankali ya sulale kasa tare da hada kai da gwaiwa yana kuka, mufida kwalo idanuwa tayi tan kalle2 cikin dakin, ban da Kukanshi babu abinda ke tashi, ahankali mufida ta durkusa kasa gabanshi tana kallon shi, hannu ta Dora kanshi tana cewa

“Baby what happened?…” Ta tambayeshi cikin sanyin murya, bai amsa ba ya ciigaba da kuka, itama fashewa tayi da kuka din ba karamin tashi hankalin ta yayi ba

“Baby is it me?…wani abun nayi maka?…” Ta tambayeshi tana kuka , da Sauri ya daga kanshi yana girgiza kanshi, sai lokacin mufida ta lura da how swollen his eyes look,

“No..it’s not you…it’s me…I have made a very…. Bad mistake… And it will hunt me…for the rest of my life…” Yafada cikin matsanacin kuka, mufida Bata so jin mistake din da yayi ba cos kukan shima ya isheta tashin hankali, da Sauri ta rungume shi tana shafa bayanshi, shima riketa Gam yayi yana cewa

“Am sorry.. Babu ask Allah to forgive me?…” Yafada cikin kuka, mufida dai shafa bayanshi kawai take tana tunanin what could it be, ko two timing dinta  dayayi ya ga baiyi daidai ba yazo yana kuka, tunani kala2 ta dingayi  tana shafa bayanshi don ita data cika tana jin haushin shi dai ta koma rana tausaya mashi,sai wata zuciya ya dinga raya mata kilan budurwan ce tayi mashi wulakanci. Dan daina kukan yayi ya kalleta

“Baby kin ci abinci?…” Ya tambayeta ahankali,  itama cikin sanyin jiki ta girgiza mashi,

“To muje inyi feeding dinki…” Yafada wet face dinshi dauke da murmushin karfin hali, da Sauri ta girgiza kai

“I don’t have appetite…” Tafada tana zama nan kasan tiles, ahankali ya mike, tare da kama mata hannu

“Stand…” Yayi commanding dinta, ahankali ta mike, yana rike da hannun ta har kan dinning, mufida kam har yanzu bata bar mamakin abinda ke faruwa ba. Kan dinning ya zaunar daita ya fara Bata abinci tana amsa amma duk yanda tayi yaci kinci yayi daga baya itama tace bataci, dole yayi forcing dinta taci har to koshi Sannan ya shiga bathroom ya dauro alwallah, falo ya dawo ya tarda ta zaune tayi tagumi tana tunanin ganin ya fito zashi masjid yasa tace

“Baby..your face showed you are sad…pls kar kaje masjid kar ya zama kaman we are having some marital problems…” Ta fada mashi cike da so da kauna, murmushi yayi yana gyara hannun jallabiya daya nade kafin yayi alwallah,

“Don’t worry.. I will be OK…” Ya fada mata tare dayi mata kiss a goshinta Sannan ya tafi.

A wannan ranar yazid bai ci ko sha ba har dare, ba karamin tashi hankali mufida ta shiga ba, ha yanda kanshi ke sarawa Sannan ga fever daya rufeshi amma Kiri kiri yaki shan drugs, rufe kanshi yayi da blanket yana rawan sanyi. Aranar sai ya kasance a very bad day for him don gani yake its over for him. The following day ya koma family house ya sanar da iyayenshi zai koma abuja, data alkhairi sukayi mashi Sannan ya fadawa mufida ta shirya zasu koma abuja the following day. Nan hankalin mufida ya kwanta don har lokacin gani take rabuwa sukayi da budurwan da yake ce mata zai aura. Amma kuma abinda ke Bata haushi shine ta tabbatar yanason wannan budurwan don komai nashi yayi tsaye chak

[3:23PM, 3/20/2018] 鈥�+234 806 125 0020鈥�: 馃挌馃挋鉂ゐ煐ゐ煉滒煉�

NA CUCE TA

馃挋鉂ゐ煉涴煐ゐ煉滒煉�

庐zuwairat(ummu Maryam)

1鈨�6鈨�

One, two, three, four, five months have gone by da faruwan abun, duk Wanda yasan yazid the last months in ka ganshi yanzu sai ka rantse ba shi bane, don ya rame sosai daman ba kiban gareshi ba amma raman shi na yanzu is far worst, sau uku suka je Kano da mufida, duk zuwa sai dad dinshi dasu Hajiya sun tisashi gaba kan ya fadi abinda ke damunshi amma sai yace masu babu komai, sau biyu yana amsan sick leave daga wajen aikin, shi dai gani yake kilan Allah is really punishing him for devouring an Allah’s property, he Kawai ji yake ya mutu ya huta, mufida kam ga Hutu ga komai amma tunda tana murna kilan rabuwa sukayi da budurwan shi har ta fara tunanin is better ta dawo suyi aure don kar ta rasa mijinta, dukda yazid na kokari sosai don kar ya shiga hakkinta amma ganin shi zaune a falo duk dare yana kuka is so unbelievable for her that she wishes he do what ever makes him happy, sau biyu Salem NA zuwa katsina yana Neman masu kaiwa mutane yan aiki yana tambayan su khadija amma sai suce basu Santa ba, ba komai yasa yake hakan ba is done kar ya rasa abokinshi cos duk inda yake tunani yazid yafi haka. A office kam sultan abokin aikin shi and bestie dinshi a abuja yayi mashi tambaya har ya gaji ya sa mashi ido, din countless times hakan ganshi zaune a office yana hawaye.

Yau ma yana zaune a office ya hada kai da desk ba kuka yake ba amma he’s so lost in his thoughts, shi gani yake kilan khadija is not human, Kawai Allah ya turo ta don ta nuna mashi ishara kan yanda komai abokanshi sukayi sai ya kushe, don gani yake ko matanda ka aura Allah yayi mata rasuwa within five months ya kamata ka fara healing amma nashi kullum heart dinshi is going bad saboda ita

Kullum ji yake kaman ya mutu ko Allah yasa ya huta cos its so unbelievable,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button