NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Am really laughing in Swahili…kai dai Kawai kace 8k per plate of food is too expensive for you shiyasa kakeson chanza wuri…” Wani irin bazwaran dariya yazid yayi yana cewa

“Kaima kasan ba haka bane don ko ban aiki a CBN common 8k a plate na abinci bazai gagareni ba….amma don’t worry Allah ya kawoka Kano lafiya zakasan ba da CBN nake takama ba….” Dariya sultan yayi Yana   cewa

“Oho dai…kai zaka biya kudin duk abinda naci…” Inji sultan

“Wannan ba case bane…” Yazid ya fada adaidai lokacin da aka bude mashi kofan restaurant din suka shiga tare.

Wannan shine kaidan yazid, baya dauka lack of moral character, ko gidan su ansan da hakan, din duk yanda kannanshi ke jin dadin rayuwa da yazo gida komai nasu yake tsayawa don dole su dawo gidan by 8pm ko su kwana waje, alhaji wato babanshi yana sonshi saboda wannan halin nashi, haka Hajiya babba wato mahaifiyarshi hakama Hajiya karama kishiyar mamansu, amma yaran gidan especially shahid da Sharif basuson zuwan shi don yana slowing rayuwan su kaman yanda suke cewa, amma yan Matan gidan irin su Zainab da yusra tare da Maryam NA sonshi kaman lollipop, likewise yan yaran gidan marzuq, mimata, ihsan da Ameera suma basu wasa da shi they love him so much don gani suke duk sun fi sonshi fiye da kowa,. Yazid ne babba a gidansu, sai da akayi shekara takwas da haihuwanshi Hajiya Bata kara haihuwa ba sai alh ya kara aure wanda month din da alh ya kara aure Hajiya babba ta samu cikin shahid itama amarya ta samu cikin Sharif wanda hakan yasan ake kiransu da twins from different mothers, saboda kamaninsu daya da alh, Kuma komai masu iri da har tsawon Sannan behavior dinshi NA rashin ji is the same, don ko da wasa Hajiya babba Bata isa ta siyawa shahid abu bata siyawa Sharif ba,

Bayan shahid Hajiya Bata kara samun haihuwa ba saida Hajiya karama ta haifi yusra da Maryam Sannan Hajiya babba ta samu cikin Zainab, atakaice dai yaran Hajiya babba 4 yazid, shahid, Zainab sai auta marzuq ita Kuma Hajiya karama nada  6, Sharif, yusra, Maryam, mimata ihsan sai auta Ameera. Zaman su is very lovable saboda ko kadan alh bai basu room din kishi ko wani abu makamancin wannan ba, he make all of them feel special don duk lokacin da yake tare da daya yana mantar da ita wata kishiya, zai nuna maki babu kaman ki so kowacce gani take yafison ta alhalin ba haka bane yana sonsu daidai amma fa bai wasa da Hajiya babba saboda karamcinta.

Yau suna zaune falo Hajiya babba tare da Hajiya karama kowacce taci ado cikin expensive swiss lace little brats of the house NA wasa cikin tsakiyan falo kaman yanda su Sharif ke kiran  marzuq ihsan da Ameera kenan,

Hajiya babba kam tamkar carbon copy NA yazid don komai nasu iri daya har red lips dinta. Wata matace dauke da yar paper da pen hannun ta da alaman list take, Hajiya babba kallon Hajiya karama tayi

“Ni iyakan abinda nakeson ayi kenan… Ki fada naki…” Tayi directing maganan ta to Hajiya karama,

“Ni dai ayi dinner.. Ko Kuma party till dawn…” Tafada tana girgiza kirjinta, da ganinta irin civilised women din nan ce, itama ta hadu ba kadan ba, dariya Hajiya babba tayi

“Kinsan Dan naki..Yana iya cewa bai attending…” Inji Hajiya babba,

“Kam har ya isa?.. AI bai isa ba…first wedding da zaayi a family din isa bala should be the talk of the nation…” Hajiya karama ta fada, kallon Matan dake zaune tsakiyan su tayi Sannan tace

“Hajiya wedding planner…kiyi adding party till dawn….” Shuru tayi ta kalli kofan da aka bude, shahid ne ya shigo ya zauna gefen Hajiya karama don mostly sunfi yi daita saboda Bata fiya hanasu duk rashin jin da zasuyi ba, baki ta bude zatayi magana shima Sharif ya shigo ya zauna dayan side din Hajiya karama, Hajiya babba kallon su tayi ta saki murmushi tare da girgiza kai, Hajiya karama tacigaba dacewa

“As I was saying before my angels interrupt me…kiyi planning big till dawn party…” Wannan irin shewa Sharif da shahid sukayi tare da manna mata kiss a both cheek dinta

“That’s why I love you little mom…” Inji shahid don haka suke kiranta da little mom, dariya tayi tana lumshe idanuwa don jindadi,

“Wallahi haka ya kamata ayi Kawai…” Inji Sharif, Hajiya babba dariya tayi tana cewa

“Ai kunsan da Kyar Zai yarda…kun San halin yayan naku…” Daure fuska sukayi shahid yace

“Big mom..Kawai ki fada mashi yayi zaman shi Chan abuja in yaso in an gama bikin sai ni da Sharif mu saka matar a mota mu kai mashi…” Yafada babu wasa,

“Ai hakan Kawai zaayi…zuwan shi ma bai da amfani…” Inji Sharif,

“Kunci gidanku… First son dina kuke cewa hakan?… Zanci ubanku wallahi kunsan halina sarai…” Hajiya karama ta daka masu tsawa, shuru sukayi din sun San tana Iya birkice masu yanzu, Hajiya babba dai kallon su Kawai take with adoration, tana tunanin lokacin da akace zaayi mata kishiya komai nata tsayawa yayi saboda bakin ciki amma yanzu kam kullum cikin hamdala take da Allah ya hadata Dana gari,

“Kuma ki hada mana get together NA mothers Kawai…” Inji Hajiya karama, matar da aka kira da Hajiya wedding planner sai rubuce2 kawai take, duk abinda aka fada sai ta rubuta, sai da aka gama fada mata komai da zaa bukata sannan tace

“To zanyi listing komai Sannan in aiko maku da bill…” Inji Matan

“Wannan babu case…” Inji Hajiya karama dake magana tamkar danta zaayiwa biki, matar mikewa tayi Hajiya babba da Hajiya karama suka bi bayanta, har bakin motan Matan suka rakatq Sannan suka komo cikin part din Hajiya babba don most of the time nan suke zama suci susha, har yan yaran ma basu zama a dakin wasansu sunfi son su kwaso kayan wasansu su dawo part dinta Kuma bata hanasu tunda da akwai masu aiki da zasu gyara waje ko sun Bata.

Falo suka dawo suka zauna suna listing wayanda zasu gayyata din kar lokacin ya kara matsowa su rikice, Hajiya babba NA fadan sunayen mutanen itakuma Hajiya karama NA rubutawa cikin iPad dake hannun.

Sai daf da sallan ishai su dija suka dawo daga tallan daman kusan kullum haka suke dawowa saboda sai bayan sallan asar suke tafiya, agajiye ta shigo gidan ba ko sallama ta shiga dakin ta tarda ammi zaune su binto suna bacci kan tabarma, ajiye ruban tallan tayi da karfi ta zauna kasa gaban ammi

“Sannu da dawowa…”

Ammi ta fada mata tana cire gammo daga kanta,

“Yauwa…” Ta fada tana kallon su binto dake bacci,

“Har sunyi bacci?..” Ta fada har lokacin Bata bar kallon su ba,

“Yan rigima sunyi bacci…ya kasuwa?…”

“Lafiya lau…” Ta amsa mata tana kwanciya kasan inda take,

“Madalla…”

“Ga kayan da kikace in sayo nan cikin roban,….” Ta fada tana nuna Roban data ajiye

“Yauwa yar albarka…” Ammi ta fada tana jawo roban gabanta tana kallon abubuwan da dija ta sayo, dija gyara kwanciya ta tayi yanda zata Iya dauko kudin dake daure a haban zaninta, daga kwance ta fara kunce daurin ta dauko kudin

“Ga sauran…dari biyar ne da ashirin.. NA sayi awara ta talatin cikin kudin…” Ta fada tana mikawa ammi kudin

“To dijata…nagode kinji…dafatan babu Wanda yayi maki zancen banza yau?…” Daga kwance ta girgizawa ammi kai

“Yau ban shiga garejin ba…cikin garin dauran na shiga kuma na saida duka….”

“To alhamdulillah….” Ammi ta fada tana jin dadi, ammi mikewa tayi ta dauki roban ta ajiye shi gefe

“Ammi gobe Dan Allah a kai gero injin… Wallahi marata ke ciwo….” Tafada tana Dan dafa maranta, ammi ajiye roban tayi ta dawo ta zauna

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button