NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Di…ja…wayayi…maki…ciki?…” Tafada kaman mai asthma saboda yanda numfashin ta ke up and down, dija kara kallon kanta tayi tace

“Ciki?…” Ta tambaya sounding very surprised, da gudu ammi ta fita waje, kaman mai.Neman wani abu kuma ta dawo dakin batare data dauki wanin abun ba, dija dai tsaye take tana kara cewa

“Ciki????…” Sai kallon kanta Kawai take tana maimaita same word NA ciki

“Wa yayi maki ciki?…” Ammi ta fada kaman wata sabuwar cigan mahaukaciya, dija Sam batasan abinda ammi ke nufi ba don a iya saninta tana da ciki mana so batasan cikin haihuwa ammi ke magana ba, jin wani irin mari yasa ta dafe cheek dinta

“Wa yayi maki ciki!!!!…” Ammi ta tambayeta wannan Karin tana fita waje still da gudu, itacen dake cikin murhun dake ci da wuta ta dauko ta shiga dakin, sai lokacin dija Tasan this is something serious,

tsalle ta farayi tana kuka

“Nace wa yayi maki ciki.. Ashe ke yar iska ce ban saniba…” Ammi ta fada tana kwalla mata itacen dake cida wuta, wani irin ihu dija ta saki tana cewa

“Nima ban Sani ba…” Amma jin ammi ta kirata da yar iska yasa ta fara tuna yazid kuma tana tuna abinda yayi mata, bare back dinta ammi ta kara kwalawa firewood dinta dija ta kara sakin ihu, sai tsosta jikinta take saboda garwashin wutan dake sauka a jikinta,

“Bazaki fadi ba kafin in kashe ki?…” Ammi ta fada tana harbe cikin ta, nan take dija ta durkusa kasa tana kuka tana dafe da cikin ta

“Wayyo Allah… Cikina….cikina…” Ta dinga maimaitawa da karfi,

“Baki fadi?…” Ammi ta fada tana dukanta kaman an aikota, dija sai rusa ihu take Tana kiran cikinta don ammi na harbe mata ciki taji kaman wani abu ya gitta cikin cikinta, ammi na dukanta tana kuka tana cewa

“Wa yayi maki ciki?…”

Tafada cikin wata irin murya mai kama dana macen zaki dake jin yunwa, dija dake dafe da cikinta duk idanuwanta waje ta kalli ammi da idanuwanta tana cewa

“Dan…Allah… Ammi….kar…ki…kashe…ban San…yanda..akeyin…ciki ba…” Tafada kaman mai asthma saboda yanda numfashin ta ke fita da kyar, kan itacen da har lokacin yake hayaki ammi ta kara buga mata, da Sauri ta fara scratching wurin wannan Karin batayi ihu ba saboda azaban da takeji a jikinta yafi karfin ihu,

“Da wa kike iskanci…” Ammi ta tambayeta, dija rana girgiza kai tana ja baya ko pant babu a jikinta, tana ja baya taga inda ta bari da jini kasa, kara dafe cikinta tayi

“Wayyo cikina… Mutuwa.. Zanyi…wani…ne…ya…saka..min..wani..abu….” Tafada da kyar, ammi ko kallon jinin kasan batayi ba ta ajiye itacen ta Dora hannu kan,

“Wani!!!!???….” Ta fada tana tsalle tana kuka, da Sauri dija dake cije lips dinta saboda azaba ta gyada mata kai,

“A ina?…” Ammi ta sake tambayan ta cikin tashin hankalin da tunda dija take Bata taba ganinta haka ba,

“A..chan…birni….” Tafada har lokacin Bata bar ja da baya ba Sannan har lokacin hannun ta biyu rike da maranta gam,

“Daman karuwanci aka kaiki?…” Ammi ta fada tana kara fashewa da wani matsanacin kuka,

“Karuwanci kika yarda aka kaiki?… Shi yasa aka baki wannan makudan kudin?…” Ammi ta fada tana sulalewa kasa sai kuka Kawai take, dija sai kara ja da baya take saboda yanda ta razana da ammi, sai da ammi tayi kuka ta koshi Sannan ta kalli dija da ta lumshe idanuwa hawaye na zuba,

“Nace ya bari..banso…” Tafada cikin kuka, ammi kallon tsana kawai take mata, ji Kawai take kaman ta shaketa ta mutu don bakin ciki. Tana maneji da yan marayunta dija ta rasa abinda zata kwaso mata sai ciki,

“Da bakiso kin fadamin abinda akayi maki?…” Ammi ta tambayeta wasu new tears na rolling, da Sauri dija ta girgiza mata kai Kara dafe cikinta tayi

“Wayyo cikina… Zafi nakeji…” Tafada cikin kuka, don dukan da ammi tayi mata baiyi mata zafi kaman yanda cikin takeyi mata zafi ba. Jin abu NA zuba daga kasanta yasan ta kara dagawa da kyar daga inda take zaune ta rarrafa ta koma gefe guda.

“Maza ki tashi ki tattara kayanki ki tafi gidan Matan da ta kaiki karuwaci….” Ammi ta fada babu wasa, sabon kuka ta farayi tana girgiza kanta

“Ammi….”

“Ki tashi nace!!!…” Ammi ta daka mata tsawa, da Sauri ta kama bango zata tashi amma ta kasa saboda yanda cikinta ya kara murdawa,

“Cikina…ammi…ban..Iya …tafiya….” Tafada tana komawa zaune,itacen ammi ta kara dauka Wanda yasa dija tayi saurin mikewa da kyar, kallon yanda jikinta yayi jajir saboda duka da wuta. Sai jini ke bin kafanta, tana dafa bango ta je wajen bag dinta, dukawa tasoyi don ta saka kayanta amma hakan ya gagara, bango ta kama ta zauna Sannan ta bude bag din da Hajiya aisha ta

Saya mata ta dauko daya daga cikin kayan da ta taho dasu daga birni ta saka, kallon ammi tayi ta kalli yanda kafanta ya jike da jini, ko kadan babu alaman tausayi tattare da ammi, daga inda take zaune ta dauko pant ta saka da kyar Sannan ta dauki rag Wanda take amfani dashi wajen period dinta ta tura cikin pant din. Ahankali ta mike

“Ki dauki jikanki…” Ammi ta shaida mata,

“Ammi …INA…zani?…” Ta tambayeta tana kuka

“Ki tafi chan inda aka koya maki karuwanci…” Ammi Tafada in I don’t care tune

“Dan..Allah.. Ammi…kiyi.  Hakuri…” Ta fada cikin matsanacin kuka, itace ammi ta kara dauka, da Sauri ta mike tana kara dafe cikinta, tana kuka tana bawa ammi hakuri amma a banza, ammi daukan kudin kayan da tayi niyyan zuwa kasuwa dashi tayi ta watsa mata

“Ga kudin karuwanciki…” Tafada tana watsa mata kudin, dija Bata kalli kudin ba ta fara tafiya duk kafanta jini, tana kuka ta juyo ta kalli ammi,

“Kiyi hakuri.. Dan…Allah… Bansan…inda…zanje ba…” Ta fada tana kuka kaman ranta zai fita,

“Inyi hakuri ki haifamin shege acikin gidan nan?…hakan ba zai taba yuwuwa ba..ki tafi Chan… Ko bani da da ko.daya ban zama da ke…balle inada saura…ban barinki ki Bata masu tarbiyan su…maza ki tafi…” Ammi ta fada mata tana nuna ta da itacen dake hannun ta,

“Kuma ki.kwace dukkan kudin nan da kayanki…banason in kara ganin ki…ban yafe maki ba…maza ki fitar min daga gida kafin in kasheki….” Ammi ta fada da karfi, sai lokacin su binto dake tsaye bakin kofan suka fara kuka, ko kadan ammi bata kalli karanta dija ba, da Sauri dija ta duka ta fara kwace kudin da hannun ta daya tana kuka, dukan su ta kwace ta zuba cikin bag tayi zipping Sannan ta dauki bag din da hannu daya, dayan hannun ta kan cikin ta, haka ta fita daga gidan tana tafiya ahankali ta kuka, Kawai karfin hali Kawai take tana tafiya amma ji take kaman wani abu zai fado daga gabanta. Tana tafiya ana tambayan ta inda zata amma ko kai Bata Iya dagawa balle tayi magana.

[3:24PM, 3/20/2018] 鈥�+234 806 125 0020鈥�: 馃挌馃挏鉂ゐ煐ゐ煉欚煉�

NA CUCE TA

馃挍鉂ゐ煉滒煐ゐ煉氿煉�

庐zuwairat(ummu Maryam)

1鈨�7鈨�

Kafin ta kai bakin titi har maraice tayi saboda ahankali take tafiya ga ciwon Mara ga duk jikinta zafi ga jinin bai bar zuba ba don ji take kaman rag din data saka yayi wet. Nan bakin titi ta ajiye bag dinta ta zauna sama tana kuka

“Wallahi sai naje kin fada mashi ya cire min cikin…” Tafada cikin kuka

“Ke kika kaini gidan….” Take fadawa kanta, tafi minti talatin nan zaune kafin ta samu motan zuwa cikin daura, wayanda ke cikin motan kallon yanda yar karamar yarinya ke kuka Kawai suke sai tambayan ta suke amma Bata cewa komai. Lokacin data isa kofar gidan Hajiya Hajiya Aisha ko gani batayi sosai don har lokacin jinin bai tsaya ba, tana Dan bugawa ta tsaya, jin shuru yasa ta kara turawa sai taji bude yake, cikin gida ta shiga tana kuka, tana shiga Hajiya Aisha tana dawowa daga unguwa, kallon dija dake faman kuka tayi from head to toe ta kwalo idanuwa tana kallon kafan dija dake jini, da Sauri ta karaso wajenta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button