NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Dija lafiya?…” Ta tambayeta tana kallon bag dinta dake kasa, cikin shessheka dija tace
“Ki maidani chan gidan ya cire min….” Tafada cikin kuka, kallon mamaki Hajiya tayi mata don Bata gane abinda take nufi ba, Hajiya Bata damu da abinda take cewa ba sai Kara cewa tayi
“Dija me akayi maki !!…” Ta tambayeta cikin tashin hankali tana daga doguwar rigan dake jikinta tana kara kallon jinin dake kafanta, tana cewa
“Inna lillahi…” Don anata tunanin raping dinta akayi, dija Bata amsa mata ba tacigaba dacewa
“Ki maidani…” Bata idaba Hajiya ta ce
“Wai meke damunki…” Ta daka mata tsawa da karfi, da Sauri ta fara cewa
“Ammi tace ciki gareni….shine tace inzo ki maidani…a cire min…” Ta fada cikin kuka, idanuwa Hajiya ta kara zarowa
“Ban gane ciki ba….” Hajiya Aisha ta tambayeta cikin tashin hankali don abinda bai taba faruwa da sauran yaran da take kaiwa gidan aiki bane
“Wai ina da ciki ammi tace….” Inji dija,
“Wannan jinin fa?…” Hajiya ta fada tana nuna legs dinta
“Nima ban Sani ba….” Ta amsa mata,
“To wa ya fadawa amminki kina da ciki?…” Hajiya ta sake tambayan ta,
“Nima ban saniba….cewa tayi ina da ciki wai in tafi da jikkata kuma wai Bata yafemin ba…tace kar in kara dawowa…” Hajiya Aisha dai tsayawa tayi tana kallon dija don ko kadan babu alaman ciki tattare daita,
“Village mentality… In ma cikin gareki sai ta koreki?…to bari ijn tambayeki…kin raba kwanciya da wani?….” Ta tambayeta, da Sauri dija ta girgiza mata kai Sannan tace
“Wani ne ya saka min wani abu a gabana…” Da Sauri Hajiya tace
“Waye?…” Cikin kuka dija tace
“Chan gidan da kika kaini….” Baki Hajiya ta bude tana mamakin abinda ke faruwa, dija kara dafe cikinta tayi, ta fara yarfe hannuwa tana cewa
“Wayyo cikina…”
“Me ya sami cikinki….” Hajiya ta tambayeta
“Ammi ta harbe min ciki…” ta fada cikin kuka, mai aikinta Hajiya ta kwalawa kira, sai tataho da gudu saboda yanda Hajiya ta kirata on top of her voice, kallon dija tayi ta tsorata, umarni Hajiya tayi mata da ta dauki bag din dija su shiga dakinta ta gyara mata jiki zata kaita hospital. Nan suka shiga dakin dija ta shiga wanka sai kuka take dukda muryanta bai fitowa saboda kuka. Hajiya kuma zama tayi falo ta rafka uban tagumi, tana aduan Allah yasa ba hakan bane don batasan abinda zai biyo Bata ba muddin hakan ya zamo gaskiya.
Mai aikin Hajiya Aisha tambayan ta tayi abinda ke faruwa, dija fada mata komai tayi, fashewa tayi da kuka saboda tausayi don itama taga cikin sanda dija ke saka wasu kayan bayan ta fito daga bathroom, duk pant da rag da dija ta saka ya cike, pad mai aikin Hajiya ta Bata ta nuna mata yanda zatayi amfani dashi. Few minutes later Hajiya ta shigo ta umarceta data biyota, nan suka kama hanyan hospital, inda doctor ya shaida mata da gaske dija na dauke da cikin wata biyar kuma ya Kara dacewa tana bukanta bed rest, don kar cikin ya yamu matsala, hannu Hajiya ta dafa ga kai tana kuka, don gani take dija tayi karanta da sanin namiji balle ciki, kiran dija waje tayi, saida suka kebe Sannan tace
“Dija tsakanin ki da Allah wa yayi maki ciki?…” Ta tambayeta cikin sanyin murya, sabon kuka dija ta fara tana cewa
“Nima ban San yanda ake ciki ba…” Hajiya goge hawayen face dinta tayi
“Wa ya saba saka maki abun fitsarinshi….” Hajiya Aisha ta tambayeta, da Sauri dija tace
“Wannan mutumin dake gidan da kika kaini ne ya saka min wani abu… Ban San ko meye ba…” Hajiya kara fashewa tayi da kuka tana tuna lokacin da dija ta susuce kan dole sai an maido ta gida Ashe wannan ne dalilin,
“Nashiga uku…” Hajiya ta fada cikin kuka,
“Waye daga cikin yan gidan?…”
“Wannan babban…Wanda akace zaayiwa biki…” Ta fada cikin kuka, itadai Hajiya shuru tayi tana tunanin abinyi don da Bata kaita ba da bazaayi mata ciki ba, dakin doctor suka koma Hajiya ta zauna Sannan tacewa doctor
“Dan Allah a cire cikin… Yarinyan tayi karanta…Sannan ba aure gareta ba..”
“Inna lillahi waina ilaihi rajuun…” Doc ya fada Sannan yacigaba dacewa
“Gaskiya Hajiya bamu irin wannan danyen aikin nan wurin.. Sannan INA baki shawaran bai kamata ayi kisan kai ba don Allah ya kaddara hakan zai faru…sins din zasu yi yawa…Kawai ni shawara ta shine ki kaita gidan da akayi mata ciki, in da hali kilan ya aureta…” Doc Wanda ba bahaushe bane ya fada mata, cikin kuka Hajiya tace
“Ai mu bamu irin wannan abun…”
“To Baku irin wannan abun amma anayiwa yara raping?… This is an act of molestation… Kawai ni shawara ce na baki…” Yafada Sannan ya mike, bayan ya rubuta mata drugs da zaa sayawa dija
Hajiya kasa tafiya tayi don duk ta rasa abinyi, banda faduwan gaba babu abinda ke damunta, kallon dija dake tsaye gefen ta hannun ta dafe da cikin ta tayi
“Ya akayi kika yarda…bakisan babu kyau kwanciya da namijin da ba aurenki yayi ba?…gashi yanzu yayi maki cikin shege…” Hajiya ta fada, dija kara fashewa tayi da kuka don tanajin yanda ake magana kan cikin shege cikin tatsunniya kuma babu Wanda ya tabayi a garinsu sai ita,
“Ki kaini ya cire min…” Ta fada,Hajiya tsoki taja saboda haushi babu kaman yanda dija ke nuna Bata San komai dangane da abinda ke faruwa ba,
“Wa zai cire maki?..” Hajiya ta tambayeta tqnq hararanta,
“Shi Wanda ya saka min…” Tafada tana kuka. Wani irin dogon tsoki Hajiya ta kara ja,
“Sakarcinki yayi yawa..shiyasa kikaje kika gwale kafa…to ni babu ruwana…gidanku zaki koma…daga taimako bazaki batamin suna ba…ba a kanki NA fara kai yara aikatau ba…” Tafada tana mikewa, fita tayi dija ta bi bayanta suka shiga mota suka bar hospital. Chemist tabi ta sayi Maganin da aka rubuta ma dija. Sannan suka koma gida. Da kyar mai aikin Hajiya tasata taci abinci Sannan tasha Maganin kafin ta kwanta.
The following day cikinta ya bar ciwo kuma jinin ya tsaya. Bayan breakfast Hajiya ta umarceta data dauko bag dinta, cikin sanyin jiki ta je ta dauko bag dinta suka shiga mota, hanyan garinsu dija Hajiya Aisha tayi, dija fashewa tayi da kuka tana cewa
“Dan Allah ki maidani…ammi tace kar in kara zuwa gida…tace batason kara ganina…Dan Allah ki maidani ya fara cire min kafin in koma gida.. Dan Allah.. ” Tafada cikin matsanacin kuka,
“Dalla rufe min Baki….” Hajiya ta daka mata tsawa, da Sauri ta kama bakinta tana hawaye don yanzu baya ga yazid babu wacce take tsoro kaman ammi cos taga real colour dinta
“In ba don kina munafuka ba in namiji yayi maki wani abu bazaki fadawa amminki ba…amma sai kika boye mata…ko kin fada mata?…” Ta fada cikin fada, dxa Sauri dija ta girgiza mata kai,
“Har tambayan ki na dingayi kan abinda ke damunki amma kikace babu komai…”
“Shi yace kar in fadawa kowa…” Ta fada cikin kuka
Tsoki Hajiya ta Kara ja
“Amma baki da wayau Wallahi…” Tafada Sannan sukayi driving in silence har garinsu dija. Fitowa Hajiya tayi, dija kam da kyar ta samu courage din fita tana tafiya ahankali, sallama Hajiya tayi ta shiga tsakar gida yaran ne suka amsa banda ammi dake kwance lullube da wata tsohuwar bargo. Hajiya shiga dakin tayi ta kara sallama, da Sauri ammi ta mike zaune, nuna hajiya tayi da yatsa sannan ta fara cewa
“Allah yaisa tsakanina dake…yanda kikasa aka lalata min rayuwar ya Allah yasa ayiwa naki haka…don ina talaka Mara miji kikasa aka lalata marainiya rayuwa….” Kuka ne ya CI karfinta tayi shuru,



