NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

Gaisawa suka shiga yi, nan da nan aka kawo masu abin sha. Hajiya Aisha juyawa tayi bataga dija ba,
“Dija!…” Ta kirata, sai lokacin ta fito ahankali tana goge hawayen ta, Hajiya karama kallon Hajiya babba tayi Sannan ta maida kanta wajen dija tana kallon ta from head to toe
“Aa.. Ashe tare da dija kuke…” Hajiya karama Tafada tana kallon dija datayi mata girma don ko kadan Bata gane itace ba. Ahankali ta durkusa ta gaidasu kanta kasa, amsawa sukayi cikin faraa as usual amma suna mamakin abinda ke faruwa har suka taho dukan su, yayar Hajiya karama ce ta ajiye drink din hannun ta ta fara cewa,
“Ni Ku saurareni in fadi abinda ke tafe damu don inason Zan koma katsina yau…” Tafada in a serious tune, murmushi Hajiya babba tayi Sannan tace.
“Hmm ke kullum kaman visitor a gidan nan…daman nasan ba haka nan kika zo ba…muna sauraron ki…” Tafada cikin raha,
“Ai dai kunsan wannan Yarinyan ko?…” Yayar Hajiya karama ta fada tana nuna dija,
“Sosai ma…ai itace tayi min aiki for just few weeks ko?..” Hajiya karama tayi responding, itadai hajiya Aisha shuru tayi tana godewa Allah dayasa yayar Hajiya karama ta biyosu don gani take ita da kawarta bazasu Iya fuskanta wannan maganar ba,
“To tana da ciki.. Kuma yaran gidan nan suka yi mata…” Tafada babu alaman wasa ko wani abu, da Sauri Hajiya karama ta kalli Hajiya babba sukayi four eyes, Hajiya karama daure fuska tayi,
“Yaya ban gane wannan magana ba?..” Ta tambayeta atakaice,
“Me baki.gane ba?…” Itama ta amsa mata atakaice,
“Haba yaya…ya zaayi ki biye wa irin wannan maganar… Kinsan gold digger will do anything to gate to fame…” Hajiya karama ta fada cikin baccin rai, itakam Hajiya babba mutuwan zaune tayi don komai.nata tsayawa yayi tana tunanin abubuwa da dama at the same time,
“Haka Kawai suna son dragging sunan mu into.mud Sai ki biye masu….” Hajiya karama ta fadawa yayarta Sannan ta juyo ga Hajiya Aisha,
“In wannan plan ne don ayi black mailing dinmu to tirrr…don it won’t work… ” yanda take magana shows she is so angry, yayarta baki ta bude tana kallon,
“Daman ke haka kike…baki.bincike.. Sannan baki ganin laifin yaranki….” Hajiya karama Kara daure fuska tayi
“Yo yaya haka nan Sai in fara ganin laifin innocent children?… Tun yau nake zaune da masu aiki?…sai wannan zaayi wa ciki?…ni Gaskiya su bar min gida kafin inyi rashin mutunci…” Tafada sounding very bitter, ahankali Hajiya babba ta rike mata hannun alaman cool down, itakam Hajiya Aisha kunyan duniya ne ya kamata farat daya, KAWARTA ma rasa bakin magana tayi, yayar Hajiya karama ce tace
“To kina nufin karya akayiwa yaran nan kenan?…”
“Sosai ma kuwa…I can’t believe zaki yarda with such allegations against yaran nan ba…” Tafada tana watsawa Hajiya Aisha harara don gani take it was all her plan. Hajiya babba ce ta saki ajiyan zuciya Sannan tace
“Dija…” Ta kirata cikin sanyin murya don dama Hajiya babba Bata da hayaniyan Hajiya karama, ahankali dija ta daga wet face dinta ta kalleta batare data amsa ba cos ko kadan Bata Iya magana, don ita duk.maganar da akeyi bashi ne damuwanta ba Kawai kar yazo ya sameta, don tana shiga gidan wannan tsoron ya dawo mata kaman bha ita ke cewa a kawita ya cire mata ba.
“Waye ya kusanceki cikin yan gidan nan?…” Shine tambayan da Hajiya babba tayi mata , ba karamin haushi Hajiya karama taji ba
“Haba anty… Why are you asking such question?…badai ki yarda da wannan mutanen ke cewa ba?…” ta fada cikin fushi, hannun ta Hajiya babba tabkara kamawa, dija.shuru tayi ta kasa amsa mata, maimaita tambayan Hajiya babba tayi, Sannan dija dake kuka tace
“Wannan.. Ne…dayazazo daga…tafiya…da zaayiwa biki….” Tafada cikin matsanacin kuka,
“Hope she don’t mean yazid?…” Hajiya karama ta fada kaman ta shake dija, Hajiya babba kam nan take ta fadawa kanta karya ne wannan zancen Kawai anason Bata mata sunan yaro ne,
“Me sunan shi…” Hajiya babba ta tambayeta trying to calm her self,
“NA…mance….” Dija ta masa mata cikin kuka,
“Sharif?…” Hajiya ta tambayeta, da Sauri ta girgiza mata kai,
“Shahid?…” Ta sake tambayan ta, Hajiya karama kam ta cika tayi fam,
“Ki fada kar ji tsoron kowa…..” Yayar Hajiya karama ta fadawa dija, Kawai Sai Hajiya karama ta wulla mata harara kaman ba yayar ta ba
“Daman kin Dade kina nuna tsananki kan yaran nan..kome sukayi maki?… Oho…” Hajiya karama ta fadawa sis dinta, Hajiya Aisha da KAWARTA dai yan kallo Kawai suka koma don she can’t wait wannan discussion yayi over cos yana damunta don ji take kaman ta bude kasa ta shiga,
“Yanzu ni kike cewa NA tsani yaranki?…” Yayarta ta fada tana nuna kanta,
“Yo ko baki fada ba ai kin nunamin baki sonsu cos babu mai son mutum da zaiyi conniving da wasu don su Bata maka suna….” Inji Hajiya karama dake cika tana batsewa,
“Dan Allah kiyi hakuri…” Hajiya babba Tafadawa yayar Hajiya karama, Sannan ta maida duban ta ga dija
“To waye cikin su..ko yazid ne?…” Sai lokacin dija t tuna sunan shi, da Sauri ta daga mata kai, wani irin tsalle Hajiya karama ta daka tare dacewa
“Ayyiiirrrrr…kin dai gan abinda nake fada maki ko?… Wai set up din ma bai tsaya kan yan yaran ba sai kan yazid… To before in rufe idona in bude…Ku bar min gida…now…” Tafada da karfi, Hajiya babba kam murmushin takaici tayi don gani take kowa na duniya na it aikata irin wannan abun amma banda yazid don ta sanshi in and out, anata tunanin, Hajiya karama NA ihu dija ta mike da Sauri ta fita daga falon tana kuka, karaf Sai wannan mai gadin ya ganta don ko.kadan bai lura da ita lokacin data shiga ba,
“Hmmm result din abinda kukayi ya fito…amma da gani kece zaki wahala….” Yafadawa kanshi cikin ranshi yana. Kallon dija dake kuka, Hajiya Aisha da KAWARTA ma mikewa sukayi itama yayar Hajiya karama ta mike tabi bayansu, da Sauri Hajiya babba ta rike yayar Hajiya karama kan kar ta tafi amma taki saboda bacin ran abinda kanwarta tayi mata. Bag din dija suka dauka daga cikin motan yayar Hajiya karama,. Koda ta tambayesu ina zasu kaita Hajiya Aisha tq amsa mata da jos zata kaita,. Nan suka fita daga gate a kafa ita kuma ta shiga driver dinta ya kama hanya KT daita. Dija NA tafiya tana kuka don batasan takamemen sunan ainahin garinsu ammi ba amma Tasan daga jos take.
“Allah na gani ban dauko ki don in wulakanta maki rayuwa ba….ki yafemin…” Hajiya Aisha ta fada tana fashewa da kuka,
“Kin dai tabbatar kin San garinku ko?…” Ta sake tambayan ta, kai Kawai dija ta daga mata don ita Kawai so take kilan a hanyan zuwa jos kilan tayi accident ta mutu Kawai da bakin ciki da take . keke suka tsaida ya kaisu har bus stop, kawar Hajiya Aisha Sai tsoki kawai take. Suna zuwa tasha dija ta shigaitan jos, Hajiya Aisha ta biya kudin mota Sannan ta Bata 10k. Number wayanta ta rubutawa dija, ta bude bag dinta ta saka kudin da number. Hajiya Aisha na tsaye har motansu ya tashi Sannan su suka hau motan KT.
[3:24PM, 3/20/2018] 鈥�+234 806 125 0020鈥�: 馃挍馃挌馃挏馃枻馃挋鉂�
NA CUCE TA
馃挍馃挌鉂ゐ煐ゐ煉滒煉�
庐zuwairat(ummu Maryam)
1鈨�8鈨�
Bayan Hajiya babba ta koma falo zama tayi tare da rafka uban tagumi tana tunanin abinda ke faruwa, confirm Tasan something is wrong amma ba ta hanyan yazid ba kilan wasu yaran gidan
“Wai menene anty?…” Hajiya karama ta tambayeta tana kallon how lost in thought she is, ajiyan zuciya Hajiya babba ta saki