NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Enough… Ka bar kukan haka nan…the damage have been done,..tashi…” Tafada tana goge hawayenta, kin tashi yayi ya kara cewa
“Pls Ku fadawa khadija ta yafemin… Na cuci rayuwanta…na zalunceta…am sorry… Sharrin shaidan ne…” Ya cigaba dacewa, sai lokacin asabe ta gano inda matsalan yake, ko kadan batayi tunanin dija is pregnant ba, Kawai tana tunanin yana confessing kan abinda yayi mata ne. Hajiya karama rike shi tayi ya mike ta saka hannu tana goge mashi tears din face dinshi wasu suna zubowa, duk a lokacin yana tunanin dija tana gidan. Hajiya karama kam tausayin yazid Kawai take don yanda ya chanza shows he’s really sorry, kama hannun shi tayi sukayi hanyan bedroom dinta, Dan tirjewa yayi
“Small mom…I need to see khadija…” Yafada cikin low voice,
“An tafi daita…” Tafada mashi ahankali, kuka ya kara fashewa dashi,
“We don’t know any of you could be responsible… Tace Kaine amma we thought it was a plan to blackmail us…” Ta fada mashi, ahankali yazid ya zauna kasa tare da dafe kanshi yana kuka. Hajiya babba kam tana cikin bacci taji hayaniyan yara suna kiran yaya yazid, da Sauri ta mike don tunda Hajiya karama ta shaida mata bata dawowa itama ta kwanta. Autanta ne ya shigo dakin yana cewa
“Big mom yaya ya dawo…” Kallon surprise tayi mashi,
“Yana ina?…” Shine tambayan data yi mashi don tabbatar he’s not lying,
“Yana bangaren small mom…tace bashi da lafiya…” Yafada with exergration, surprise look ne kwance kan fuskanta,
“Bai da lafiya?…” Ta tambayi kanta ahankali, yaron dai komawa yayi itama ta sauka daga kan gado ta fito falo. Zama tayi tana jiran shigowa shi har kusan minti ashirin baizoba nan take ta mike tayi hanyan part din Hajiya karama, tuna shiga falon ta fara jin sautin kukan shi,
“Ni dai Ku fadamin inda take in tafi…” Taji yana cewa, da Sauri ta dafe kirjinta saboda yanda gabanta yayi mugun faduwa,
“I need to be on my way….” Yafada cikin kuka, nan take Hajiya babba ta yanke jiki ta fada kasa tim, Wanda yasa Hajiya karama da yazid kallon wurin suka ga Hajiya kwance kasa kumfa na fitowa daga bakinta.
Har magrib dija na yawo wajen park da bag dinta, Allah ya taimaka mata bag dinta ba babba bane, babu wasu kaya ciki Sai gowns data dawo dasu daga Kano, duk inda ta ga mata nan take zuwa ta Dan raba da sun watse sai ta nemi wani wajen,har lokacin bata CI komai ba sai kalacin dataci gidan Hajiya Aisha, tana zaune kan wani benci kusa da wasu yara dake saida abinci kala na talakawa, tunanin inda zata zauna Kawai take, ji tayi wani abu NA juyawa cikin cikinta ga amai na tukanta,kusa da daya daga cikin masu saida abinci taje ta fada mata ta bata abinci na hamsin, yarinyan kallon ta tayi daga am a zuwa kasa Sannan ta maida kallonta ga abinda take saidawa, daya daga cikin robanta ta dauko ta zuba mata shinkafa babban spoon daya ta saka mata yaji da mai ta mika mata dija ta amsa ta bata hamsin cikin kudin dake cikin bag dinta Wanda ammi ta wurga mata. Gefe daya ta koma tana ci wasu da suka dan maida hankalin su kanta suna kallon ta while wasu basu damu daita ba. Tana gamaci taji abincin bai isheta ba ta kara komawa ta sai na hamsin. Atakaice saida taci kusan na Dari biyu Sannan ta koshi. Tana nan zaune har karfe goma, sai da mai saida abinci na karshe ta mike Sannan itama ta mike tana kallon titin daya fara komawa lonely, tana tafiya tana kuka tana kiran ammi, wani waje ta tsaya katon gate taga cars suna shiga suna fita itama ta kusa kai ta shiga wurin dake kama da gari guda, Ashe hospital ne, yawo Kawai take tana ganin mata da maza suna shiga suna fita, Chan nesa daita ta hangi wasu mata zazzaune da saurinta ta karasa wajen babu wacce ta maida hankalin ta kanta, ahankali tq zauna kan daya daga cikin kujerun, batafi minti biyar ba taji anacewa
“Ina masu Maryam isa?…” Da sauri mata biyu suka mike, dija tsaya kallon su tayi sai taji anacewa
“Ta haihu..an samu namiji…” Sai lokacin ta gane inda ake haihuwa ne.
Around 8:30 a falon su dad dakin yazid, dad ne zaune sai Hajiya babba data fita hayyacinta kaman ba itaba duk idanuwanta sunyi mugun kumburi hannuwanta bisa kanta sai hawaye Kawai take, opposite dinta Hajiya karama ce zaune sai yazid dake zaune kasan carpet kanshi kasa duk ya chanza, dad kura mashi ido yayi ya rasa abun cewa don sunfi hour zaune wurin nan amma ko word biyar dad bai fita ba don he’s beyond confused, banda kukan Hajiya babba babu abinda ke tashi don shi yazid a yanzu ko muryanshi bai fita sosai, saboda kuka,
“Am very disappointed in you…” Shine maganar da dad ya kara fada
“Very …very…disappointed in you….kullum kaman ustaz amma Ashe deceiving dinmu kake….gashi yanzu halin ka ya fito fili…amma Allah yaisa tsakanina dakai…ka lalata min suna…..” Dad ya fada cikin wata irin murya, yazid sai hawaye Kawai yake don he’s expecting more,
“Allah NA ganin ba irin tarbiyan danayi maka bane….I tried my best…” Ya sake fada Sannan yayi shuru saboda yanda ranshi tayi mugun baci, Hajiya karama dake hawaye tace
“Kayi hakuri…nasan kaddara ya Riga fata….am sure bai taba irin wannan abun ba…regrets is written all over him….”
“Shut up!!!!” Dad ya daka mata tsawa,
“Daman kece ke goya masu baya suyi duk abinda suke zo…” Yafada mata Hajiya karama kara fashewa tayi da kujadon maganar ba karamin bata mata brain yayi ba
“And you..ka fita kaje chan Ku karasa…babu abinda ya dameni….” Dad ya fada yana kokarin mikewa, da Sauri Hajiya babba ta tashi ta je inda yake ta rikeshi Hannu daya tasa ta goge face dinta, ahankali yazid ya daga kanshi ya kalleta yaji wani irin haushin kanshi da tausayin mom dinshi.
“Pls don’t forsake him…abinda yayi is bad…very bad..amma yanzu me zamuyi?… Abinda ya faru ya riga ya faru…let’s find solutions to this….” Tafada cikin kuka, dad tsayawa yayi yana kallon ta gwanin ban tausayi don har cikin ranshi yake jinta, hannun ta dake rike dashi ya kama,
“Wane irin solutions?… Right now am confuse…” Tafada yana shafa hannun ta,
“We should find the girl…ya aureta ko yana so ko bai so…” Tafada tana hararan yazid,
“What about the pregnancy?..” Dad ya tambayeta,
“We find her first… Maybe ina Iya kaita wajen grandma har ta haihu…kar abar iyayenta da wannan abun kunyan cos our sons mistake will ruin them…” Tafada tana kuka,
“You are the best mom in the world…” Yazid ya fada cikin ranshi, hannu dad yasa ya goge mata face dinta
“In haka kike so babu komai… Hakan zaayi…” Yafada ahankali, kallon yazid dad yayi
“Kai kuma I will surely find away to deal with you….” Ya fada mashi cikin bacin rai Sannan ya bar falon, Hajiya babba barin falon tayi tana hawaye, itama Hajiya karama mikewa tayi ta kama hannun yazid sukayi part dinta. Hajiya babba nashiga part dinta ta tarda miss call din Maman mufida rututu, nan ta zauna ta daidaita kanta Sannan ta kirata, bayan sun gaisa take fada mata ga mufida ta dawo sai kuka take kuma ta tambayeta abinda ke damunta taki ta fada mata, Hajiya shuru tayi tana tunanin kilan maganar cikin taji shiyasa tayi yaji,
“Dan Allah Ku tambayi yazid ko ya fada maku abinda ya faru tsakanin su donni nayi har na gaji…” Inji mamn mufida,
“To shikenan…” Hajiya ta amsa mata Sannan sukayi sallama, tana kashe wayan ta kira yazid, yana kwance falon Hajiya karama yana counting hours before dawn yaji ringing din wayanshi, yana ganin mom dinshi yayi saurin picking,