NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“In bakason ranka yayi mugun baci kaje ka bawa mufida hakuri… In ba haka ba Wallahi ko.gaidani karkayi….” Tana kaiwa nan ta kashe wayan ta.  Kallon agogo yayi yaga 9:00 yasan yanzu babu holdup don haka zuwa gidansu mufida won’t be difficult. Mikewa yayi ya fita ya hau mota ya kama hanyan gidansu mufida, duk ranar baici abinci ba kuma ko kadan baijin yunwa, duk Wanda ya ganshi yasan Sam baya Cikin kwanciya hankali. Cikin minti 43 ya isa kofar gidansu, bai shiga da mota ba yayi parking nan waje ya fito ya buga kofan mai gadi ya bude mashi, shiga yayi har falo yaga babu kowa, nan ya tsaya yana kwalla sallama mom din mufida ta fito suka gaisa Sam babu alaman damuwa tattare daita, tambayan mufida yayi ta nuna mashi hanyan dakinta. Mikewa yayi yabi inda ta fada mashi har bedroom dinta, ahankali ya bude kofan ya hangeta kwance tayi rub da ciki, idanuwanta bude amma ta bawa kofa baya taji an bude kofa amma batayi tunanin yazid ba, ahankali ya Kara bakin gado ya zauna tare da dafe bayanta, sai lokacin taji kamshi perfumes dinshi, da sauri ta juyo ta kalleshi, mikewa tayi zaune

“Me ya kawoka?… Ko Marin kazo ka karamin…ka fitar min daga daki….” Ahankali ya mike daga kan gado yayi kneeling bakin gadon

“Baby am so sorry… I will never hit you again… Pls forgive me…” Yafada ahankali, kura mashi ido tayi tana kallon shi, sai lokacin ta lura da irin kumvurin fuskanshi don tunda suke bata taba ganin fuskanshi haka ba, ahankali ta sauka daga kan gado ta tallabo face dinshi,

“Baby me ya sameka?…” Shine tambayan datayi mashi, tana kallon shi at the same time tanajintanajin sonshi na ratsa zuciyanta, murmushin karfin hali yayi

“Kece kika barni…” Yafada ahankali, kai ta girgiza mashi,

“pls tell me…some is wrong again.. Did you rape another gal?…” Dariya ya karayi don ba karamin dariya ta bashi ba

“Yanzu baby kin maidani irin mazan nan da basu Iya ajiye joystick dinsu waje daya?…”

“Kaga laifina ne?…AI with you anything is possible… ” ta fada ahankali,

“Now tell me…kin yafe min?….” Ya tambayeta yana kama waist dinta, hararanshi tayi tare da turo baki

“Ka bari saina huce…”

“Pls baby ki huce…mom tace in baki dawo ba kar in kara yi mata magana…so pls ijn har kinason fiddani daga fushin mom ki ki tashi ki shirya mu tafi….”

“You mean now?…”

“Yes…now…pls…”, da kyar ya shawo kanta ta yarda tabishi. Mom din mufida kam mamaki Kawai take yanda batasan abinda ya hadasu ba kuma har sun shirya, around 10:30 suka kama hanyan gidansu yazid.

part 19

38 17 5

by ummumaryam29

????????❤????????????

NA CUCE TA

????????????????????❤

®zuwairat( ummu Maryam)

1⃣9⃣

Yana tuki suna hira kaman babu abinda ya taba hadasu, yazid kam ban da tunani babu abinda yake, Wai shi yazid ne zaiyi fathering da out of wedlock, har yanzu tamkar mafarki yake don he can’t believe it, sai yanzu ya yarda don’t take yourself to be perfect, don’t feel too perfect cos in har baka bar duniya ba to baka wuce jarabawa ba,

“Ganawa kaddara….” Tafada kasan makoshinshi Wanda yasa mufida dake lumshe swollen eyes dinta kaman zatayi bacci ta kalleshi, shima kallon ta yayi ya sakar murmushin karfin hali,

“Am sorry I hit you…” Yafada kaman shine main problem dinshi,

“Nace ya wuce…” Tafada tana rike hannun shi dake kan staring, duniyar tunani ya kara fadawa, yanzu ya yarda cewa not all that glitter is gold, don before gani yake most of his friends are corrupt with dirty different characters amma duk cikin su babu mai shege sai shi, tuna how young khadija is yayi, shi har yanzu gani yake kaman dream don a nashi tunanin she can’t get pregnant. Yasan yanzu duk zaa tsaneta gidansu, yasan she will be stigmatized, he can’t wait for tomorrow, tamkar ya jawo gobe yake ji, yanzu baiji kunyan kowa kan wannan maganar, haka Allah ya kaddara mashi kuma he will take it in good faith. Sai around after 11 sukaiso gidansu, part dinshi suka shiga ta ajiye bag dinta Sannan ya kama hannun ta sukayi bangaren Hajiya babba, yasan its late amma yasan for sure mom dinshi bazatayi bacci ba. Kofan falo ya bude suka shiga yana rike da hannun mufida, bakin kofan bedroom dinta sukaje ya radawa mufida tayi sallama, tanayi mom ta amsa mata, sakin hannun ta yayi ya koma baya don har yanzu basu kebe da mom ba tunda aka fara wannan magana Sannan he’s so ashamed of himself da bazai Iya hada ido daita ba. Falo ya koma ya zauna ya dafe kai yana counting seconds to dawn.

Mufida NA shiga mom ta daga kai ta kalleta da idanuwanta da suka chanza tamkar ba nata ba, tana ganin mufida tayi saurin goge face dinta don ko kadan bata dau muryanta ba.

“Daughter kece da wannan Daren?…” Ta tambayeta ahankali, kan mufida kasa tace

“Eh…” Sannan ta durkusa ta gaida ta, amsawa tayi

: Cikin sanyin murya tana nuna mata wurin zsama kusa daita, ahankali ta zaune gefen ta, itadai mufida tunanin abinda ke damun Hajiya tayi sai kuma ta tuna kilan sai yanzu suka San abinda yazid ya aikata not knowing they is more to it. Cikin rawar murya Hajiya tace

“Kiyi hakuri kinji?… Komai mukaddari ne…haka Allah ya kaddara… Ki rike mijinki hannu bibbiyu…” Tafada tana fashewa da kuka, itama mufida fashewa tayi da kuka, ahankali Hajiya ta jawota jikinta suka bude sabon babin kuka kaman anyi mutuwa.

“Bansan irin wannan kaddara ba…ko sau daya ban taba kama yazid da wata karamin laifiba sai Kawai Ace yayi wa yar karamar yarinya ciki….” Hajiya ta fada cikin matsanacin kuka, gaban mufida yayi mugun faduwa dajin ciki, ahankali ta daga kanta daga shoulder Hajiya ta kalleta, cikin kuka Hajiya ta kalleta, surprise look dake face dinta ya tabbatar mata batasan wannan zancen ba kuma bataso ace ita ta fara sanar mata ba.

“Mom ciki gareta?…” Ta fada cikin kuka, Hajiya dafe kai tayi tana kuka,

“NA shiga uku…Hajiya gidanmu zani…ban iya zama dashi…..” Ta dinga fada kaman wata zautatta, dafa ta Hajiya tayi tana girgiza mata kai,

“Don’t say that….hannun ka bai rubewa ka yarda…mijinki ne kuma bazaki kishi saboda jarabawan Allah ba…kiyi hakuri wata rana zakiji kaman ba a taba hakan ba…” Tafada tana shafa bayanta, mufida kukan bakin ciki da kishi Kawai take, watanta biyar da yazid ko batan wata bata tabayiba, kullum tana fadawa mom dinta rashin batan watanta amma sai mom dinta ta fada mata its nothing wai itama saida tayi shekara uku Sannan ta samu cikin mufida, amma yanzu shine wata zata rigata haifawa yazid da ko ya

“Shege ne…” Ta fada cikin ranta, hakan yasa ta Dan saka ranta a inuwa amma still bata bar kuka ba. Tana cikin kuka bacci ya dauketa nan kan gadon Hajiya. Yazid kam yanda ya ga dare haka yaga rana. Haka Hajiya babba da Hajiya karama ma duk basuyi bacci ba.

Abangaren dija kam nan asibiti ta kwana inda yan waiting ke tsayawa, Allah ya taimaketa babu Wanda ya damu daita, kowa ta kanshi yake duk suna jiran yan uwansu su haihu lafiya kuma har garin Allah ya waye baa rasa mutane wajen ba, dija batayi wani baccin kirki ba saboda kuka da cizon sauro, tana fara ganin hasken gari mike ta dauki bag dinta, banda fitsari babu abinda ke damunta, kusa da wata mata dake zaune taje

“Dan…Allah… Ina.. Ake…fitsari?…” Ta tambayeta matar daga kanta tayi ta kalleta from head to toe tana mamakin me yasa zaa zo da irin wannan karamar yarinyan wajen haihuwa, wata kofa ta nuna mata batare data ce mata uffan ba. Da Sauri dija ta shiga cikin wurin rike da bag dinta don rike taje da bag dinta tamkar her life depends on it. Wurin babu laifi its neat, durkusawa tayi ahankali saboda yanda wani abu ke tokare mata maranta, tana fitsari tana wash, saboda yanda fitsari bai zuwa da yawa sai zafi da take ji ba don komai ba sai don tun jiya take jin fitsarin amma batayi ba sai yanzu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button