NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“To sai a kai injin din..amma ki kokarta muyi surfe mu wanke don mu bawa awaki su sha…” Dija turo baki tayi tana cewa

“Ammi ni marata ke ciwo…irin ciwon da yayi min wancan lokacin yake yi min…”

“To kilan bakon watanne zai zo…” Sai lokacin dija ta tuna da watan da ya gabata ta fara ganin jini Wanda ammi ta shaida mata cewa alaman girma ne.

“Wai ammi duk wata sai nayi wannan abun?..ni wallahi banason shi….” Tafada hannun ta biyu kan maranta,

“Ai lalura ne Kuma Allah ne ya dorawa mata Kuma ba din bayason mu ba…wasu ma sai sun nema amma basuyi…don haka ki bar cewa bakison shi….”

“To ammi…”

“Tunda bai kaiga zuwa ba kije kiyi sallan ishai….” Dija ta fi minti biyar kwance Sannan ta mike ta fita ta dauki buga ta shiga kewayen su da aka zagaye da buhu. Few minutes later ta Fito tana cewa

“Ammi yazo…” Tafada da karfi, ammi murmushi Kawai tayi Bata amsa mata ba.

[3:12PM, 3/20/2018] 鈥�+234 806 125 0020鈥�: 馃挏馃挍鉂ゐ煐ゐ煉欚煉�

NA CUCE TA

鉂ゐ煉滒煉涴煐ゐ煉氿煉�

庐zuwairat(ummu Maryam)

3鈨�

Da Sauri ta dawo cikin dakin tana cewa

“Ammi NA ganshi…” Tafada cikin jindadi

“Naji…wai in tambayeki…murnan me kike?….” Ammi ta tambayeta tana kallon ta,

“Babu komai…” Ta fada ahankali,

“Hmmm NA gane Kawai don bakison yin sallah ne…to kiji tsoron Allah… Maza ki tashi ki tafi makaranta….nasan an zauna tunda anyi sallan ishai….” Ammi ta fada mata, nan ta kara Bata rai tana cewa

“Ammi NA gaji…” Bata idaba ammi tayi mata dakuwa

“Kinci mai garinku…maza ki tashi ki tafi…” Ammi ta umarceta, bata fuska tayi kaman zatayi kuka ta fara cewa.

“Ammi gasu binto basu je ba?…ni ki bari sai gobe.. ” ta fada kaman zatayi kuka, baki ammi ta bude tana kallon ikon Allah, tana mamakin yanda komai sai dija ta hada kanta da kanwarta, komai Bata yarda itace babba sai tace su binto kasa da kasa

“Wai ke in tambayeki… Ke da binto waye babba?…” Ammi ta tambayeta tana kallon yanda idanuwanta suka chanza kaman zatayi kuka

“Ni…” Ta amsa mata ahankali,

“To meyasa komai sai kin hada kanki da binto?… Baki San kome kika shi su ma Zasuyi ba?… Ke ce babba son haka ki dinga daukan girma…” Ammi ta fada mata cikin lallashin,

“To ammi…” Ta fada rana turo baki don ko kadan Bata gamsu da maganar ammi ba, kullum komai ita, shiyasa kullum tana aduan Allah yasa a dauketa, har wani lokacin adua take tana cewa

“Allah kasa a saceni a kaini katon gida ko shara da wanke2 in dingayi…” Take fada duk lokacin da take tallan fura ba kaman in ta zama frustrated.

“Maza tashi kar a fara ba dake ba…” Ammi ta fada mata,

“To..ammi amma ki bani ashirin din in kashe in naje chan…”

“Ban baki ashirin… Amma ga goma…” Ammi ta fada mata tana bata naira goma daga cikin kudin data kawo, amsan kudin tayi Ta bude wata old Ghana must go ta dauko wata old and faded pant tare da kyalle ta cire pant dake jikinta ta saka Wanda ta dauko tare da tura kyallen data dauko, ta gyara daurin dankwalinta tana fita daga gidan babu hijab, tana tafiya tana kallon yara dake wasa cikin hasken wata har ta kai kusa da wani mai nama, karasawa tayi kusa da inda mutum yake

“Danmusa inayini…” Ta gaida shi tana kallon naman dake maiko a gabanshi

“Khadija ya kike?…” Inji saurayin Wanda bazai wuce shekara 18 to 20 ba

“Lafiya lau…” Ta amsa mashi ko blinking batayi saboda yanda take kallon naman, murmushi yayi

“Har kun dawo kenan?…”

“Eh…” Ta amsa mashi atakaice, har lokacin tana kallon naman tana aduan Allah yasa ya yanmata kaman yanda ya saba,

“Makaranta zaki je?..” Ya tambayeta

“Eh…”, dariya saurayin yayi yana kallon yanda take lashe baki, yanka uku ya debo ya zuba cikin takarda ya mika mata, kaman zakin daya shekara bai ci abinci ba ta miko hannu zata amsa sai saurayin ya maida hannun shi yana kallon ta Sannan yace

” yaushe zaki bani amsa ta?…” Ya tambayeta ahankali,  Dan turo baki tayi tana cewa

“Gobe…” Dariya saurayin yayi

Hmm dija sarkin wayau..kullum sai kice min gobe…to yaushe goben zai iso?…” Da Sauri tace

“Allah gobe zan baka amsa…”

“Allah ya kaimu goben… Amma in baki bani amsa ba bazan kara baki nama ba…kin amince?..” Da Sauri ta gyada mashi kai tana cewa

“NA amince…” Sai lokacin ya mika mata naman, tana amsa ta bar wajen da Sauri tana bude takarda naman, tana tafiya tana yaga kadan2 wai don kar ya kare. Haka tana zaune makaranta tana cin namanta ahankali daman she’s use to it.Har aka tashi karfe goma dija bata gama cinye naman ba saboda yanda take yagan daman ahankali. Ana tashi ta tafi gida tana hamma, daman Tasan kafin ta iso duk sunyi bacci don haka tana shiga gidan taja kaurensu da baida sakata taje ta kwanta tana tunanin yanda gobe zai kasance mata.

Yazid bai shiga apartment dinshi ba sai bayan sallan ishai daman mostly sai bayan sallan ishai yake shiga gida don quarters din is very lonely Kuma shi bayason hayaniya most especially Kuma ba yanayin halinsu daya da sauran guys din ba don mostly su da yan mata suke wining time dinsu shikuma da calling iyayenshi ko Kuma karatun alquran sai kuma kiran mufida Wanda wani lokacin da wayan yake kwantawa a kunnenshi saboda ita.

Yana shiga apartment dinshi Wanda ta hadu daga company don komai is made abroad, ko zama baiyi falo ba ya shiga daya daga cikin four bedrooms din ya cire kayan jikinshi yayi folding dinsu tamkar mace ya ajiye su cikin closet ya shiga wanka ta fito bai wani shafa mai ba ya saka jallabiya Sannan ya dauki wayanshi yayi dailing number Hajiya babba

Alokacin duk suna babban falon alhaji suna fira yara suna wasa sai sai yanmatan na chatting da wayansu ga  katon naman akuya roasted suna ci ana hira, Hajiya dauka wayan tayi yan yara suka taho wurin ta da gudu don sun san shine cos mostly lokacin yake kiran su, sallama Hajiya babba tayi ya amsa yana cewa

“My mommy good evening…”

“Evening sweetie… Ya aiki?…”

“Alhamdulillah… Ya gida da yara?…” Ya tambayeta a nutse, da Sauri yaran sukace

“Yaya ga mu….” Suka fada a chorus, Dariya yayi, Hajiya babba ta ajiye masu wayan bayan ta sashi hands free, nan suka fara labari ko wa NA bashi labarin abubuwa kala saida suka gama Sannan Hajiya babba ta dauki wayan suka fara hira tana cewa

“Son ga junior mom tana hada maka party till dawn…” Dariya yayi yace

“Small mom…nasan kina jina…banason party till dawn…” Ya fada yana Dariya,

Itama dariya tayi Sannan tace

“Kayi kadan…” Tafada cikin high voice, yanda zai jita da kyau, dariya ya karayi yana cewa

“Nidai ko kun hada ban zuwa…sai dai kuyi abunku Ku kadai…” Yafada cikin raha yana jiran amsan small mom don yasan ta da tirjewa kan abu,

“Ai kayi kadan yaro…party kam an hada an gama…” Ta fada again da karfi, alhaji kam ko kallon su baiyi sai cin naman yake yana korawa da juice while suma yan yaran suna ci suna wasa.

“Wai yaushe zaka dawo?…” Hajiya babba ta tambayeshi,

“Sai nan da sati biyu…” Ya amsa mata

“Kai yaro maza ka dawo…nan da sati biyu is too far…” Inji Hajiya karama,

“Sai lokacin hutuna zai fara…”

“Nidai ka dawo nan da sati daya…” Hajiya karama ta umarceshi,

“To momcy…” Ya amsa mata in a funny way.

“Ina twins?…” Ya tambaya, don haka yake kiran Sharif da shahid,

“Basu dawo ba…” Hajiya babba ta amsa mashi

“Aikensu akayi ko yawon ne Mara amfani?…” Ya sake tambaya, dariya Hajiya karama tayi tana cewa

“Suna waje suna shan iska….”

“Ai ba zafi ke da akwai cikin gidan ba…bari in kira su…” Ya fada Sannan sukayi sallama, kashe wayan yayi Sannan yayi dailing number shahid, alokacin Sharif na tukin mota shi Kuma shahid na zaune, yana chatting, yana ganin kiran yazid ya kalli Sharif yace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button