NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ki yafe ni…kiyi hakuri… Ki fadamin inda khadija take…. Dan Allah….” Yafada dan guntun hawaye da fitowa daga swollen eyes dinshi
Ammi tsayawa tayi tana kallon shi, kura Mashi ido tayi tana ganin nadama koina na fuskanshi, amma dayake tana da dakakken zuciya sai ta kara janye kafanta don gani take abinda ya aikatawa yarta ba abu bane wanda zaa yafe, gani take he deserves to die for what he did to her dija,
“Ka barmin…gida….” Shuru tayi tana kallon zaure da ake sallama, bata amsa ba haka shima yazid, daman Salem bai expecting a amsa don haka shigowa kawai yayi tare da mutane dake bayanshi, ammi kallon haushi da takaici tayi masu,
“Wai nace…Ku bar min…gida….wallahi.. Zan tara maku mutane….” Tafada tana tari, this time vomiting ta farayi sosai tana saukowa kan knees dinta, da sauri yazid ya mike d sauran strength dinshi shima Salem tahowa yyi da sauri ya rike shoulder dinta, ammi sai a man jini kawai take, amma sai ture hannun Salem dake shoulder dinta kawai take.
Su binto kam ko da suka fita suna ihu basu tsaya koina ba sai gidan kawu nanu,
“Kawu….kawu….wayyo Allah kawu wani mutum ne gidan mu…..kuma bamu ga amminmiu ba…dan Allah ka taho….” Binto dake haki kaman wacce ta kubuto daga bakin kura ta fadawa kawu nanu dake alwallah, kallon banza ya watsa mata,
“Wai Ku ba a koya maku gaida manya ba?…” Ya fada bbu wasa, binto dafa chest dinta tayi saboda yanda yake beating very fast,
“Kawu..amminmu….” Karamin cikinsu ya fada yana fashewa da kuka sai lokacin ya gano da akwai matsala,
“Me ya samu amminku?…” Ya tambayesu, nan binto ta kara fada Mashi abinda ta gani, kaman kar yaje don shima tsoro yakeji
Amma yayi ta maza ta mike ya shige masu gaba.
Dija tana nan kwance ta har daf da magrib, jitayi ana taba mata kafa, da sauri ta mike data tuna da inda take bacci, wata babbar mace ta gani tsaye tare da wata yarinya wacce bazata wuce 16 to 17 ba, dija hannu tasa ta goge bakinta tare da sadda kanta kasa,
“Ya akayi kike nan wajen har magrib?…ko baki samu ganin doctor bane?….” Shine tambayan datayi mata, dija ajiyan zuciya ta saki don gani take dukanta zatayi, da sauri ta gyada mata kai,
“Ke kadai kika zo ganin doctor?…” Hajiya ta kara tambayan ta, kara daga mata kai, matar tsayawa tayi ta kura mata ido for a while kaman xatace wani abu sai kuma tayi shuru tace
“To ki tashi ki tafi… Baa ganin doctor yanzu…sai in emergency ne….” Da sauri dija ta mike jikinta har rawa yake, budurwan dake tare d matar kura mata ido tayi tana kallon ta, same ita ma Hajiyan sai kallon dija dake sauri kawai take,
“Mom ni tausayinta nakeji….” Yarinya ta fada tana rike hannun mom dinta sannan ta tale baki kaman zatayi kuka, ni kuma kurawa yarinya ido nayi sai naga remarkable resemblance dinta da sultan coworker don yazid,
“Me akayi na tausayi yanzu da kike Neman kuka?…” Matar ta tambayeta suna takawa ahankali xuwa wajen wata black jeep dake tsaye,
“Mom kilan bata da mommy… Nasan inda mommy tana da uwa tare zasuzo ganin doctor….” Ta fada tana kankame hannun mom dinta, matar batace kala ba suka kusa zuwa wurin motan wani ya fito ya bude kofa amma yarinya ta tsaya
“Mom dan Allah ki sa wani doctor ya duba ta….mom daga gani ba daga nan garin ta ke ba…..” Yarinya ta fada tana buga kafa kasa,
“Zaki fara rigiman ko?… To ki shiga hankalinki ko kuma you will never set foot in this hospital again….” Ta daka mata tsawa, kuka ta fara yi tana
“Sorry mom….” Ta fada ahankali tana shiga motan,
“Shahida kiyi hakuri, da akwai mutane da yawa irun wannan… In kace zaka fara kiran doctor suna dubasu daga baya bakinka zaa gani a dinga cewa sabod you are ahead of them shine kake yi masu haka….” Ta fada tana gogewa daughter ta face dinta,
“Kin San halin mutane….” Ta karasa maganar tana jawo yar ta jikinta
Bata kara cewa komai ba driver ya jasu suka bi hanyan gate amma sai waige2 take chan ta kara ganin dija dake tafiya zata tsallaka titi tana rungume da bag dinta.
Dija na tsallakawa ta koma wajen yan matan dake saida abinci ta zauna nan kusa dasu, wani irin fitsari take ji don maranta yayi fam, zama tayi tana matse legs, da kyar ta iya bude baki ta tambayi wata inda zatayi fitsari, kallon ta yarinyan data tambaya tayi sannan tace
“Wai ke baki da gida ne?…. Jiya ma na ganki?…” Ta tambayi dija ahankali, dija shuru tayi bata ce komai ba. Ganin bazata bata amsa ba yasa itama ta daure fuska sannan tace
“Ga wani gida chan…kiyi sallama killan su barki kiyi fitsarin….”, da sauri ta mike tayi gidan da aka nuna mata, cikin Saa aka barta tayi fitsari wannan Karin ma fitsari bai fitowa sosai, tafi minti goma nan durkushe sannan taji saka ta mike ta dawo wurin yarinya mai saida abinci ta saya yanda zai isheta.
Ammi tafi minti biyar tana wanna amai duk hankalin yazid da Salem ya mugun tashi, mutum da salem ya zodashi ya fara cewa
” gaskiya sai dai a kira ambulance a tafi daita hospital wannan yafi karfin home medicine…. ” yafada Mashi atakaice, yazid dai kasa magana yayi.
“Waye nan cikin gidan?!…” Aka fada da karfi daga zauren gida Dukkansu maida hankalinsu, ammi ta kara ture hannun Salem dake shoulder dinta, da sauri yazid ya taka ahankali xuwa zaure, yana ganin babban mutum yayi kneeling cos he knows mutum family ne kuma a nashi tunanin yasan abinda ke faruwa,
“Dan Allah kuyi hakuri….Ku yafemin Ku fadamin inda khadija take….” Ya fada palm dinshi biyu harde wuri daya,
“Kai waye?….” Shine tambayan da kawu nanu ya yiwa yazid, yazid sadda kai kasa yayi sannan yace
“Ni….ni…nine….nayi….” Tari ammi ta dingayi da karfi don kar ya fada amma ko waigowa baiyi ba don shi bai gane manufar ta ba
“Ni…ne..nayi…mata…ciki….”
[6/22, 4:29 PM] ᴬᴮᵁᴮᴬᴷᴬᴿ ˢᴬᴸᴱᴴ: Na cuceta 22
by Ummu Maryam
❤????????????????????????
NA CUCE TA
????????????????????????❤
®Zuwairat (ummumaryam)
2⃣2⃣
Wattpad: ummumaryam29
Or
Visit www.ummumaryam.com for more
_Love you beautiful people_
Kawu nanu bude baki yayi don bai gane inda yazid ya nufa ba,
“Dan Allah kuyu hakuri….” Yazid ya kara cewa
“Wai ni ban gane ba….wa kayiwa ciki?….” Kawu nanu ya tambayeshi full of surprise, sadda kai kasa yazid yayi don sai yanzu ya San bai San da maganar ba, ammi sai kuka take tana
” Allah yaisa…. ”
“Ku fadamin mana…wa akayiwa ciki?….”
“Dija….” Yaji binto ta amsa mashi
Baki kawu nanu ya bude ita kuma ammi ta kara tsananta kukanta,
“Wai wace dija?…” Ya tambaya cikin tashin hankali, dukkan su shuru sukayi
“Ashe dija ciki gareta!!!!…Ashe karuwanci kika kaita?….amma ke gwadayinki ya jawowa zuriyan dan uwana abun kunya…..” Ya fada cikin fada,
“Babu…laifinta….laifinane….kuyi hakuri dan Allah….” Yazid ya fada yana hawaye. Likitan da yazid ya zo dashi kallon agogon hannunshi yayi
“Ya muke ciki….za taho da ita cikin birni ko yaya?….” Ya tambayi Salem, Salem kallon ammi yayi
“Dan Allah ki taso a kaiki asabiti….kina bukatan likita….” Salem ya fadata mata in a soft tune, ko kallon shi ammi batayi ba ta dafa bango ta mike
“Duk garin nan sai sun San abinda ki kayi…. Sai na fadawa mutanen garin nan yanda kika wulakanta rayuwa dija saboda kudi….” Kawu nanu ya fada tare da Jan tsoki sannan ya fita daga cikin gidan, da sauri yazid ya mike daga inda yake durkushe yabi bayan kawu nanu dake ruwan balai sai magana yake da karfi,