NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

Suna cikin tafiya yazid daya kwantar da seat din motan ya kwanta yace “Pls…mu wuce..Kano..pls…” Ya fadawa Salem, “Gaskiya we need to rest….kawai mu sami hotel mu samu abinci muci, muyi freshening up mu huta then first thing in the morning sai mu kama hanyan kano. ” pls banson kwanciya kan gadon hotel….” Yazid ya fada idanuwanshi lumshe, murmushi Salem yayi “Ai sai ka kwanta kasa…amma gaskiya ban Iya tuki for another 3 to four hours…in kuma zaka tuka motan you are welcome… Sai na iso….” Ya amsa Mashi atakaice, yazid dai bai kara cewa komai ba, kawai yana tunani yanda duniya ta chanza Mashi farat daya ya koma bai da kowa sai Salem then Hajiya karama itama tunda ya kashe wayanshi bata kara kiran shi ba yasan fushi take cos he knows how upset she can easily be. “Khadija….

Where are you?….” Ya fada ahankali. Salem dai bai kalleshi ba har ya hangi wata babba hotel ya juya yayi wurin, parking yayi a parking lot bayan an bude masu gate, fita yayi ya shiga, reception ya nufa yayi booking daki for a night aka nuna Mashi dakin duk yazid na kwance cikin mota. Sai da ya shiga dakin ya watsa ruwa sannan ya fito ya sauka downstairs. Wurin yazid yaje yaga kaman ya fara bacci, tapping dinshi yayi yabude ido ahankali, “Muje…” Ya fada Mashi, hannu yazid ya mika Mashi Salem ya amshi hannun tare da jawoshi waje, jingina yayi da mota Salem ya kulle mota ya rike Mashi hannu suka koma ciki “Duk ka maida kanka kaman wani patient… You better be easy on yourself before you die for nothing….” Salem Ya fada yana hada Mashi ruwan wanka.

Dija kam tunda ta ga yazid abun da yayi mata ya dawo mata saboda, tana tafia tana goge hawaye, “Allah yaisa….da yanzu ammai bata koreni ba…” Tafada tana tunanin ba don abinda yayi mata ba da tana a small but happy and sweet home da siblings dinta, kara goge face dinta tayi amma hawaye bai daina fitowa ba, a wannan ranar ko low diet dinner data sabaci bata ci ba saboda bakin ciki da Kuma ciwon jikin don duk ilahirin jikinta hurts like hell, yau data koma labour room waiting area sai taga babu komai, it felt so lonely and scary, mai gadin wajen ne kawai zaune, bata je wurin ba ta koma baya, cikin hospital ta dinga yawo tana ganin mutane jefi2 inada ta kwanta jiya da rana taje taga babu kowa amma da akwai florescent light wajen, babu kowa wurin amma hasken wurin makes it a little less scary, wajen ta nufa ta ajiye bag dinta a jikin bango ta kwanta yanda ko mutum ya zo wurin bazai ganta ba, tana kuka tana kiran ammi har Bacci yayi gaba daita.

The following day around 12 a compound din gidansu yazid shareef zaune kusa da shahid kan mota, inda suke zaune yana kallon bakin gate, wayan hannun shahid ya nunawa shareef,”Ka gane wannan yarinya?….” Shahid ya tambayi Sharif,”Yes…kam hanan ko?…””Yes itace…kasan I have special plans for her….saboda abinda tayimin jiya a school in har na kamata sai na bata banana that will last her for eternity….” Shahid Ya fada sounding very mean, dariya shareef yayi”Ina zaka kamata?…” Sharif ya tambayi shahid, dariyan mugunta yayi”A wurin convocation party da zaayi zan bata ecstasy pills…” Bai idaba Asabe ta fito daga part din Hajiya karama zata part din Hajiya babba, dariya sukayi tare sannan Sharif yace”Ni kuma am so Hungry for this gal…

I wish I will have her for just a night…” Ya fada yana kallon Asabe dake tafiya waist dinta na shaking ahankali, dariya suka karayi sannan Shahid yace”Ka mance the last time da muka samu wannan yarinya ta dinga yi mana ihu….Allah ya taimaka grandma bata gida data…..” Bai idaba akayi horn a bakin gateShuru sukayi tare da maida hankalinsu ga gate don ganin Wanda ke tahowa, maigadine ya bude gate motan Salem ya shigo,”Abokin ustaz ne….” Inji Sharif, basu ga yazid ba kasancewan yana kwance, saida Salem yayi parking sannan ya fito ya zagaya ya bude kofa tare da tada yazid da yanzu yanayinshi is becoming scary, ahankali yazid ya fidda kafa daya zai fito amma duk ilahirin jikinshi sai rawa yake kaman irin people da old age, Salem kamashi yayi ya fito ya tallaboshi suka fara tafiya ahankali, Sharif kallon shahid yayi”Wai shi da waye wancan?…” Ya fada don ko kadan basu kawo wa Kansu yazid ne ba, ganin yanda Salem kadai bai Iya tafiya dashi don almost dukkan jikinshi ya sakar Mashi, Salem kallon su Sharif yayi”Pls you guys should give me a hand….” Ya nemi taimakonsu, sai lokacin suka diro daga bayan motan suna wondering who it could be, suna karasowa suka ga yazid ne, da sauri suka kwaceshi daga hannun Salem”What’s wrong with him!!!…” Sharif ya fada da karfi, Salem baice komai ba”Yaya!…meya sameka?…”

Shine questions da suke jera Mashi while suna rike dashi from both sides, ba karamin tashi hankalunsu yayi ba cos basu taba ganin dan uwansu haka ba,”Pls somebody should say something!…” Sharif ya fada sounding very tensed amma babu Wanda yace komai, kofan part dinshi Salem ya bude suka shiga ciki, kan three seater suka kwantar dashi kowannensu ya fito da gudu, Sharif part din dad yayi da gudu while shahid yayi part din Hajiya babba shima aguje, da ihu shahid ke kiran big mom da small mom, da sauri small mom ta mike ta tari shahid,”Moms…Ku taho…yaya isa critically sick… Yanzu nan yaya Salem ya shigo dashi….” Ya fada yana haki, dan dakatawa yayi yana kallon mom dinsu that looks so emaciated, sai lokacin ya lura da yanda ta koma, sannan yana kallon I don’t care looks on her face dayayi maganar yazid,”Mom bakuji bane?…. Yaya baida….” Bai idaba yaga big mom ta mike ta kama hanyan bedroom dinta”Mommy!!!…” Ya kwala mata kira amma ko juyowa batayi ba ta shige abinta, kallon small mom data sadda kai kasa yayi”Small mom…what’s happening?…” Shine tambayan dayayi mata yana shafa kanshi back and fro,”Ina yazid din?…”

Small mom ta tambayeshi, bai amsa ba yace”Small mom I know something is wrong… Nasan big mom bata wasa da yaya… So pls Ku fadamin abinda ke faruwa,…” Hajiya karama bata saurareshi ba ta fita zuwa part din yazid, shima sharef na zuwa part din dad ya tarda shi zaune yana karatu, shima cikin tashin hankali ya sanar da dad abinda ke tafe dashi, ko kallon shi dad baiyi ba,”Dad…am talking to you… Yaya…””Ka bar min wuri kafin ranka ya baci….” Dad ya daga kai tare da daka Mashi tsawa, surprise look ne kwance kan fuskan Sharif,”Dad am talking about yaya yazid fa…””Wai baka wucewa!…” Dad ya kara daga Mashi tsawa, aikam gefe daya ya koma yana buga kafa a kasa yana cewa”Dad ka taho mu tafi…hes in critical conditions… Pls dad…in ma da laifin da yayi maka kayi hakuri….” Bai idaba yaga dad ya Ciro palm sandal dake kafanshi ya biyoshi da gudu, shima aguje ya bar wurin yana mamakin abinda ke faruwa.

Hajiya karama zama tayi bakin kujeran da yazid ke zaune”Yanzu son kashe kanka zakayi?…you want to kill yourself?….so we are all worthless to you… Bamu da amfani wajenkako?…” Ta fada hannunta dafe da forehead dinshi dake harbawa, shahid dai yana tsaye yana jin abinda take cewa amma baisan manufarta ba”Gaskiya he needs a doc,…tun shekaranjiya da muka bar nan baici komai ba…” Inji Salem, Hajiya karama daga wayanta tayi tare da dailing number doctor, aguje Sharif ya kara shigowa yana kallon yazid dake kwance sai nishi yake, kallon shahid yayi”Ina big mom?…” Ya tambayeshi”She’s not coming….”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button