NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sorry…ki bani tea…zansha …” Ya fada don kar ya bata mata rai kuma Mikewa tazoyi ya Kara riketa, “Baby ki bari sai later…I miss you a lot….” Yafada ba don in zata bukaceshi zai Iya komai ba amma don ya nuna mata how much he cares, hannu ta Dora kan tummy dinshi that is so flat “Kalli yanda cikinka ya hade da bayanka….pls ni dai bari in hado maka tea din….” Bai kara cewa komai ba ya saketa ta mike shi kuma ya koma ya kwanta.

Direct Sharif da shahid suka shiga part din dad dinsu ba ko sallama, sai wani cika suke suna basarwa, big mom ce zaune tana magana da dad while Hajiya karama tana sauron su. Mom shuru tayi tana kallon su, kowannensu tsayawa yayi suma sun zuba masu idanu “Wai kuna haukane zaku shigo babu sallama sannan kunyi ma mutane tsaye?…” Hajiya karama ta fada cikin fada, “Munzo jin abinda ke faruwa ne….” Sharif ya fada yana daga gira daya, dad dinsu kam ya cika yayi fam “Kambu…amma wallahi zanyi maganinku yanzu nan in har Baku bar wajen nan yanzu ba…” Hajiya karama ta fada kaman zata tashi sama “Ai in mun bar wajen nan to kun gaya mana abinda ke faruwa… Dalilin dayasa yaya bai da lafiya amma duk baku damu dashi ba….ai muma yan gidan nan ne kuma we are no more kids….” Shahid ya fada atakaice sannan ya kalli Sharif yace “Ko ba haka bane?…” Ya tambayeshi da sauri Sharif yace “Haka ne …” Hajiya karama ji tayi kaman ta mike taci ubansu amma dad ya daga mata hannu alaman ta kyalesu, mom kam ko kallon su batayi ba balle su bata mata rai, dad daukan wayan dake gefenshi yayi sannan yayi dailing wata number, few seconds later ya fara cewa “Yauwa inspector… Ka taimaka ta turomin 4 police…” Sharif kallon shahid yayi shima shahid ya kalli Sharif suka yiwa junansu magana da ido suka juya, dad dinsu dakatawa yayi da wayan “Ku tsaya mana manya…you have some nerves…idiots…” Ya fada sannan ya ajiy wayan, daman he wasn’t making any Call Suna fita suka tsaya “Meye abunyi…nifa am disturbed… I really what to know abinda ke faruwa…dukda wannan ustaz yana hanamu walawa amma he’s our brother….” Inji shahid, ajiyan zuciya Sharif ya sauke “Nima I really want to know… Amma since it seems secret mu kyalle…in yayi tsami munji…” Ya fada given up “No gaskiya… We need to know… Duk sun raina mana hankali …har yanzu kallon yara suke mana.. They don’t think we are matured balle suyi sharing family problems damu…and were are the second born of this family…” Inji shahid, “Then me xamuyi?…” Sharif ya tambayeshi, shuru yayi for a while sannan yace “I know what to do…muje wajen grand ma….am sure mun San yanda zamuyi tormenting dinta har fada mana….” Yfada yana murmushin keta “Yes ni ban ma tuna ta ba…she’s our only hope… amma wait what if bata San abinda ke faruwa ba…” “Sai mu tisata gaba tazo ta tambayar mana…” Dariya shahid yayi yana cewa “Yau ana yinta kenan…” Kenan.

Abangaren dija kam ji tayi ana taba mata kafa tayi saurin mikewa, wata cleaner ta gani da kayan aiki, “Ke lafiya kike kwance nan?… Ko duk salon saurin zuwan ne?…” Matar ta fada, ita dai dija bata ce komai bai sai saurin take ta mike, ji tayi kanta yayi mata dummm, jikinta rau da zafi, bag dinta ta dauka ta fara tafiya ita kuma matar ta tsaya tana kallon ta. Dija ji tayi duk ilahirin jikinta babu abinda yake mata sai ciwo, ankles dinta kaman an takasu, kawai sai ta fara breakfast da kuka, tana tafiya tana kira ammi cikin ranta, ji tayi she still want to lay down, tana tafiya tana kallon ko da akwai inda zata dan zauna for a while. Wani wuri ta gani still cikin hospital din, wurin ta nufa ta zauna tare da hada kanta da gwaiwa, sabon babin kuka tabude, babu abinda take kira sai ammi kaman yau ta bar gida tajeji, tana kuka tana taba jikinta tqnq imagining what sort of hotness is this? Cikinta ne yayi motsi tayi sauri dakata da kuka tana saurraron motsin, still wani motsin ta karaji, ahankali ta Dora hannu kan cikin ta,

for the very first time dataji abu yayi portraying a cikinta, goge face dinta tayi ta rike cikinta da two hands dinta, kalle2 ta danyi don tabbatar da babu mai kallon ta, hannu tasa cikin riganta tana shafa cikin ta, still abunda ke cikinta sai motsi yake, ko a lokacin dija batayi tunanin dane cikin cikinta ba, sai da cikinta ya motsa for almost 8 times sannan yayi still. Sai lokacin ta cire hannunta ta cigaba da kukanta “Gida nakeso….” Kawai take cewa. Kafin karfe seven na Safiya fever ya rufeta sosai don babu abinda take sai rawan sanyi, gashi rabonta da abinci tun kafin taga yazid. Ganin masu wucewa da yawa suna kallon ta yasa tayi karfin halin mikewa ta bar wajen tana tafiya kaman Kazan da ruwan sama ya doka sai rawa jikinta yake, sai da ta kai bakin titi ta tsaya tana kalle2 wani chemist ta tsaya kallon mai wurin yana budewa tana ganin ya gama budewa ta taka ahankali ta shiga wajen har lokacin bata bar kuka ba, mai wajen dake dusting wurin zaman shi ya daga kai yana kallon ta, ganin batace komai ba sai kuka yasashi cewa “Lafiya baiwar Allah?…” Ya tambayeta yana zama, bakin dija na rawa ta fara cewa “Ma…ga…ni…zaa…bani….” Ta fada tana kokarin daidaita kukanta, saurayin tsaya kallon face dinta yayi sannan yana kallon how swollen her lips is, “Maganin me?…” Ya tambayeta, shuru tayi tana tuna yanda ammi ke aikenta siyan maganin musassara, “Na…musassara….” Ta amsa Mashi, still tsaya kallon beautiful but sad face dinta yayi “Wa ya aikoki?…” Ya sake tambayanta, kai kawai ta girgiza Mashi alaman babu Wanda ya aikota “Me ke damunki?…” “Jikina…ke…ciwo….” Ta fada tana kuka, “Ina mamanki?…” “Tana….gida….” Tayi Mashi karya “Kinci abinci?….” Kai ta girgiza Mashi, “To…zan baki magani….amma ki tabbatar kinci abinci kafin kisha…kinji ko?…” Da sauri ta gyada Mashi kai, mikewa yayi ya tattara mata drugs. Nuna mata yanda zatasha yayi sannan ya mika mata. “Nawa?…” Ta tambayeshu gwanin ban tausayi, kura mata ido yayi for a moment sannan yace “Ki barshi…yi sauri ki koma gida kici abinci sai kisha maganin ki kwanta…kinjiko?….” Ya fada mata sounding very caring, ahankali ta gyada Mashi kai. “Na….go…de….” Ta fada sannan ta juya ta bar wajen.

[6/22, 4:34 PM] ᴬᴮᵁᴮᴬᴷᴬᴿ ˢᴬᴸᴱᴴ: NA CUCETA 25

by Ibraheem

????????????????????❤???? NA CUCE TA ❤????????????????????????

®Zuwairat ( ummumaryam)

2⃣5⃣

Tafiya tayi for about 5 minutes taji legs dinta sun gaji, bakin wani closed shop ta zaune ahankali sai shessheka take, ji take kaman ta hau titi ko mota yabi ta kanta ta huta, bayan kaman mintu goma ta kara mikewa this time wani shop ta nufa ta sayi small bread da ruwa, ahankali ta koma gefe daya ta bude fara ci, nan take ta fara vomiting kaman babu gobe, sabon kuka ta fara tana rike cikinta “Wayyo cikina….ammi…cikina…”

Ta dinga maimaitawa while tana amai, tana gamawa ta zame ta kwanta nan wajen batare data sha maganin ba. At that same time itama ammi tana chan tana kuka, already mutane gidan sun San abinda ya sami dija, kuma ba karamin fada da tsinuwa tasha wajen danginta ba don cewa sukayi tafi dija laifi, tunda tazo take kuka don gani take dija is no more,

she hates herself so much that she wish death should take her away, babu mai kallon ta balle ya rarrasheta cos duk haushinta sukeji, at that moment da dija ke kwance kaman zata mutu itama ammi na kwance tana kuka tana kiran sunan dija, “Dija ki yafemin…” Kawai take maimaitawa, “Allah ka karemin dija in dai tana da rai…..Allah ka tsaremin dija indai bata mutu ….”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button