NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ta fada tana kuka, “Wai baki yiwa mutane shuru?…bake kika koreta tabi duniya ba?… Kukan me zakiyi kuma?… Kawai ki zuba ruwa kasa kisha….” Inji wata tsohuwa mai kama da ammi,cikin kuka ammi ta dinga cewa “Yau ina jin dija cikin jikina….ina ji kaman wani abu ya sameta….” Tafada cikin matsanacin kuka, baki tsohuwar ta tabe “Ba sai ki ji dadi ba….ai sai ki zuba ruwa kasa kisha….
In ba keba wacece zata yanka hannunta ta yar koda kuwa hannun ya rube…..amma ke kika Iya korar marainiyar Allah bayan zaluncin data fuskanta….da akwai hisabi tsakanin ki da ita…kawai ki jira ki gani……” Tsohuwar ta fada sannan ta bar mata creepy and disgusting room wanda babu kamshin abinda ke tashi sai na tsamin furan daya kwana. “Ni dai…Ku taimaka Ku nemomin dija….wallahi nayi kuskure…
” Ta fada tana kuka “Ina jin da akwai abinda ke samun dija…ina ji a jikina….” Ta dinga maimaitawa.
Itama dija dukda tana kwance nan kasa idanuwanta rufe amma bata bar kiran ammi ba, hawaye da fita daga closed eyes dinta. Sai nishi kawai take tana haki kaman wacce tayi gudu while two hands dinta rike da tummy dinta
Wajen karfe biyar na maraice su Sharif suka iso gidan grandma dinsu dake hotoro Sukaje, kusa da bakin kofan falo sukayi parking motarsu instead of parking lot, ba komai yasa sukayi hakan ba sai don plan din da sukayi saboda abunda ke tafe dasu.
Falon old woman din suka shiga suka tardata ta kurawa arewa 24 ido da medical specks a face dinta. Daga kai tayi tana cewa “Wane arnene ya shigo babu sallama?…” Ta fada cikin tsiwa dukda tasan sune amma dayake itama ba daga bayaba. “Arnayen jikokinki ne?…”
Suka amsa mata suna zama both side dinta, tsoki taja “Wai Ku yaushe zakuyi hankali…?” Ta fada tana juyowa tana kallon faces dinsu one after the other, “Lokacin da jakkuna sukayi kaho…” Sharif ya amsa mata as usual, “Murja!!!!….” Shahid ya kwalawa wata kira, Wanda saida tsohuwar ta Dade kunnenta sabida kara cos sun San ko kadan bata kaunar hayaniya. Da sauri yarinyan da aka kira da Murja ta fito da gudu har jikinta na rawa don tasan ko suwaye, “Ki kawo mana abunsh…” Shahid ya fada mata, da sauri ta juya, su kuma suka kalli juna tare da fashewa da dariya, ko na meye oho.
Ko da yarinyan ta kawo masu kunun aya dariya suka sake yi duk sun takurawa baiwar Allah dake zaune tsakiyansu, saida sukasha sannan Sharif yayiwa shahid alama da ido, ahankali shahid ya dauke wayan grandma dake kusa dashi ya saka cikin aljihunshi sannan Sharif ya fara cewa, “Inna…munzo ne dan Allah ki fada mana abind ke faruwa chan gidnmu…” Ya fada mata sounding very stubborn, tsohuwar gyara zaman specks dinta tayi sannan tace “Ban ganeba….meke faruwa?… ” ta tambayesu tana kallon faces dinsu “Oho…muma bamu Sani ba…inda mun sani ai baki ganinmu nan…” Inii Sharif, dakuwa ta sakar Mashi a fuska tana cewa “Kaci uban daya haifeka….ni kake cewa oho?….ni Saar ubanka ne?…
Ku tashi Ku tafi kafin in kira ubanku….” Ta fada tana dungurin Sharif a goshi, shikam shahid rike baki yayi yana dariya, saida ta gama balbaleshi sannan shahid yace “Inna baki gane ba…yaya yazid ne bai da lafiya…Kuma duk yan gidan basu damu dashi ba,…ko zuwa inda yake basuyi ba…shine mukace muzo mu tambayeki ko zaki fada mana abinda ke faruwa….” Kallon banza ta watsa Mashi “To ban Sani ba…Ku tashi Ku bani wuri….” Kallon juna su kayi, Dukkansu mikewa sukayi, “Wallahi sai kin fada mana…ko kuma mu saka waka….” Inji Sharif, “Kun Dade Baku saka wakan ba…” Ta fada tana gyara zamanta, remote dinta suka dauka suka chanza zuwa tashan boom TV, suka saka waka sannan suka saka a highest volume, tsohuwa zaro idanuwa tayi tare da dafe kanta, da sauri ta mike ta kashe kallon tana neman wayanta don kiran dad dinsu amma bata ganshiba, gefe daya suka koma tare da folding hands dinsu a chest sukayi tsaye suna kallon tsohuwa tana birkita inda ta zauna, daga kai tayi ta kallesu “Dangin firauna ina kuka kaimin waya?…” Ta fada tana gyara daurin zaninta, “Ai inna ki fada mana kawai sai mu baki wayanki tare da bar maki gida….” Shahid ya fada atakaice, tsohuwar zama tayi bata ko kallesu ba Ganin Sharif ya nufi wajen kayan kallon zai kara kunnawa yasa ta mike “Kana kunnawa sai da tsinewa ubanka…. ” ta fada kaman zata sauce,
“Ai danki ne…in kin tsine Mashi matsalan ki…” Inji shahid dake jingine da bango yana dariya, Sharif kara kunnanawa yayi ya kara kura volume, ta bishi ya gudu ta koma kashe suka kara komawa, babu irin zagin da basu sha ba amma kememe suka ki rabuwa da ita har saida ta gaji da kashe kayan kallon ta zauna tana haki kaman wacce tayi race, “Wallahi ban san abinda ya fara ba…uban Ku bai fada min ba…” Ta rasa maganar da zagi, rage volume sukayi sannan shahid yace “An ma rainaki wallahi… Yanzu bari in dauko maki hijjab mu kaiki har gida ki jiyo abinda ke faruwa….” “To Ku fara bani wayata….” Ta fada masu, kallon juna sukayi suka tuntsure da dariya
“This old woman wants to use sense on us….” Sharif ya fada yana dariya “Ai inna in kin ga na baki wannan wayan to mun isa chan Gidan….” Inji shahid, daman tacika tayi fam kuma tana bukatar gaya danta yayi mata iyaka da su, Murja ta kira ta dauko mata hijab, few seconds later ta fito da hijab, fixgan hijabin tayi daga hannun Murja ta Dora a shoulder dinta ta tashi kaman zata tashi sama tayi waje, kallon murja dake tattare cups sukayi Sharif yace “Babe ya ranar nan?…” Ya tambayeta yana daga mata gira, batace kala ba sai dariya suke da sauri ta kwace cups, “Babe kilan mu dawo da mun ajiye Hajiya…
Me kike so…” Inji shahid, har ta shiga kitchen ta leko ta watsa masu disgusting look sannan ta shige, kara dariya sukayi sannan shahid yace “Kin harari uwarki da ubanki…” “Don’t mind her ta samu fresh boys sai yanga take…remember she wasn’t a virgin….” Inji Sharif, cikin dariya shahid yace. “Kilan she’s jealous of the gal we brought here last….” Bai idaba Hajiya ta dankara Masu ashar Wanda yasasu barin wurin. Suna kaiwa gida sukayi parking sannan suka bata wayan ta, tana fitowa ta fara kwallawa dad kira tundaga waje “Isa!… Isah!!!….” Kawai take fada da karfi, yaran gidan dake wasa a falon Hajiya babba fitowa sukayi da gudu “Inna lafiya?….” Daya daga cikin su ta tambayeta, “Kin ci ubanki….ina ubanku yake….” Tafada tana tafiya irin na old people sannan har lokacin hijjab dinta na kan shoulder dinta, dad ne ya fito, yaga mom dinshi sai zazzaga balai take, tana ganin shi ta fara “Wallahi kayi min iyaka dukkan yaranka…kar shegen daya kara takamin gidan….kar ka kuskura su kara zuwa gidana…” Ta fada tana wuceshi zuwa part dinshi, dad dai tsaye yayi ya rasa inda ta dosa, bin bayanta yayi “Wani abu akayi maki?…” Ya tambayeta in a soft tune, “Ni dai kayi min iyaka da yaranka kawai…mussaman wayan nan masu kama da shaidanun….” Tafada tana shigewa falonshi, shima shiga yayi.
Su mom ma zuwa sukayi suka gaidata amma ko amsawa batayi ba sai balai kawai take tana ya rabata da yaranshi, sai datayi mai isanta sannan tace “Ina yazidu?…” “Yana bangarenshi…” Hajiya karama ta amsa mata, “To ubanme yayi maku kuka ki kula dashi bayan ance baida lafiya?….” Ta tambayesu atakaice, dukkan su shuru sukayi sai dad yayi karfin halin cewa “Wa ya kai maki wannan maganar?…” Dakuwa tayi Mashi “Wato dai gaskia ne baida lafiya kuma Baku kulawa dashi…to Ku fadamin abinda yayi maku….” Ta kara tambayansu, dad zama yayi yana Neman hukuncin daya dace da dasu Sharif don yasan its their hands doing.