NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“You are talking kaman bakasan halin dad ba….yana wasa da maganar wannan tsohuwar ne?….kasan what ever she says is final…ni dai am scared… Allah yasa kar dad yayi cutting allowance dinmu….” Inji sharif, shuru ya dan biyo baya for a moment sannan Sharif ya saki wani dan iskan murmushi tare da cewa

“Wai is it true yaya yayiwa wata ciki?…. I still can believe this….” Yafada with amusement, shima shahid dariya yayi yana cewa

“Amma yaya is a disappointment… Ji yanda ya rame kaman kanshi farau….mtwsss….”

“Novice ne…don da gani he’s regretting it….” Dariya sukayi duka, wayan shahid ne ya fara ringing,

“The boss is calling…” Ya fada yana nunawa sharif screen din wayan,

“Wallahi wannan tsohuwar najadun ta ja mana….” Inji sharif yana kallon screen din wayan da aka rubuta my hero, which means their dad, yana picking yayi saurin saka a loud speaker,

“H….” Bai karasa ba dad dinsu yace

“Ku sameni now!!!…” Yana kaiwa nan ya katse wayan. Kallon juna sukayi sharif ya hadiyi wani abu sabida tsoro, shahid hannu ya Dora bisa kai, few seconds later yace.

“See we have to be bold… We shouldn’t look suspicious….” Inji shahid dake juya kan mota zuwa gida.

Dija na nan kwance har karfe 10, wani irin bacci mai nauyi ya kara daukata amma ba mai dadi ba, taba bacci tana firgita,   kudundune kanta tayi sabida sanyin da takeji amma rana da fara dukan jikinta ta fara jin dadi amma fever da takeji kara rising yake don inda zaa aunata da thermometer sai ta bawa 48 baya, abunka da jos babu mai maida hankali kanta, kowa ta kanshi yake amma wasu sukan tsaya su kalleta for just few seconds sai su wuce while wasu ko inda take basu kallo, ahankali ta bude idanuwanta da sukayi mata nauyi, ganin mutane na wucewa da yawa yasa tayi karfin halin mikewa zaune, kokarin mikewa tayi amma she couldn’t, da crawling ta koma jikin wani bango dake gefe daya ta Jingina, duk abinda ke faruwa tana rike da bag dinta tare da drugs and sauran bread data saya, she never needs her mother the way she needs her now, she don’t want anything, kawai abinda takeso is someone she can hold on to, somebody that will hold her back,

“Ammi….” Tafada ahankali tana nishi, maganin da aka bata ta dauko, ahankali ta daga kai ta yiwa mai saida ruwa alaman yazo da hannunta, da sauri yaron ya kawo ruwa ta mika Mashi goma ya bata ruwa daya batare datace uffanba, maganin ta balla ta saka a baki sannan tasha ruwa, bread tayi kokarin ci saboda yanda cikinta ke crumbling amma ta kasa, kara daga kai tayi tana kallon masu wucewa ko Allah yasa taga abinda zatayi shaawanci Allah so kind sai ta hangi mai saida gurasa, sai taji she can eat it despite her lost of appepite, kiranshi tayi ya zo ta sayi na hamsin, ko rabi bataciba ta ajiye sauran gefe daya, inda ta jingina babu rana so she was so cold, hawaye ne ya kara gangaro mata.

Ahankali ta daga hannunta ta goge, tana gogewa wasu na fitowa, yanzu takejin rashin uwar tattare daita, she’s missing her family like crazy, adua take ko Allah yasa taga mutum daya Wanda tasani, she really needs a comforter, she’s so lonely, she is wondering how cruel and wicked the world is, gata yar yarinya in pain and agony amma no body cares, gani take inda zata mutu nan babu bai bin ta kan gawanta,

“Mutuwa…kazo…dan Allah…..” Ta fada sounding so feed up. Tana nan zaune har karfe sha biyu inda taji wannan fever ya sauka, amma she still feels weak, ganin babu mai damunta kan ta tashi inda take zaune yasa ta kara relaxing, bag dinta ta ajiye kayi tayi pillow dashi, few minutes later bacci ya kara dauketa.

Bata farka ba sai bayan asr, mikewa tayi taji jikinta da sauki sosai, tanason dan yawo kaman yanda ta saba amma gani take zata hadu da yazid, har yanzu sunanshi bai zauna mata sosai ba, at times she recall Yasir wani lokacin Kuma ta tuna hes yazid not Yasir,

“Allah yasa kar in ganshi….” Ta fada tana tashi tsaye daga inda take zaune.

Bayan sallan magrib dad ne zaune ya hada tagumi sai Hajiya karama da Hajiya babba da suke zaune both side dinshi, then inna dake zaune kan kujera da plate hannunta tana cin tuwo shinkafa sai fada take wai bai yi taushi ba

“Wai tuwon shinkafan sai gris…gris…yake…mata babu abinda suka Iya…..ko danko tuwon baiyi ba.. Ko saurin uban mu kuke oho….”tafada tana kai loma Kuma from all indication tana jin dadin abincin amma she cant stop complaining, Hajiya babba bata daga kai ba don abinda ya dameta daban, ita Kuma Hajiya karama kallon ta tayi ta watsa mata annoying look batare data bari ta ganiba, sallama akayi Hajiya karama ta daga kai ta amsama su sharif dake sanye da jallabiya kaman wasu ustazai, don suna dawowa suka tarda dad zai fita masjid, suma da sauri suka karasa tare da  watsa ruwa suka tafi masjid, kowanne da tunanin dayake, direct daga masjid part din dad sukayi. Itadai Hajiya karama tasan abinda ke nan amma Hajiya babba bata Sani ba cos bata nan lokacin da inna ta fasa wannan kai, inna na ganin su shigo dakin ta daga kai ta watsawa each and everyone dinsu harara tare dacewa

” shegu Ashe kuna sallama…dayake ni kun raina ni….” Tafada masu, basu kalli inda take ba suka samu gefe daya suka rakube, sunfi minti biyar da zama sannan dad ya daga kai idanuwanshi kaman garwashi ya fara cewa

“Ba…..” Da sauri inna ta daga Mashi hannu,

“Me zakayi?….”

“Magana zanyi masu… ”

“Ina yazidu?… Ai shine babba… Don haka…kome zaayi dole a kirashi….” Inna ta fada atakaice, dad dai baiso hakan ba amma bai yiwa inna gardama don haka ya umarci shahid ya kirawo yazid, Shahid na zama shima ya shigo da sallama ya samu wuri ya zauna tare da mike legs dinshi sannan ya soka hands dinshi cikin cinyanshi, kanshi kasa, daman yana shigowa dad ya kara hade rai, saida kowa yayi settling sannan dad ya fara cewa

“The reason Dana kirawo Ku nan is not for anything sai don Ku biyu….” Ya fada yana nuna sharif da shahid, gabansu ne ya kara faduwa, matsawa shahid yayi kusa da Sharif ya Dora hannunshi kan hannun sharif dake kasan tiles,

“Na Baku nan da sati biyu kowannen Ku ya fiddo matar aure!!…..” A razane su shahid suka daga kai suna kallon dad, surprise look ne kwance kan face din Hajiya babba, Hajiya karama tayi saurin cewa

“For what?….” Bata idaba inna ta katseta dacewa

“For meye?….basu isa auren bane?….ko da akwai abinda shegun yaran nan basu Sani ba?….” Shi kam yazid eyes dinshi lumshe Kuma tunda ya shigo falon bai daga kai ba,

“Gaskiya ni ban son aure….” Sharif ya fada

“Nima wallahi am not ready for marriage….” Inji shahid,

“Kai!!!….” Dad dinsu ya daka masu tsawa,

“Ina wasa daku?….” Da sauri suka girgiza kai,

“Then kowanne ya fiddo wacce yake so ko Kuma ni in zabar maku….” Dad ya fada atakaice,

“Ni wallahi bani da wacce nake so….” Shahid ya fada kaman zaiyi kuka at the same time yana harara inna dake lashe hannunta kaman babu gobe,

“To ai an gama…isa ka bari ni zan zaba masu mata cikin dangi…..” Inji inna dake ajiye empty plate dake hannunta kasa, da sauri suka mike,

“Wallahi bamu son aure…yanzu ….” Suka  fada in chorus,

“Sit now!!….” Dad ya daka masu tsawa, da sauri suka koma suka zaune, yazid dai ko uffan baice ba cos hes absent minded,

“Bakuson aure kuke bin Matan banza?…” Inji inna, da sauri suka daga kai suka kalleta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button