NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Mu!!!!!” Suka fada tare kaman basu San abinda take cewa ba, itama Hajiya babba daga kai tayi tana kallon inna cikin tashin hankali
“Inna matan banza Kuma?…”
“Eh sharri zanyi masu?…to aure babu fashi… Sai anyi ko kuna so ko baku so….” Tayi directing maganar ta to su Hajiya, Da sauri hajia babba ta mike tana cewa
“Nifa ban gane abinda ke faruwa nan ba….” Itama inna mikewa tayi
“To dukana zakiyi ne….naga kin tashi tsaye,…” Kallonta dad yayi ta koma ta zauna
“Mu wallahi babu ruwanmu….sharri take mana….” Inji shahid, hannu innata Dora bisa kai,
“Ni kuke kira da makaryaciya?…..inna lillahi…..isa kana ganin yaranka suna kirana da makaryaciya?….” Inna ta fada kaman zatayi kuka, hararanta Hajiya karama tayi,
“To gaskiya baa yiwa wayan nan yaran da basu mallaki hankalinsu ba aure….how old are they?….ni dai ….”
“Keep quite!!….” Dad ya daka mata tsawa sannan ya maida hankali shi kan su shahid
“Both of you are getting married in the next two months… That’s final…” Inji dad
Hannu suka Dora bisa kai
“Dad dan Allah kayi hakuri.. Babu abinda mukayi….wannan innan karya take….”
“Quite.. Inna ke karya?…” Inji dad, yazid ko nude eyes baiyiba balle ya daga kai har yace kala,
“You can go..tunda baku da wacce kukeso….sai inna ta nema maku mata….” Inji dad, da sauri shahid yace
“Ina da wacce nake so….” Wani irin disgusting look Hajiya karama ta watsa Mashi,
“Wai da gaske kake ne?…” Ta tambayi dad,
“Do I look like am joking?…” Ya amsa mata atakaice
“Haba alhaji…pls let’s do some investigation…. It might not be true…” Inji Hajiya karama, Hajiya babba kam confusion bai barta tayi magana ba, ita ba aure ne damuwanta ba, kawai matar banza da inna ta ambata, daga kai tayi ta kalli yazid dake zaune wuri daya ko daga kai baiyi balle motsi, she feels for him har cikin ranta,
“Yauwa dan albarka…wacece kakeso?…” Inji inna ta tambayi shahid, bai amsa ba ya watsa mata harara
“Ba da kai akeba?…” Inji dad, da sauri shahid yace
“Asabe….” Ya fada yana tunanin his feelings towards her, kallon shi Sharif yayi
“Wacece ASABE?….” Dad ya tambayeshi,
“Mai aikin small mom….” Yafada kanshi kasa at that moment sai yaji ko yanzu aka daura aure its OK, wani irin tsoki small mom taja
Good….kai kuma fa?…” Dad ya tambayi sharif,
“Ai dad ni wayanda nakeso suna da yawa…” Ya fada yana turo baki,
“Made up your mind….” Inji dad, hajia babba mikewa tayi itama Hajiya karama tabi bayanta inna tabisu da harara.
“To mutum biyu nakeso….” Ya amsa wa dad,
“Zan aura maka daya kai kuma in kana da hali ka auri daya da kanka….” Inji dad
“Ai dad ban iya auran daya in bar daya…sai dai kayiwa shahid kadai in na fara aiki in hada su biyu in aura….” Ya fada babu kunya,, yazid baisan sanda murmushi ya bayyana kan face dinshi ba
“Wallahi dad karya yake….in baa yi Mashi yanzu nima kar ayi min….” Inji shahid, hararanshi sharif yayi
“Ai kai kana da wacce kakeso….kawai kayi ni nayi nan gaba ….” Shahid zai magana dad ya daka masu tsawa don ya lura abin zai zama wasa inna kuma tagumi tayi ta cika tayi fam.
“You are all dismissed.. Kuje Ku fara shiri…your wedding is in two weeks time….” Dad ya fada atakaice, da sauri suka mike
“Ku tsaya dan waje Ku maidani dan ubanku…” Inji inna, basu CE komai ba suka fice, inna mikewa tayi tabi bayan su shahid, ahankali shima yazid ya mike ya koma part din shi.
Inna ba karamin jijjiga tasha a motansu shahid on their way back ba, sai tsine masu take amma basu juyawa balle su tanka mata, har bump suke tsallakawa da gudu.
_Two months later_
Atakaice cikin wata biyu saida yazid ya je jos sau uku duk don neman dija amma all to no avail, duk zuwan dayake bai fadawa mufida the exact place da zashi sai dai yace office things, amma duk zuwan zan in har ya dawo sai yasha drip sabida rashin cin abinci.
Abu kaman wasa anata preparation din auren sharif da shahid, babu irin magiyan da su Mom basuyi ba amma babu abinda dad ke cewa sai ban barin yaran nan sukani cikin hallaka so better in fita hakkinsu.
Su kam yanzu basu damuwa don sun San dadin mace so suna tunanin they don’t have to screw and be afraid anymore, they are free to do what so ever da matansu, kuma sun San money won’t be the matsala cos dad yayi masu starting elaborate business kowa da nashi, wani lokacin sai sharif ya rafka uban tagumi da shahid ya tambayeshi matsalan sai yace
“Yanzu @ 25 zamu samu yara kenan?…” Sai shahid yace
“Haven’t you had of family planning?…”
“Amma ance it’s dangerous…. I love asiya( ASABE)….”
“Then get ready tobe a dad…nidai am not ready… Abinda nakeso is non stop sex…har inji na bar shaawa….” Inji shahid dake mika.
“Hmmm…”
“Ni one thing is that zan kara mata ko zuwa next year ne…” Shahid Yafada not planning at all.
Ita kam ASABE tunda sharif yace ita zai aura dad yasa aka maidata gidansu without reason, gidansu fada suka dinga mata kan ta watsar da damanta tunda tayi laifi an maidota, duk explanations da take masu kan batayi komai ba is not accepted by her guidance har sai bayan sati daya da dad da wasu friends dinsu sukaje Neman auren asabe ga shahid. Da gudu suka amince amma ita da kanta bataso.
Su Mom basuki zabin shahid ba don sun San da talaka da maikudi are all from Allah, and what will be will always be nor matter the obstacles. Lefensu irin daya akayi duk expensive and elegant kaya aka zuba. Tunda ake maganar wedding din yazid bai taba magana ko sau one ba, shidai nashi ido don according to him his problems are enough for him.
Abangaren dija kam taga rayuwa cos tayi spending two whole months on the street of jos, yanzu her pregnancy is 7 months, in ka San dija last three months to yanzu bazakayi identifying dinta ba don tayi baki tayi dirty kafanta yayi developing cracks she looks so tired and pale, yanzu ko hijjab bata yawo dashi kanta kaman na mad person, she looks older than her age, people around sun Riga sun San she’s homeless hakan yasa wasu ke dan bata abinci kyauta, tayi kukan rashin kowa har ta hakura ta barwa Allah komai. Amma one thing shine babu Wanda ya kara molesting dinta don kafin a farga da she’s aloner har cikinta ya fito. At time in Tana zaune gefe daya kafin ta kwanta sai ta rungume cikinta da kanta don yanzu tasan da akwai da cikin cikinta, the moment tayi hugging cikin sai taji all loneliness is gone, wani lokacin sai ta dinga yiwa cikinta magana in short kaman wata insane person ta koma.
Sweetheart kar wacce tayi min kuka cos of dija, remember its just a fiction nothing real.????????♀
Once again thanks for the prayers.
[6/22, 5:51 PM] ᴬᴮᵁᴮᴬᴷᴬᴿ ˢᴬᴸᴱᴴ: ❤????????????????????
NA CUCE TA
????????❤????????????
®Zuwairat (ummumaryam)
2⃣7⃣
Yau anyi ruwa sosai a jos hakan yasa garin yafi da sanyi, dija da rakube gefe daya a inda take kwanciya wato inda masu ganin doc ke zama, ji tayi sanyin yayi yawa, ga jikinta nayi mata itching don har ta mance rabon da tayi wanka, she can smell her body, amma hakan bai hanata jin sanyin ba, bodyguard dintane ya motsa don tana ganin cikinta amatsayin abinda ke tsaronta don duk yanda take da jin tsoro data tuna da akwai wani cikin jikinta sai ta rage jin tsoro, duk yanda take cikin damuwa data tuna abin cikinta sai ta saki murmushi, kawai sai ta zauna tana picturing face din abin dake cikinta,