NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“No…I will find my way back….” Amsa mashi
“Hmmm you are just unbelievable…. To bari driver ya kaika tunda ba garin kasani ba sosai…”
“OK.. ” yazid ya amsa mashi amma ba don ya so ba
Sultan fita yayi ya fadawa mom dinshi yanda sukayi da yazid, Sam bataji dadi ba amma daya fada mata nan gidan zai kwana sai ta saki ranta. Wurin driver yaje ya sanar dashi ya shirya zai fita da abokinshi.
Part din shi ya koma ya tarda yazid daya rafka tagumj, nan ya fada mashi motar is ready da sauri ya mike kaman wanda ke zaune kan allura. Bayanshi sultan yabi da kallo yana mamakin how boring yazid have become. Yazid na fita ya tarda driver dake zaune cikin motan yana jiranshi da sauri ya jefa kanshi gaban motan yanda zai samu view din gari da kyau,
“Ka kaini supermarket…” Ya fadawa driver don sayawa su ammi foodstuffs kaman yanda ya saba saye duk sanda zaije kauyensu. Daya daga cikin supermarket driver ya kaishi. Fita yayi ya shiga yana kalle2. Bayan kaman minti ashirin aka biyoshi da kayan abinci kala2. Daga nan suka kama hanyan kauyensu ammi.
Ita kuma dija data tashi yau taji duk jikinta babu dadi, haka nan take samun weird feelings, kawai cewa cikinta tayi batajin dadi, ta fita tana yawonta amma she walking tana bude legs sabida yanda batajin dadin tafiyan. She feels so uncomfortable. Inda take cin abinci Safiya taje ta gaida matar
“Dija an tashi?…” Matar ta tambayeta,
“Eh….” Ta fada tana zama dan nesa daita don tana ganin the look on people’s face duk sanda ta zauna kusa dasu hakan yasa take zama dan nesa dasu. Tafi minti goma zaune bata ce kala ba, juyowa mai kosan tayi
“Yau dija baki sayen kosai ne?… Ko sai ta kare?….” Matar ta tambayeta,
“Zan saya….” Ta amsa mata cikin sanyin murya, shuru ya an biyo baya sannan tace
“Dan Allah….inyi wanka…..gidanki?….” Ta tambayi matar muryan ta na rawa,
“Eh…babu matsala…amma ki jira in gama sai muje tare tunda da nisa kadan…” Matar ta amsa mata, wani irin dadi taji don tunda aka gano she’s on the street bata kara samun wurin wanka ba, da tana wasta ruwa cikin bathroom din hospital amma yanzu angano she’s not a patient aka hanata wanka wurin. Yanzu ta manta rabonda ta sakawa jikinta ruwa. Kosai ta saya na hamsin ta zauna nan ta ci tana jiran matar ta gama su tafi.
Sai wajen 10:30 matar ta gama ta tattara kayanta dija tabi bayan ta suka tafi gidanta
Suna isa ta nuna mata kewayenta
“Bissimillah….” Matar ta fada mata,
“To…na…gode…” Dija ta fada ta nufi tiny toilet din, tana shiga taga empty bucket, daukowa tayi,
“Ina…ruwa…da sabulu?…” Ta tambayi matar da ke kaikaye gidanta saboda yanda yara suka hargitsa mata gida.
“Ga ruwa cikin wannan drum…” Ta fada tana nuna mata drum dake tsaye
“Sannan da akwai sabulu bakin window…” Ta nuna mata inda soap yake, jiki na rawa ta debo ruwa, bata diba da yawa ba ta dauka ta kai toilet sannan ta dawo ta dauki sabulun.
Tana rufe kofa ta fara rage maranta sannan ta cire kayan jikinta, tana yi tana dan cije labe ko ina ke mata zafi oho, tana gama cirewa ta ratayesu, tsayawa tana shafa cikin ta,
“Yau zamuyi wanka….” Ta fada cikin whisper, hannunta biyu rike da tummy dinta ta jingina da bango, sai tayi saurin dagowa tare da Dan sakin kara, hannu ta dan zagaya bayanta tana tabo inda keyi mata zafi, still inda ammi ta doketa da itacene, tana tabawa taji kaman wajen na ruwa. Kurawa cikinta ido tayi kaman baa gobe, tana shafawa tana murmushi,
“Ko ta ina zaka fito?….” Ta tambayi cikin, ahankali ta duka ta fara watsawa jikinta ruwa sannan ta dauki soap da soso dake rataye ta fara wanke jikinta kaman wacce bata taba wanka ba, the more tana wanke jikinta the more tana jin relief especially her private part, wani irin sakayau taji, bag dinta dake gefe daya ta bude ta dauki wata riga amma ba neat one ba, saka kayan tayi ta maida wanda ta cire sannan ta fito. Adua take Allah yasa matar tace ta zauna ko da na minti ashirin ne,
“Na…gama….” Ta fadawa matar, juyowa matar tayi da murmushi fuskanta
“To dija….” Ta amsa mata
“Nagode….” Dija ta fada mata ahankali,
“Babu damuwa….” Ta amsa mata. Ahankali dija ta juya ta bar gidan.
Wankan datayi yasa taji kaman ta samu wuri ta kwanta, still tana jin yunwa cos kosan bai isheta ba, tana tafiya cikinta na crumbling,
“Yi hakuri….kudin mu ya kusa karewa….dole muyi maleji….” Ta fadawa cikinta tana tafiya.
Wani waje Mara yawan mutane ta samu ta zauna nan kasa tare da mike legs dinta ta harde hands dinta kan cikinta ta zauna tana kallon masu wucewa.
A kano kam ba karamin shagali ake ba, family house dinsu yazid ya cika tatul da mutane. Da mufida tazo ranar Friday tambayan yazid hajuya karama tayi ta sanar da ita zai zo yau asabar, mom dinshi kam haushi da takaici ya cikata da bata ga yazid ba, amma data tambayi Hajiya karama ko tayi waya da yazid sai ta shaida mata mufida tace zai zo yau. Hakan yasa ta dan kwantar da hankalinta.
Yau tun ten suke saka ido don ganin yazid amma babu shi, number shi mufida ta kira taji switch off. Mom dinshi fada ta dinga yi dataga har karfe 1 babu yazid kuma karfe biyu ake daurin auren. Itama kira tayi taji kashe
“Wannan yaron na naiman raina ni ko?… Zai ci ubanshi ne…” Inji mom dinshi dake tsaye kusa da Hajiya karama cikin wata karamar daki wanda babu kowa,
“It’s not late…kilan ya iso kafin daurin auren…”
“I doubt that… Gashi wayanshi bai zuwa?… Wallahi in bai zo ba to he better remain in abuja… Don ranshi zaiyi mugun baci in har ya taka Gidan nan….”
Inji Hajiya babba dake huci
“Kiyi hakuri anty..kinsan yazid ya chanza…nidai Allah yasa yaga dija ko hankalin kowa ya kwanta….” Inji hajia karama in a calming tune. Hajiya babba bata kara cewa komai ba ta fice daga wurin, Hajiya karama daukan wayanta tayi ta sake trying number yazid amma shuru.
Yazid dai nan zuwa gidansu ammi driver ya fito ya fara shiga da kayan da yazid ya sayo. Ammi ta koma rai da kashi don babu sauran flesh jikinta, duk wanda ya ganta sai yayi tunanin bazata kai hour daya da rai ba, yazid yayi sallama ya shiga bayan an gama shiga da kayan, an gidan ya fara gaidawa suna amsa mashi, da suna fushi dashi kan abinda yayiwa jikansu amma yanzu sun gane haka Allah ya kaddara, ji yayi binto nacewa
“Har yanzu bamu ga adda ba….” Ta fada mashi don tasan saboda ita yake zuwa. Nan take yazid yaji legs dinshi sunyi sanyi, amma daman he wasn’t expecting su ganta. Inda ammi ke kwance ya nufa, gabanta ya durkusa ya gaidata, ko bude ido batayi ba balle ta amsa mashi, sai nishi kawai take
“Dan Allah ki bari in kaiki asabiti….dan Allah ki rufamin asiri kar hakkinku yayi min yawa….” Inji yazid dake magana kaman zaiyi kuka, still ammi bata ce kala ba, yafi minti goma nan durkushe amma ko eyes bata bude ba balle ta tanka mashi, ahankali ya mike ya je wajen tsohon gidan. Request ya nema kan a fadawa ammi ko zata yarda ya kai ta hospital, tsohon mikewa yayi ya tarda ammi inda take kwance ya dinga sauke mata zafafan words wanda yasa ammi fashewa da kuka
“Zanje….” Naji ta fadawa tsohon,
“Maza tashi ki shirya…in banda abinki ai wannan yaron nada tsoron Allah…ji yanda yake wahalan zuwa nan….INA tabbatar maki in wasu ne ko tunawa basuyi….maza tashi …” Ya daka mata tsawa, ahankali ta mike jikinta sai rawa kawai yake Kaman 100 years old woman. Da taimakon binto ta shirya, yazid na waje yana jiran fitowanta, few minutes later ta fito binto rike da hannunta, sai wata mata dake biye dasu. Da sauri yazid ya bude mata bayan motan ta shiga da binto sai yaruwan ammi.