NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shima yazid shiga yayi,
“Ka kaimu asiti….” Yazid ya fada ma driver,
“Wanne?…” Driver ya tambayi yazid,
“Nima ban sani ba….amma ka kaimu mai kyau…” Yazid ya amsa mashi, tada motan driver yayi yana cewa
“Ko in kaiku general hospital?…” Da sauri yazid yace
“Aa…nasan da akwai cikowa…”
“Zanyi masu bayani tunda momin abokinka babbace a asibitin… Na tabbatar basu bata maka lokaci…” Inji driver,
“In ka tabbatar da hakan mujeto…” Ya fada ba don yaso ba don shi anything general ba so yake ba.
Around three suka kama hanyan cikin gari, ammi ta jingina idanuwanta lumshe,binto sai kalle2 kawai take, adaidai lokacin da suka kusa isa gate da zai sadasu da hospital ita kuma dija ta taho zata cin abinci rana don tun wannan kosai bata kara cin komai ba duk don tayi manejin yan kudinta da baifi 1k ba, binto ta fara ganinta daga nesa amma bata yarda cewa itace ba, shima yazid ya ganta kuma kallo daya yayi mata ya kauda kanshi gefe, da sauri ya kara maida kanshi yana kallon ta while motan na shiga hospital, da sauri binto tace
“Laaaaa….wannan kaman.. Adda dija….” Tafada da sauri, da sauri ammi ta bude ido, yazid ji yayi gabanshi yayi mugun faduwa,
“Stop the car!!!!!…..” Ya fada cikin muryan da shi kanshi baisan yana dashi ba,
“Adda!!!!….” Binto ta kwalawa dija dake wucewa gefensu, dija daga kai tayi sukayi ido hudu da binto, tsayawa tayi tana kallon binto then ammi data fashe da kuka ganin yanda dijarta ta koma kaman almajira ga kuma ciki, yazid dai mutuwar zaune yayi yana kallon dija at the same time hawaye na bin juna, dija na tabbatar amminta da binto ta gani ta saki bag dinta ta fara bin motan nake Neman wajen parking da gudu tana kira ammi on top of her voice, motan na tsayawa ta karasa wajen tarufe Marfin motan ta bude, nan take ta fada jikin ammi tana kuka, babu abinda take cewa sai
“Ammi….ammi…kiyi hakuri….ban…karawa….ammi waje nake…kwana…..ammi kalli cikina….ammi Dane cikin cikina…ammi yana motsi..ammi…ki maidani gida….ammi kar ki barni nan…ammi ban kara yi maki gardama….ammi dan Allah ki maidani gida in barjin sanyi daddare…..” Yanda take magana sai ka rantse Mara hankali ce, babu abinda yazid yake sai kuka, yana hawaye hannunshi biyu kan bakinshi. Dija kara rike ammi tayi tana kuka tana magana, binto kuka likewise sis din ammi, shima driver dake zaune kusa da yazid juyawa yayi yana kallon yar yarinyan dake irin wannan maganar shima saida hawaye ya tarar mashi, ammi tallabo face dinta tayi
“Dijata….” Tafada cikin kuka, dija na kuka jikinta na rawa ta kama hannun ammi
“Ammi ki taba kiji….yana motsi….” Ta fada cikin matsanacin kuka, tun yazid na hawaye kawai sai kukan taci karfinshi, jin kukan mutum yasa dija daka kai ta dan leka gaba, nan suka hada ido da red and tearful eyes din yazid, da sauri ta mike tana
“Ammi shine….ammi wallahi shine….” Tana maganar tana ja da baya, ganin mota ya taho ita kuna na ja da baya2 yasa yazid saurin fita daga cikin motan, aikam tana ganin ya fito kuma su ammi basu hanashiba yasa ta juya da gudu wanda yayi daidai da zuwan motan. Before driver Motan ya taka break it was late, wani irin karo dija tayi da motan yayi sama daita.
Hannu yazid ya dafa ga kai tare da saki wani irin razanannen ihu.
[6/22, 5:52 PM] ᴬᴮᵁᴮᴬᴷᴬᴿ ˢᴬᴸᴱᴴ: ????????????????????❤
NA CUCE TA
????????????????❤????
®Zuwairat (ummumaryam)
2⃣9⃣
_Follow me on:_
*Wattpad @ummumaryam29*
*Email:Zuwairat.nuhu@gmail.com*
*IG: zuwairatummumaryam*
*Website:Www.ummumaryam.com*
*And also join my new Facebook group: Zuwairat ummumaryam and Zuwairat ummumaryam page.*
*Snapchat: ummumaryan29*
Ammin data dade batayi tafiyan kirkiba sai gata ta fito daga cikin mota da gudu, haka zalika su binto da driver dake cikin mota, yazid bai San sanda ya karasa inda dija ke wance ba, shima doc daya bugeta fitowa yayi cikin tashin hankali,
“Khadija!!!…..” Yazid ya dinga kiranta yana rike daita nan kasa, hannu ammi ta dora bisa kai tana kuka,
“Khadija dan…Allah… Wake up….” Yafada yana girgiza ta da karfi amma ko motsi batayi, mutane taruwa sukayi suna kallon su, doc daya bugeta ya rike yazid don ya samu daman duba dija amma wani naushi yazid ya kai Mashi Wanda ya tsorata shi yayi saurin ja da baya,
“Khadija… Pls….don’t do this to me….I will be miserable for the rest of my life….” Yafada yana dorata kan kafanshi at the same time yana kuka kaman ranshi zai fita, duk mutanen dake tsaye babu Wanda yayi kokarin taimakawa, doc daya bugeta nason taimakawa amma yana tsoro kar yazid ya kara naushinshi, yazid tsaya kallon yanda cikinta ke motsi yayi ya daga kai yana kallon faces din mutane yana cewa
“Dan Allah Ku taimaka min….pls help…..” Da sauri doc din nan ya zo ya rike wrist dinta for a while sannan yace
“Ka dauketa muje….” Inji doc cikin sauri, da sauri yazid ya mike ya dauketa, ammi da dasu binto babu abinda suke sai kuka, bin bayan yazid sukayi shi kuma yazid na biye da doc, sai sauri yake amma ko gabanshi bai kallo sai dija, yana tunanin yanda ta koma kaman baitaba
“Me zanyi maki in biyaki for all this pain….” Yafada yan kuka, kallon yanda cikinta ke ta motsi kawai yake, bai ankaraba yaji zaa amsheta daga hannunshi, sai lokacin yaga nurses da gadon da ake tura mutum, baisan ya akayi sukazo ba, babu musu ya dorata kan gadon aka fara turata amma yana rike da hannunta, goshinta daya kumbura ya kalla.
Motsin dan cikinta looks so visible da ko daga nesa kana Iya hangen yanda cikin ke motsi kaman zai fito
Doc kallon ta yayi for ya moment sannan yace
“Take her to the labour room…” Hankalin yazid ne ka Kara tashi, baisan lokacin dayace
“Its just seven months….”, doc dai baice komai ba amma deep down yana tunanin wanne relationship ke tsakaninshi da ita don they look so different, babu alaman dangantaka tsakaninsu don duk Wanda yagansu yasan they are from two different part of class and level amma yanda yake nuna damuwanshi is questionable to him
Inda dija ta kwana for some days aka shiga daita only she was unconscious, tsaye yazid yayi aka shiga ciki daita, ammi dai kuka yaki tsayawa, yazid goge face dinshi yayi ya fiddo wayanshi dake cikin aljihunshi Wanda ya kashe tun 12am na jiya kuma bai kara kunnawa ba saboda kar mufida ta tisashi gaba. Kunnata yayi sannan yayi dailing number Salem, after like ringing biyu zuwa uku yayi picking yana cewa
“Wai me yayi zafi da zaayi bikin lil brothers dinka amma baka zo ba?…. Gaskiya baka kyauta ba… Dazun saida dad dinku yayi min magana bayan daurin auren… Karya nayi Mashi nace kuna port….” Duk maganar da yake yana fada cikin annoyance ne amma gurin yazid shine ya kai aya sannan ya fada Mashi abinda yake son cewa, yana jin shuru yafara cewa
“Na ganta!…” Ya fada in one word,
“Wa?…”
“Khadija…” Ya amsa Mashi cikin sanyin murya , dasauri Salem ya saki ajiyan zuciya tare dacewa
“Ina?…”
“A jos….”
“Da akwai cikin?…” Ya tambayeshi full of excitement,
“Yes….amma she have an accident while running away from me….” Yazid ya fada muryanshi na rawa,
“Subhanallah!!….how is she?…”
“Yanzu anshiga daita ciki….salem… Na cuceta….you need to see her….ta koma kaman baitaba….I don’t know what made me do it….” Yafada yana kokarin sake kuka saboda yanda heart dinshi keyi Mashi zafi,