NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Rabo…kaddara…destiny….” Salem ya amsa Mashi in a calmly manner

“Yanzu me doc yace?… Hope it’s not serious?…”

“Bata motsi….amma naga cikin na motsi…ka tayani adua…I don’t want to loose anyone of them…. Inason in biya Khadija for the pain and agony I caused her….kuma inason abinda zata Haifa….nasan ana iya stigmatizing dan ko yan…amma ba laifin shi ko ita bane….it’s all my fault… The child deserve to live….” Yafada in a regretting manner at the same time hawaye na gagarowa daga idonshi,

“Insha Allah the child will live…babu abinda zai samu both of them…. Ka kusa zama dad ko…” Salem ya karasa maganar da zolaya, yazid zai bude baki yayi magana yaji call ya shiga, dubawa yyi yaga small mom,

“Bari zan sake kira…mom is calling…”

“OK..pls give me updates about her…” Inji Salem

“OK…” Kawai ya fada yayi picking call dinta, itama balbaleshi ta farayi kan meyasa baizo daurin auren su Sharif ba, saida ta kai aya sannan ya fada mata ya gan dija

“Kai alhamdulillah….” Ta fada with excitement kaman baita ke fada few seconds ago ba,   dan murmushi yayi sannan ya fada mata halin da ake ciki,

“Inna lillahi waina ilaihi rajuun!….hope it’s not bad?…” Fada mata komai yayi

“OK…ka kula daita…zan yiwa anty magana  don she’s so angry…” Ta fada Mashi,

“OK nagode….” Ya fada yana juyawa don gani Wanda ke tahowa, ganin doctor ne yasa yayi saurin katse wayan tare da nufanshi

“Doctor… Ta tashi?…” Ya tambayeshi,

“Yes…pls waye mijinta?…” Shine tambayan da doctor yayiwa yazid Wanda har su ammi sunji Sadda kai ammi da family dinta sukayi while yazid ya kasa replying question din doc,

“Pls ya jikinta..hope  its not bad?…..” Ya sake tambayanshi,,

“Not that bad…few injuries ne….” Ya amsa Mashi sannan ya sake cewa

“Waye mijinta?…”

“Ni…..” Ya amsa Mashi kanshi kasa, kallon up and down doc yyi mashi, yafi minti biyu yana kallon shi inda shi kuma yazid bai yarda suka hada ido na,sai da ya gama kallon  sannan yace

“Follow me…” Ya fada Mashi atakaice tare da juyawa, jiki ba kwari yazid ya bi bayanshi,  wani office dake kusa da labour room doc ya shiga inda wata babbar mace ke zaune, yazid na daf da shiga yaji kaman dija na cewa

“Wayyo ammi cikina…wayyo mutuwa zanyi….”  Da sauri yazid ya shiga cikin office din yana cewa

“Kaman kukanta nakeji….pls what’s happening?…” Ya fada cikin tashin hankali,

“Sit….” Matar dake cikin office ta fada Mashi tare da nuna Mashi seat dake opposite to Wanda ya banke dija.

“As a result of event daya faru..ta shiga labor….” Aikam sai ya dafa kai

“Labor doc…its seven months… Anya babyn zai rayu?….” Ya fada kaman zaiyi kuka, kallon juna sukayi don basu yarda He’s responsible for the pregnancy ba…kawai suna ganin He’s lying,

“Ai seven months na da…baka taba jin an haifi bakwaini ba?… Kawai saidai maganar incidents daya faru…amma da pregnancy is OK…” Inji matar, yazid shuru yayi ya rasa abun cewa,

“So zaa sayo kayan haihuwa…although bamu amsan irin wannan haihuwan but due to the circumstances we will help….” Matar ta sake fada Mashi, yazid dake zufa dag red eyes dinshi yayi ya kallesu

“Pls…Ku cire abinda ke cikinta….I don’t think tana da strength da zata haihu….” Ya fada voice dinshi na cracking, kai matar ta girgiza,

“Its a government hospital.. We don’t work that way…” Ta fada Mashi,

“Then zan kaita private hospital…” Ya fada yana mikewa, da sauri doc yace

“Ina da private hospital… In that case mu kaita chan…” Ya fada yana mikewa, daman already yazid tsaye yake, fita yayi ya sanar da ammi yanda sukace, fadawa doc din yayi suyi gaba yana biye dasu.

“Who will pay the bills…” Doc ya tambayeshi,

“Money is not the problem…” Inji yazid, cikin mota gidan su Salem ya shiga ya zauna baya, gudun kar dija ta kara  ganinshi ta rude, few minutes later aka fito daita zaune kan wheelchair, sai kuka taka tana cikinta, tana ganin ammi ta mika mata hannu, da sauri ammi ta mike taje inda ake turota ta rike mata hannu, duk ta manta da aladansu, babu abinda ke cikin ranta sai tausayin dija,

“Ammi cikina….cikina…marata…” Kawai dija ta take fadi, yazid na kallon ta daga inda yake zaune cikin mota, cikin mota doc aka sakata su ammi suka shiga suka bar wurin, yazid ya umarci driver yabi bayansu.

Kawai adua kawai yake kar wani abu ya sami dija he can bear loosing the child amma banda dija. Shi gani yake the child won’t make it amma yana da hope cewa he will have any number of kids he want in the future

“Pls make it….” Ya fada under his breath, kiran mufidane ya shigo wayan, da sauri yayi picking yana cewa

“Baby am so sorry I lied… Kiyi hakuri….pls don’t be offended…” Ya fada mata in a whisper don kwantar mata da hankali,

“What can I say…kawai kullum sai….” Bata idaba  ya katseta dacewa

“Baby ki yafemin….pls don’t say anything OK…” Ya fada mata cikin sanyin muryan dayasan she can’t resist,

“OK…yanzu kana ina?….” Ta tambayeshi, shuru yayi for a while sannan ya fada mata exactly abinda ke faruwa, cikin karfi hali tace

“To Allah ya bada saa….” Zai bude baki yayi magana yaji ta katse wayan. Murmushi kawai yayi.

Achan family house duk cikan dayayi sabida yan taro bai hana Hajiya karama kebewa da Hajiya babba ba, bayan  sun Shiga inda babu kowa, sai Hajiya karama ta fadawa Hajiya babba exactly abinda yazid ya fada mata, shuru tayi hawaye na taruwa idonta,

“Allah yasa kar dan yazo da rai….in yaso sai ya aureta batare da ansan exact abinda ya faru tsakaninsu ba….” Inji Hajiya babba, idanuwa Hajiya karama ta zaro

“Aa wallahi…Allah yasa yazo da rai…yo haka Allah ya kaddara….besides ni fa ban ga wani aibun abinda ya faru ba…ai duk Muslim na kwarai yasan kaddara…yazid dai ba dan iska bane balle ashe daman ya saba….kuma duk Wanda yaga yanda ya damu yasan ba halinshi bane…don haka ni dai wallahi yazo da rai koni da raineshi….” Ta fada in I don’t care manner kuma she’s serious,

“Wai ke ko kadan baki tunanin abinda mutane zasu ce?….” Inji Hajiya babba, shoulder ta daga

“Who cares….kowa na da nashi cockroach in thea  cupboard…so kowa yaji da abinda ya dameshi….” Ta fada sannan ta dafa shoulder Hajiya babba da Duk ta susuce

“Anty ki kwantar da hankalinki…. In mace CE ba sai taje waje aure ba balle ayi  mata surutu…cikin dangi zaayi mata miji…in kuma na mijine babu case don for as long as he’s rich no body cares….” Yanda take magana yasa Hajiya babba dariya, dan hararanta tayi

“Wato ke har kin gama plan din komai….” Ta fada in a funny way,

“Yo me yafi raina…” Ta fada tana dariya.

Bayan kaman minti ashirin suka isa hospital, hospital din is not that big but it is unique and beautiful, da sauri nurses din wurin suka amsheta deyeka doc ya sanar dasu, fita yayi daga cikin motan yq nufi motan da yazid ke ciki, shima yazid fitowa yayi ya nufoshi,

“Zaa bada deposite of 80k…in an gama kafin a sallameta zaa bada balance of 70k,…150k muke cs anan…” Inji doc, yana kiran 80k yazid ya fiddo wayanshi, few seconds later ya daga kai yana yace

“Pls I don’t have cash on me…kuna amsan  transfer?…”

“Yes…no problem…”

“OK…pls account number…” Inji yazid, nan take ya karanto Mashi ya saka

“Bank name pls…” Inji yazid, fada Mashi yayi, ko minti biyu baiyi ba yayi receiving alert na 170K, kallon shi doc yayi zaiyi magana yazid ya katseshi dacewa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button