NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“20k din na wanda nakeson ka duba min ne….that woman….” Ya fada yana ammi data rafka tagumi,
“OK…” Doc ya fada ya juya da sauri. Ciki ya shiga, kafin ya shiga har an shanzawa dija dake ihu kaya, nan take aka hau aiki.
A waje kam ammi mikewa tayi don tasan bai kamata ace tana zaune nan dija ta haihu ba, magana tayi da yar uwarta kan su tsaya da dija. Ahankali ta zo ta wuce inda yazid ke tsaye,
“Ina zaki kuma?…” Ya bi bayanya yana tambayan ta,
“Gida….” Ta amsa Mashi atakaice,
“Dan Allah ki tsaya a dubaki…” Ya fada mata cikin sanyin murya, kai kawai ta girgiza sannan tace
“Aa….”
“To bari ya maidaki…” Ya fada yana juyawa, fadawa driver yayi a kaita inda ya dauko ta.
Driver zuwa yayi da mota inda take tsaye ta bude ta shiga. Yazid kallon agogon hannunshi yayi yaga kusan 5:30, sai lokacin ya tuna baiyi sallan asr ba. Dan shiga cikin yayi yaga har lokacin doc bai fito ba, fita ya karayi yana tafiya yana tunani, har yaje bakin titi bai Sani ba saida wani mai mashin ya kusa bugeshi sannan ya dawo sense dinshi.
Bayan thirty minutes ya dawo direct ciki ya shiga ya nufi reception, nan wacce ke nan ta nuna Mashi office din doc, jikinshi na rawa ya shiga ciki, kallon face din doc yayi ko zai iya understanding halin da ake ciki, murmushi ya sakarwa yazid tare dacewa
“Congratulations… It’s a boy…”
????????????????❤????
Sweethearts kuyi hakuri am soooooo busy ne shiyasa kuke jina shuru. Sorry for waiting too long and pls don’t forget to vote and comments.
[6/22, 5:53 PM] ᴬᴮᵁᴮᴬᴷᴬᴿ ˢᴬᴸᴱᴴ: ????????????????????❤
NA CUCE TA
????????????????❤????
®Zuwairat (ummumpls am)
3⃣0⃣
_Follow me on:_
*Wattpad @ummumaryam29*
*Email:Zuwairat.nuhu@gmail.com*
*IG: zuwairatummumaryam*
*Website:Www.ummumaryam.com*
*And also join my new Facebook group: Zuwairat ummumaryam and Zuwairat ummumaryam page.*
*Snapchat: ummumaryan29*
Baki yazid ya bude yana sucking maganar doc into his brain, ganin shuru yayi yawa yasa doc cewa
“Yes…its a boy…” Yafada yana kallon how still yazid is, ahankali yazid ya daga kai ya kalli doc
“Babyn lafiya lau?…I mean…lafiya dan yake?…” Yafada sounding out of word,
“Yes….he’s alright…”
“Khadija fa?..” Ya tambayeshi still not believing his ears,
“Itama tana lafiya….sai dai…” Da sauri yazid ya zaro eyes dayaji saidai
“I want to ask you…pls ka fadamin gaskiya…” Inji doc,
“Ina son sanin relationship dake tsakaninka da wannan yarinyan…” Doc ya tambayeshi
“She’s… My…wife….pls can I see the boy now?…” Ya fada don kar doc ya sake yi Mashi wannan tambayan,
“Eh ana cleaning dinshi …babu kayan yaro amma daman muna ajiye wasu in case if emergency…”
“,OK….” Yazid ya fada yana mikewa jikinshi har rawa yake.
“Pls sit….” Doc ya kara umartanshi, da sauri ya koma ya zauna kaman wani Mara wayau
“Pls wane dalili yasa ka bar pregnant gal haka?…. Indai kai mijinta ne as you proclaim… Don ni har yanzu bani da assurance da gaske kake….” Inji doc, yazid shuru yayi yana tunanin abinda zai fadawa doc don ko kadan bai iya fada Mashi gaskiyar alamarin,
“Guduwa tayi daga gida as a result of aljannu da suka shafeta….yau na ganta….” Yayi Mashi karya which is written all over his face don bai iya karya ba,
“OK..amma she will need a medical care…”
“OK…pls can she fly out of the country?…” Ya tambayeshi cikin ranshi yana aduan yace yes
“No bazata iya ba yanzu… Amma don’t worry…. Wannan hospital is among the best in town…zamu bata dukkan kulawan da ya kamata….”
“OK…do…pls….can I see the baby now?…” Ya sake tambayanshi, mikewa doc yayi shima yazid ya mike, har doc ya kusa shiga dakin da jaririn yake sai yazid yace
“Pls tana nan dakin?…” Ya tambayeshi gabanshi na faduwa,
“No…tana postnatal… ” doctor ya fada yana bude kofan dakin. Nurses biyu ne zaune sai gadajen newborn kaman ten, babu newborn sai na Yazid, doc na gaba har wajen gadon yaron, da sauri yazid ya tsaya gaban gadon yana kallon yaron ko kiftawa baiyi,
“Doc. He’s tiny… Are you sure he’s alright?…” Ya tambayeshi yana taba small cheek din yaron,
“Ai bakwaini ne…kuma from all indication the mother have not been feeding well…. Amma in yana samun kulawan daya kamata…he will group in no time….” Doc ya fada Mashi
Still yazid bai gamsu da maganar doc ba, dan daga white towel dake jikinshi yayi yana karewa tiny boy din kallo,
“Pls doc a kara dubashi….he don’t look fit…banga ya motsa ba….” Ya fada yana shafa hair din yaron, cikin ranshi kam yana tunanin rabon wannan yaron ne yasa ya aikata abinda bai taba aikatawa ba
“Am assuring you…lafiyan yaron lau….kawai ka bashi few months ka gani…” Inji doc, ganin irin kallon da yazid ke wa yaron yasa shi daukan yaron
“Will you like to hold him?…” Inji doctor, ahankali yazid ya gyada Mashi kai tare da mika Mashi hannu, ahankali doc ta dora Mashi yaron dake motsi, yazid ji yayi kaman he’s dreaming, wai yanzu wannan danshi ne. Kallon tiny legs din yaron yayi with excitement.
“Yanzu me dame suke bukata?…am new to the whole system…” Inji yazid, murmushi doc yayi
“First zaka kwantar da yaron….then kayo shopping baby wears…sai kayan shayi da matarka zatasha…sai ka fadawa masu kula dasu suzo….” Inji doc dake amsan yaron daga hannun yazid don dagani bai Iya rika yaro ba,
“Pls doc zan Iya samun nurse da zai dinga kula da both of them kafin su bar hospital?…. Zan biya…”_ya fada don ko kadan baison yan kauyensu ammi suce zasu kula da dija ko new boy dinshi.
” OK…” Zan nemo maka daya cikin nurses dina…” Inji doc daya mayar da yaron kan gado,
Bayan doc ya tabbatar yaron yayi balance ya juya yazid yabi bayanshi yana waigawa yana kallon yaron, har tuntube ya kusa yi saboda yanda yake waigawa,
“Doc why ba zaa kaishi inda take ba?../”
“Because tana bacci…” Doc ya amsa Mashi, ji yayi he needs this opportunity ya ganta koda na minti biyar ne don bazaiyi gangancin shiga dakin in idonta biyu ba.
“Can I see her?…” Ya tambayi doc,
“Yes….tana wancan dakin..” Ya nuna Mashi wani right handside door da aka rubuta mother resting, wucewa doc yayi office din shi shi Kuma yazid yaje bakin kofan. Da kyar ya samu courage din bude kofan, hangota yayi kwance, an rufeta da sky blue kyalle kaman yanda akewa yan operation, hands dinta biyu kan cikinta, ahankali ya shiga dakin bayan ya maida kofan ya rufe, bakin gadon ya isa yana kallon ta from head to toe, kallon how dirty her hair and feet is kawai yake, hmmm nace don ma tayi wanka yau kenan, face dinta ya kurawa ido yana tunanin how she survived for almost two months on the street with pregnancy.
“Am sorry… Daga yau baki kara shan wahalan rayuwa….I promise you that….” Ya fada in a whisper, kallon yanda kirjinta ya kara cika yayi as a result of ciki, gira daya ya daga ya juya ya bar dakin, yana fita yaga binto da yar uwar ammi, nan ya sanardasu ta haihu na miji kasancewan doc bai CE masu komai ba. Tsalle binto ta dingayi while ita matar bata nuna wata alaman murna ba, yazid ya ga the look on her face
“Ku kwantar da hankalinku…I won’t let her face any of your stigmatizations….” Ya fada cikin ranshi yana dailing number Hajiya karama don ita kadai yake Iya fara fadawa. Bayan tayi picking ya sanar da ita, har da guda tayi saboda murna,
“Yanzu wake kula da ita?…” Shine tambayan da Hajiya karama tayi Mashi,