NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Babu…amma nayiwa doc maganan ya samo min masu kula da ita kafin a sallameta insan abunyi….” Yazid ya amsa mata,
“Wane irin masu kula alhalin ga wayanda keyi mana nursing yara?… Zan turo daya gobe….” Inji Hajiya karama,
“Ai mom kafin goben dole a kula dasu….Kuma kinsan ba lallai bane dad ya amince da hakan…Kuma banason a sani da yawa….” Tsoki Hajiya karama taja,
“Naji a kawo mai kula dasu just for to night… First thing in the morning zan turo doc fatima,…sannan don’t worry ba dole bane sai sun sani abinda ya faru…iyaka tayi aiki a biyata….” Ta amsa Mashi sharply,
“I love you mom….” Ya fadawa Hajiya karama saboda yanda take nuna damu a duk alamuranshi,
“Keep quite…” Tace Mashi, dariya yayi sannan yace
“Mom…pls banason khadija ta shayar dashi.. I possible ya sha baby formulars…”
“Why?…” Ta tambayeshi, shuru yayi for a while sannan yace
“Cos hakan zai zame mata more stress… I don’t want her to waste any more time…I want her to go to school…” Ya fada yana jinginawa da wata bushiyar umbrella dake compound din hospital din.
“Hmmm kana ganin hakan ya kamata?… Kasan breastfeeding yana saka more shakuwa tsakanin da da uwa….”
“I know mom…amma I don’t want her to go through that right now…she’s too young for all this….” Yafada idanuwanshi lumshe,
“OK if you say so….sai a fara bashi ko sma gold 1 ne kafin ayi Mashi ordering na almarai nuralac….” Hajiya karama ta fada mashi, zai bude baki yayi magana tayi saurin katseshi dacewa
“Kai kyaleni inje in bada good news….” Tana kaiwa nan ta katse wayan. Murmushi kawai yayi sannan yayi dailing number Salem, same story ya bashi, shima ba karamin dadi yaji ba, he feels so excited har da cewa
“The latest dad in the world….” Inji Salem cikin zolaya
“Hmmm ka manta he’s out of wedlock?…” Inji yazid cikin sanyin murya,
“Mudai wannan bai hanamu shashewa next week Saturday….” Inji Salem, hira suka dan taba sannan yazid ya je inda yayi sallan asar yayi na magrib,, bakin gate din hospital ya koma ya zauna yana jiran dawowan. Bayan kaman minti ashirin da zamanshi ya dawo da wasu mata guda biyu da alaman still family din dija ne, bayan ya ajiyesu shikuma ya shiga mota sukayi gaba. Gaban katuwar plaza suka tsaya da taimakon driver, dukda darene amma wurin kaman rana, bangaren baby wears suka hau bayan ya tambayi wani ya nuna masu wurin. Jugum yayi yana kallon kayan wurin ya rasa mai zai saya, kallon wasu mata dake siyayyan kaya yayi,
“Dan Allah Ku tayani zabar abubuwan da jariri zai bukata…” Ya fadawa Matan bayan yayi masu sallama sun amsa. Nan suka fara zaba Mashi kayan sawa Dana amfanin, har dasu bombom baby perfumes kala2. Gefe daya ya tsaya saida suka gama sannan ya kwace kayan da taimakon yan aikin wurin zuwa inda aka duba kayan.
Komawa yayi inda ake sayarda kayan sawa nan ya dinga kwasan gowns not minding the amount da zaiyi costing, daga nan ya je bangaren, shoes ya dauki simple but expensive slippers guda biyar sai, yana tura kayan yaje inda mayuka suke, ya rasa Wanda zai saya mata amma yasan da makari mufida ke amfani and yayi mata kyau, hakan yasa shima ya dauki makari da sabulunta ya zuba cikin trolley da yake turawa, daga wannan sai perfumes da hair shampoo don har yanzu bai manta how silky and shiny kanta yake ranar da yayi molesting dinta ba. Yana turawa ya je wajen beverages da kayan malaki, katuwar nido da Ovaltine ya dauka gida bibbiyu sannan ya dinga sayan su juice da kayan dadi kaman ba gobe, sai wajen 9pm ya gama before then sultan ya kirashi don jin why basu dawo ba har yanzu sai yayi Mashi karya da hira yakesha inda yaje amma ya kusa dawowa.
Bayan ya bada credit card dinshi aka zari kudin masu yawa sannan suka saka Mashi kayan a bayan booth suka koma hospital. Saida yaje wajen doc ya fada Mashi ya taimaka Mashi yayi jagora a kai kayan Kuma ya fada mata in ta farka dole tayi amfani da kayan, doc bai nemi jin dalilin hakan ba yasa masu gadi suka shigar da kayan har inda dija ke kwance su Kuma Matan da binto na zaune suna jiran farkawanta. Ajiye kayan akayi Matan suka bude baki suna kallon ikon rabbi.
Doc komawa yayi ya shaidawa yazid an kai kayan, sai bayan nan yazid ya kara tambayanashi kan wacce zata kula dasu, sai doc ya shaida Mashi an samu daya daga cikin nurses dinshi da zatayi wannan aikin. Dadi sosai yaji ya kara shaida Mashi kan dan Allah kar a bari a jagwalgwala yaron doc ya bashi assurance kan hakan bazai faru ba. Hannu yazid ya mika Mashi sukayi sallama sannan ya mike ya fita cikin ranshi yana cewa
“Am taking responsibilities for my actions…”
Da sauri ya Kuma dawowa daya tuna maganar shayar da danshi. Nan ya fadawa doc abund yakeso ko gardama baiyi Mashi ba y amince da yayi hakan, sai lokacin ya fita har cikin ranshi yana son kara ganin face dinta amma haka ya hakura likewise yana son ganin danshi amma shi ko kadan baison ganin yanda yake dan Karami. Haka ya hakura ya fita daga cikin hospital din feeling so relaxed, ya mance rabon da yaji irin wannan farin cikin, ji yake kaman an dauke Mashi wani katon stone dake weighing dinshi down. Jefa kanshi yayi bayan mota yana murmushi with his eyes closed. Kafin su kai gidan was around ten, wanka yayi yaci abinci sosai sannan yayi salla ya kwanta bayan sunyi brief hira da sultan.
Dija bata farka ba sai wajen 10pm lokacin matan na zaune, sai nurse da zata kula daita dake kicingide kan kujera ita kuma binto tana kwance nan kasa, lokacin doc na shirin tafiya gida. Tana bude ido taji cikinta empty da Sauri ta fara shafa cikinta don ta manta events daya faru, ganin Matan dake zaune sai ta tuna taga amminta, then…yazid….da Sauri ta widening idanuwanta data tuna taga yazid tare da amminta da binto, sai ta tuna mota ya bugeta, daga nan ta tuna ta farka in do much pain,
Then an saka ta a mota an taho daita, she remember she was screaming saboda azaba then an shiga daita wani daki da wasu mutane daga nan bata kara tuna komai ba, kara shafa cikinta tayi taji kaman bandage sannan ga zafe, idanuwa ta zaro
“Ina cikina!…” Ta fada kaman Mara hankali wanda ya maida hankalin mutanen wurin kanta, da sauri nurse din ta mike likewise yan uwan ammi duk sukayi kanta
“Ina cikina?…..” Ta fada sounding more tensed sannan tana shirin kuka, d saurin nurse din tace
“An fidda maki….kin samu namiji….” Ta yi mata dalla2
“Na…mi…ji?….” Tafada tana zaro idanuwa,
“Eh namiji….” Ta amsa mata, su kam Matan tsaye sukayi suna kallon su,
“To yana ina?….” Ta tambayeta,
” zaa kawo maki shi….” Tafada sannan ta fita daga dakin, office din doc dake tartare kayanshi ta Shiga ta sanar dashi halin da ake ciki, da saurinshi ya fita zuwa dakin.
“Ina…ammi….” Ta tambayi sisters din ammi,
“Tana gida….” Daya daga cikin su ta amsa mata, bude kofa akayi nurse da doc suka shiga,
“Da akwai inda ke maki ciwo?….” Ya tambayeta, ahankali ta girgiza kai tare dacewa
“Cikina ne kawai…ina dan?…” Ta tambayeshi, murmushi yayi
“Yanzu zaa kawo maki shi…kinji ko?…” Kai ta gyada Mashi, alama doc yayiwa nurse kan a dauko dan, nan ta fita few seconds later ta dawo rike da Dan, tana shigowa dakin dija tayi saurin mika Mata hannuwanta, Dora mata yaron tayi, saida ta kalleshi for almost two minutes sannan tace