NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ina jinki…” inji matar,
“Nace..in..babu…damuwa….zan….yi…” ta kai.karshen maganar da kyar, murmushi matar tayi tana cewa
“Da kaman bazaki ida maganar ba…kina Iya aikin ne?…” Da Sauri dija ta gyada mata kai tana cewa
“Eh..” Yanda tayi maganan yasa matar dariya tana cewa
“In iyayenki basu yarda ba fa?…” Da Sauri tace
“Babanmu ya rasu..nasan ammi zata yarda…in kin je ..kin fada mata …” Ta fada muryanta na cracking, matar kura mata ido tayi tana kallon beautiful and innocent face dinta Kuma tana tunanin wane irin dalili ne zaisa yarinya ta so zuwa gidan aiki Kuma da kanta ba wai forcing dinta akayi ba, amma tana kallon how faded her hijab and wear looks sai ta gane she will definitely needs some income Kuma Tasan ta cancanci irin gidan da ake magana.
“In Bata amince ba fa?..” ta sake tambayan ta, muryan NA rawa tace
“Nasan zata yarda…” Ta Bata assurance dukda tana ganin da kyar hakan zai yiwu don Tasan stand din ammi kan barin ta tafi wani wuri aiki amma gaskiya ta gaji da wannan wahalan tallan Kuma tayi deciding zatayi anything necessary don ammi ta amince NA wannan zancen
“Wane wuri kike?…” Ta tambayeta, nan dija ta fada mata sunan kauyensu, baki matar ta bude
“Yanzu daga Chan kuke zuwa nan cikin garin?..” Kai dija ta gyada mata
“Lallai kam..amma ina ganin da nisa Kuma aikin ba a garin katsina zaayi ta..Kano ake bukatan mai aiki…” Da Sauri dija ta katseta dacewa
“Ai ba komai… Tunda baa kasa zanje ba…” Dariya matar tayi
“To..yanzu tunda an fadamin ana bukatan mai aikin da wuri bari in kaiki garin naku sai muyi magana da amminki…” Wani irin dadi dija taji amma sai cewa tayi
“Ai ban gama saida furan ba…” Dariya matar tayi tana cewa
“Ki kirge min sauran…” da Sauri dija tayi counting sauran cikin Leda ta mika mata
“NA nawane?…” Matar ta tambayeta
” sauran na dari uku da sabain…” Dari biyar matar ta dauko ta Bata,
“Ki jirani nan…” Inji matar Sannan ta shiga cikin falonta, Bata yi wasting time ba ta fito da gyale tare da car keys dinta, sai adua take Allah yasa a amince don Tasan ba karamin samu bane in kayi hulda da family isa bala, dija sai mar mar da idanuwa Kawai take, mota matar ta fidda daga parking lot dija ta shiga ciki duka kama hanyan garinsu.
Karfe biyar da minti ashirin suka iso kofar gidansu dija, da Sauri dija ta fita ta shiga gida matar ta fito tana kallon kauyen tana mamakin
Ya akayi suke rayuwa a irin wannan wuri don tamkar bayan duniya suke saboda karanta kauyen, dukda ba cikin gari take ba amma Sam batasan daura yayi extending zuwa haka ba. Dija na shiga gidan ta fara kwala ammi kira
“Ammi!!…ammi!!!…” Ta dinga fada tun.zaure, ammi dake kada miyan kuka ta mike da Sauri saboda yanda gabanta ya fadi don kiran dija har cikin zuciyanta saboda yanda take kwala mata kira on top of her voice, da Sauri ta ta taro dija dake shigowa, kallon ta tsaya yi hannun ta dafe da kirjinta,
“Dija lafiya?…” Ta tambayeta cikin tashin hankali, dija kallon ta tayi da gwala2 idanuwanta tana murmushi
“Ke lafiya?…” Ammi ta sake tambayeta tana kallon ta from head to toe,
“Lafiya lau..wata Hajiya ce ta zo wurin ki…” Ta amsa mata tana ajiye roban furan ta, kallon mamaki ammi tayi mata,
“Wacce Hajiya?…” Ta tambayeta,
“Gata nan…” Dija ta fada tana nuna matar data shigo cikin gidan da sallama, da Sauri ammi ta amsa tana kallon ta,
“Barka da zuwa…shigo mana…” Ammi ta fada jikinta NA rawa don batasan abinda dija tayi ba da aka biyota, da Sauri ammi ta shiga cikin dakin matar ta bi bayanta tare da daga labulensu da ya kasu kusa kashi takwas saboda yanda ya yage, ta kasan wusiya matar ta dinga kallon dakin tana mamakin how living creature can sleep in such an awful place, ammi kakkabe tabarma dake kasa tayi jikinta sai rawa yake Kuma zuciyanta tamkar ya fito ta bakinta saboda fargaba. Dija kam gefe daya ta tsaya tana aduan Allah yasa a samu nasara, Da Sauri ammi ta debo ruwa cikin randa ta mika wa matar tana cewa
“Maraba..maraba…” Cikin faraa matar ta amshi ruwan amma tasan ko da wasa bazatyi gigin kai kofin bakinta ba, rike cup din tayi tana kallon dija dake ragube jikin bango tana kallon su, murmushi ta sakar mata itama dija tayi karfin halin maida mata martani, ammi durkusawa tayi kasa kneels dinta biyu kasa sai tafin hannun ta biyu suma kasa
“Ina yininmu…” Ammi ta gaidata, cikin faraa matar ta amsa da
“Lafiya lau..ya gida ya yara?….”
“Lafiya kalau suke….” Ammi ta fada Sannan tayi shuru tana sauraron abinda ke tafe da matar, ahankali matar ta ajiye cup din Sannan ta fara cewa
“Sunana Hajiya Aisha…ina zaune a cikin garin daura…ina Sana’a kala2 cikin su har da kai yara gidan gidan manyan mutane don suyi masu aiki don gyara rayuwan yaran…” Ta Dan yi shuru ita Kuma ammi dai tana nan durkushe tana sauraron ta, Hajiya Aisha ta cigaba dacewa
“To da akwai wata kanwar aminiyata dake son mai aiki karama daidai kaman yarki dija…shine ta shaidamin…” Da Sauri dija ta dan buga kafa kasa wai ita mai wayau don kar ta fadi ita tace tana son aikin, Kuma Hajiya ta gane sai tayi shuru ta chanza maganan zuwa
” shine naga yarki nace bari in biyo in tambaya ko zaki amince in kaita…” Ammi da kanta ke kasa sai ta fara girgiza kai alaman AA, dija dake tsaye tana kallon su nan take taji kwaiwanta yayi sanyi don Kawai so take ta je.
“Gaskiya Hajiya kiyi hakuri… Yarana marayune…nice uwarsu nice ubansu tunda yawancin yan uwan ubansu basu damu da suna raye ko suna mace ba…nasan muna cikin hali amma gaskiya nafison in wayi gari in gan dukkan yarana kusa dani…ko kadan banason abinda zai taba masu mutuncinsu saboda nasan yanda ake wulakanta marasa karfi cikin birni…” ta fada ahankali cikin natsuwa da sanyin murya Kuma har lokacin bata mike daga inda take ba, ahankali matar ta daga kai ta kalli dija da idanuwanta suka ciko da kwallan bakin ciki, murmushi Hajiya ta saki Sannan tace
“Babu komai…amma yar uwa inason in shaida maki cewa babu inda mutuncin ya mace ke saurin zubewa kaman talla saboda yanda duniya ta lalace… Da akwai maza azzalumai Wanda suke gurin lalata rayuwan yaran mata mussanman wayanda ke yawo kan titi….” Ahankali ammi tace
“Allah NA tsarewa ai…ni kaina don babu yanda zanyi ne amma ko kadan yata Bata talla” Ta fada cikin sanyin murya, ahankali Hajiya Aisha tace
“ga dama nan…NA daya yarki Bata zuwa koina tana cikin gida..Kawai ta kula da bangaren uwar dakinta Kuma ba ita kadai bace…Sannan duk wata zaa aiko da albashinta Wanda INA tabbatar maki yafi talla saboda ita Bata wahala ba ke baki wahala ba….Kuma wannan gidan da nake fada maki suna kuka da masu aikinsu tamkar yaran da suka Haifa don har boko da islamiyya suke saka su sai na karshe ina tabbatar maki dacewa zaa kare maki mutunci yarki…don haka ina baki shawaran da zan bawa kaina…ki gwada ki gani in hakan baiyi maki ba kina iya bukatan a maido maki ita….” Hajiya Aisha ta karasa maganar ta tana kallon dija dake hawaye, ammi dai shuru tayi har saida Hajiya ta kai aya Sannan tace
“Ni gaskiya nafison in tashi in ga yarana kusa dani…Sam hankali na bazai kwanta ba duk lokacin Dana tuna yata tana wani wajen Kuma basan irin halin da take ciki ba…” Ta fada kanta kasa, da Sauri dija ta fita daga dakin tayi waje ta fara kuka sosai kaman an doketa