NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

®Zuwairat (ummumaryam)
CONTINUE TO 33
Sai karfe uku da rabi su dad suka isa kano. Gidan alhaji Yunusa suka bi suka ajiyeshi sannan suka wuce gidansu yazid dad ya shiga sannan driver ya wuce da Salem gidansu bayan dad ya gode Mashi. Bayan yayi freshen up su mom suna falo suna jiran ya gama cin abinci don they are earger to hear what he will say. Saida ya gama sannan ya dawo falo. Ya fara cewa
” alhamdulillah our visit was a success… Iyayen yarinyan are welcoming… Beside an daura masu aure….” Bai idaba Hajiya karama ta Dau
“Ayyirrrrrrrrr!!!!!…” Har saida dad ya dafa kunnenshi, Hajiya babba murmushin jin dadi tayi da abun yazo a saukake.
“Naji dadi wallahi….yanzu biki kawai ya rage?…” Hajiya babba ta fada.
“Yes…kawunta yace zai kirani in sun gama maganar ranar that is suitable to them….” Ya fada yana jinginawa ga kujrera,
“Kai yara maza sunyi wallahi…cikin few months mun samu surukai har hudu…” Inji Hajiya karama tana dariya, murmushi Hajiya babba tayi shi kuma dad kura mata ido yayi yana imagining yanda akayi bata sanin ta girma, don wani lokacin in tayi abu kaman yar yarinya,
“Yanzu dai mu fara hada lafe….” Hajiya karama tayi adding,
“No…shi zaiyi da kanshi….” Inji dad,
“Ya zaayi yayi da kanshi…ai wannan rashin adalci ne…..” Tafada tana turo baki kaman yarinya,
“Meye na rashin adalci?… Ba anyi Mashi na farko ba?…. Anyway ai kina da kudi…kiyi Mashi mana…” Dad ya fada mata cikin harshness, zata bude baki tayi magana Hajiya babba tayi mata alaman tayi shuru da ido.
Saida suka fita Hajiya karama ta fara cewa
“Anty gaskiya a zama dole mu taimaka Mashi…sabida nasan shi zaiyi kayan daki da komai tunda parent din yarinya are not buoyant…” Tafada lokacin da suke shiga part din Hajiya babba,
“To shikenan…sai mu kira a hada mana exactly irin wanda aka hadawa su Sharif…in yaso in yana da interest din kara wani abu sai a kara…” Inji Hajiya babba, dariya Hajiya karama tayi tana cewa
“Thank you antyna….” Itama dariya tayi sannan tace
“Babu wani thank you…ai 50 50 zamuyi wajen biyan kudin tunda yace bai badawa….” Inji mom
“Wannan babu case….” Hajiya karama ta fada tana zama kan kujera, kallon ta Hajiya babba tayi tana tunanin Allah ya bawa Matan kishiya irin Nata don tana jin dadin yanda take nunawa yaran tamkar ita ta haifesu mussaman yazid.
Da sauri hajia karama ta dauki wayanta ta kira Wanda ya hada lefensu shahid ta shaida Mashi suna bukatan exactly irin wannan.
Har yazid ya tashi yana expecting call din dad sannan yana tunanin abinda zai fadawa mufida. Gani yayi karfe biyar dad baice Mashi komai ba, kiran Salem yayi ya kara tabbatar da abinda ya fada Mashi. Sannan ya kira dad. Bayan sun gama gaisawa yace
“Dad…yau kaje factory ko?..how is it going?…” Ya tambayeshi, dad murmushi yayi
“This boy think he’s smart…am your father…” Ya fada cikin ranshi saboda yasan already Salem ya fada Mashi abinda akayi
“Very fine…” Dad ya amsa Mashi,
“OK…bye… ”
“Alright…” Dad ya fada sannan ya katse wayan shi.
Yazid zama yayi ya rasa abinda ke yi Mashi dadi don he wants to hear the word from dad don yaje Kano for the house preparation don yasan basu da halin yi mata komai kuma baison asan shi yayi komai mussaman mufida. Kuma ko suna da halin yi mata vaison wahalar dasu don he wants to show them.he really appreciate., bayan sallan ishai dad bai CE Mashi kala ba, kawai sai yayi deciding gobe zaije Kano amma bai barin su San yana Kano sannan ko mufida bata Sani yana Kano cos yau taje family house dinsu don haka zai sauka a gidanshi yasa ayi furnishing part din da dija zata zauna.
A chan Jos bayan kawu nanu yaci yasha bai fadawa kowa abinda ke tafe dashi ba sai bayan sallan ishai. Kiran ammi yayi da sauran manyan gidan. Sannan ya fiddo dubu darin da aka bashi na sadakin dija ya ajiye, dukkansu kallon juna suka farayi
“Na meye wannan?…” Wani dan uwan ammi ya tambayeshi,
“Wannan sadakin dija ne…” Da sauri ammi ta kalleshi,
“Ban ganeba…” Ammi ta tambayeshi
“Eh wannan mutumin dayayi mata ciki.. Iyayensa sukazo da maganar dansu zai aureta…ni kuma na basu don nasan hakan yafi daidai….kuma nan take aka daura masu aure….ko banyi daidaiba?..” Yafada yana mazurai, ajiyan zuciya ammi ta saki amma bata bari kowa yaji ba,
“Nace ko banyi daidai ba….” Ya fada yana kallon faces dinsu domin ganin reactions dinsu,
“Haba kai kam kayi daidai…daman in bashi din ba was zai aureta?… Kayi daidai wallahi…Allah ya saka maka da alkhairi…” Inii dan uwan ammi, ita kuma ammi tace
“Mun gode….”
“Meye na godiya?… Ba yata bace?… ” yafada cike da haushin ammi don tunda taki amince Mashi ya tsaneta.
“Yanzu Sunce mu yanke hukuncin yaushe zaayi shagalin bikin?…” Inji kawu nanu, cikin nutsuwa ammi tace
“Ni in a tunanina ne ba sai anyi wani bikiba..kawai in an sallameta daga asibiti a wuce daita gidanta…ko ya kuka gani?…” Tafada kanta kasa,
“Daman su suka fadamin an fidda namiji daga cikin ta…” Inji kawu nanu,
“Gaskiya hakan ma yafi…Don in akace zaayi biki tamkar wani bacin sunanne don ga jariri ga biki…gwara kawai daga chan asibiti a wuce daita kawai…tayi abun kunya sai taje chan taji da shi….” Inji danuwan ammi, abban ammi nodding kawai yayi with acceptance
“Hakan yayi daidai…” Kawu nanu ya fada, complimentary card da dad ya bashi ya fiddo yana cewa
“To Ku bari in kira uban yaron gabanku don na fada Mashi zan shaida Mashi duk yanda akayi yafada yana saka daya daga cikin digits din dad dake jikin card din. Bayan ya gama sakawa cikin the oldest phone on earth yayi dailing number ya kanga da kunnenshi. Lokacin dad na zaune tsakiyan matanshi, Hajiya karama na rike da plate of watermelon yana dauka daga cikin plate, kiran wayan ya katse silent dake dakin, picking yayi tare da sallama, daga chan bangaren kawu nanu ya amsa tare da tuna Mashi ko shi waye sannan ya fara cewa
“Alhaji na isa Jos kuma na fada masu komai har da maganar bikin… Amma sunce kawai zasu so a dauketa daga asibiti a kaita dakinta…amma ban San ko hakan zaiyi maku ba.. ” inji kawu nanu, dariya dad yayi
“Ai babu matsala….hakan ma yayi….” Yafada sounding excited,
“To alhamdulillah tunda hakan yayi maku….” Kawu nanu ya fada Mashi. Sannan ya katse wayan.
????????????❤????????????????????????❤????????????Bayan dad ya gama waya ya fadawa su mom yanda sukace, mom ji tayi jikimta yayi sanyi”
“Wato abandoning dinta zasuyi kenan…basu damu ayi bikinta ko su San wa zata aura ba…kome ya sameta they don’t care where she goes…” Mom ta fada cikin sanyin murya,
“Ai duk danku ne ya ja mata… ” inji dad,
“Wahalanta will be over soon…duk Sai sunce inama yarsu akayiwa fyaden…yan iska kawai…” Tsoki dad yaja saboda maganar Hajiya karama.
Around 9:30pm yazid na kwance cikin blanket yana waya da mufida dajin muryanshi his moody Sai yaji kaman ana kiranshi, yana dubawa yaga dad da sauri yayi excusing mufida yayi picking, nan dad ya fada Mashi ya zo Kano gobe, da sauri ya amsa da OK, zai bude baki yayi magana dad ya katse wayan.
Tsalle ya farayi kan gadon saboda farin ciki, he can’t still believe sweet khadija is his personal property, yana tuna mufida Sai jikinshi yayi sanyi, ahankali ya koma ya zauna tare da sake dailing number ta, bayan tayi picking tace.