NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Yes baby…what is the problem?…” Ta tambayeshi tana kallon eye balls dinshi,
“Baby I want you to know komai rubuce yake….we can’t stop destiny….”
“Dan Allah ka fadamin abinda ke faruwa.. ” tafada tana gyara daurin towel dinta, ajiyan zuciya ya saki ya rike palms dinta cikin nashi yana massaging sannan ya fara fada mata exactly abinda ya faru amma banda nuna farin cikin shi, aikam kura Mashi ido tayi sai hawaye sharrrr,
“Na shiga uku….” Tafada tana Dora hannunta kanta, da Sauri yazid ya rike mata hannu
“Pls baby stop it….” Yafada yana kokarin jawota jikinshi, tureshi tayi ta kara fashewa da sabon kuka,
“Wayyo ni mufida….ban kaunar kishiya….ban Iya zama da kishiya…wallahi banason sharing dinka da kowa….I love you…” Tafada cikin matsanacin kuka tana kokarin mikewa daga kan gadon, riketa yayi ya marairace fuska
“Baby pls stop saying such….kinsan ban iyawa su dad gardama…” Da Sauri ta katse shi dacewa
“Kai fuska biyu gareka….you are pretending kaman bakaso…alhalin nasan you are so happy… Nidai kawai ka sake….” Bai bari ta idaba ya kwantar daita kan kirjinshi, yana shafa kanta yana cewa
“Pls don’t say such word….you are the best thing that ever happened to.me…kuma khadija is just a small gal…she will follow our training… Ki kwantar da hankalinki pls….” Yafada yana shafa kanta, amma the more he talks the more she cries,
“Baby pls ka sakeni…kishiya bata karama….” Tafada cikin kuka sosai, kawai sai dariya ta kufce Mashi don sai ya tuna maganar Malam Kabir gombe, wai kishiya bata karama
“Baby ki bari ki gani…naki sister karama CE…mu zamuyi training dinta…kawai pls just try and take her like the sister you never had….pls kiyi min wannan indai kinasona da gaske….” Yfada yana share mata hawaye,
“,ni tsoro nakeji… Kar a rabani dakai…yan kauye suna da asiri….” Tafada gwanin ban tausayi
“No dear… Kawai just have faith.. Pls baby kiyi hakuri..
” lafewa tayi jikinshi tana kuka sosai, sai share duk hawayen daya zubo yake, hannunta biyu ta zagaye waist dinshi ta rike shi gam
“Dan Allah baby ki bar kuka haka nan….I promise zamanku zaiyi dadi….I will never do anything to hurt you….” Tafada ahankali, daga kanta tayi tana kallon shi da red eyes dinta
“Baby banason Sharing dinka da kowa….I love You so much that seeing entering another woman’s part will hurt me badly…. Pls .” kuka yaci karfinta, kara danne kanta da naked chest dinshi yayi yana mata maganar cikin kunne,
“Baby ki kwantar da hankalinki… Kinga I won’t make such mistake again… Babu abinda zai shiga tsakanina daita for years to come….” Daga kai tayi ta watsa Mashi harara
“Lie…”
“No baby am serious…. Ki tsaya ki ganta…zakaisan kawai shaidan ne ya rude na sadu daita.. Amma not because ta girma…so pls ki kwantar da hankalinki… Just feel like zaa kawo maki younger sister…. Basan bari ta rainaki ba….sannan ke kuma ki rike girmanki…she’s 14… Kinga you are 8 years older than her… Don haka ki kwantar da hankalinki don Allah… Am assuring you bazakiyi regretting hakan ba…..” Ya rada mata cikin kunne. Dan saurarawa tayi sai ajiyan zuciya kawai take, wai 14, she hates him so much, ko shekara basuyi da aure ba amma har yayi mata kishiya, yanzu she wish bata aureshi ba, tanada masu sonta da yawa amma ta nace sai shi, now ga irin shi nan,
“Yanzu nasan you don’t love me as much as I loved you…inda kanasona baxakaji shaawan wata ba balle ka aikata wani abu daita….wallahi saboda kai bana ganin kowa as namiji sai kai….” Tafada tana kara fashewa da sabon kuka sosai, patting bayanta ya dingayi yana cewa
“Wallahi ba sonki ne bayi ba…kawai bazaki gane bane….It was beyond me…..” Mufida banza tayi dashi ta cigaba da kukanta har saida jikinta ya Dau zafi,
“Baby tell me abinda kikeso…zanyi maki….” Yafada mata cikin kunne, mufida dake shessheka tace
“Kawai ka bari in tafi gidanmu….in kun gama amarcin sai in dawo…..”
“No dear…ita nan Kano zan barta….” Yayi assuring dinta.
“Ni banson ka barta nan Kano.. Kar kajamin…kawai Ku tafi…bayan wata uku sai ka dauko ni..pls am begging you….” Tafada cikin sanyin murya, murmushi yazid yayi yana cewa
“Kashe ni kikesonyi kenan…ai wata uku with out you will be unbearable….”
“Ba wani…” Ta amsa Mashi.
“Kawai ki fadi abinda kikeso inyi maki….”
“Ai na fada maka….”
“Wannan bazai yuwu ba..make another request…ko in sake maki mota?…” Da Sauri tace
“Banso…”
“To in kaiki umrah…”
“Banaso….” Tafada tana hararanshi
“To in baki 1m ki fara home business….”
“Banso….” Tafada har da murguda Mashi baki, shuru yayi kaman mai tunani, daria ya farayi
“To me kikeso….”
“Ai I told you.. Kawai ka barni gida for 3 months….ko kuma ni ka Barni nan Kano ka tafi daita….”
“Hmmm no way….”
“Ai ina kishi in ganka kana magana da wata…”
“Babyna just wait and see…” Yafada. Haka ya dinga rarrashinta yana kwanta mata da hankali har bacci ya dauketa amma still koda ta tashi tambayanshi tayi if an daura Mashi aure ya amsa mata da yes nan ta fara sabon kuka kuma kafin dare fever ya rufeta amma ko ruwa batasha balle tasha ci abinci tasha magani, haka yazid yayi tagumi ya zauna gabanta yana kallon ta tana kuka har ta kara komawa bacci sai firgita kawai take.
Itama dija ban da kuka babu abinda takeyi har ta fara dafa kasan maranta inda akayi mata aiki don tana kuka tana coughing, lokacin doc bai nan saida nurse taga abun da gaskene don kuka take sosai hannunta rike da cikinta ta kira doc ta sanar dashi. Bayan kaman minti talatin yaso yaga dija sai kuka take, komawa gefe yayi dailing number yazid, lokacin ya dawo daga masjid, ganin doc ke kiranshi yasa ya koma gefe sannan yayi picking, nan doc ya shaida Mashi Halinda dija ke ciki,
“Pls doc do something… Kar dinkin ya kunce….”
“Wani abu akayi mata?…” Doc ya tambayeshi, yazid shuru yayi yana tunanin kilan an fada mata she’s married to him ne,
“Ai kune kusa daita…nidai just do something… Ko alluran bacci ne kayi mata…in ta farka in bata daina kukan ba ka kara mata…I don’t want anything to happen to her pls…” Yafada cikin tashin hankali, daria doc yayi yana cewa
“We don’t work that way…amma it will be better in zakayi mata magana…kiln ka kwantar mata da hankali…” Inii doc, idanuwa yazid ya zaro wishing inama yana Iya rada mata sweet words cikin kunne ta amma yasan it won’t help,
“Doc ai tunda aljanu suka shafeta bata son ganina balle jin muryata…kawai take care of her.. ” yafada agajiye don today is among the longest day of his life, kashe wayan yayi ya dan jingina da bango yana tunanin Ashe haka yake da wahala hada nauyin mutum biyu bisa kanka,
“Hmmm masu mata uku suna kokari….” Yafada ya kama hanya part dinshi.
Part dinshi ya koma ya tarda abinci kan dining while mufida na bacci sai ajiyan zuciya take saukewa. Komawa yayi falo ya cika cikin shi da abinci sannan ya zuba cikin plate ya rufe y kai bedroom ya ajiye kan side locker. Yafi hours zaune yana jiran mufidata tashi taci amma bata farka ba, daya gaji da zama ya kwanta.
Har garin Allah ya waye mufida bata ci komai ba sai kuka, farat daya yanayinta ya Chanza, duk ta susuce. Tea ya hada ya bata ta ki amsa yayi Iya kokarinshi amma bata amsa ba.
“Pls baby in har you love me….ka bari in tafi gidanmu…ranar da zamu koma abuja sai kazo ka daukeni…pls I beg you. ..” Tafada cikin dishessen murya..