NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“OK…” Kiyi wanka in kaiki…ranar Saturday zanzo maidaki gidanmu cos kinsan ke zaa bawa khadija… Sannan ranar Sunday zamu wuce abuja…I will give you the space you need ….alright?… ” yafada yana rike da hannunta, kai kawai ta daga Mashi, mikewa yayi ya hada mata ruwan wanka ta shiga tayi ta fito sai tafiya take kaman iska na kadata. Bayan ta fito shimaya shiga ya watsa ruwa ya shirya, part din mom dinshi suka shiga tayi masu sallama, nan Hajiya karama ta zaunar daita tana bata shawara.
Bayan ya ajiye mufida ya kira mai decorating gida ya shaida Mashi suna gidan suna aiki. Nan ya kama hanyan gidan don ganin how it’s going.
Around 11am ya dawo gidansu inda ana ta shirye2 kai kayan lefen jos. Godiya ya kariya wa Salem cos still shi zai rakasu. Already doc Zara da nanny da akayi hiring don kula da Mahmud suna hanya
Dija dai idanuwa sin kumbura sosai sabida kuka, yau ma data tashi bata bar kuka ba, tana zaune around 2pm aka shigo da yaron, ko daga kai batayi ba don banda tunani babu abinda takeyi, nan aka shaida Mata zaa tafi da yaron kaman yanda doc ya bukata,
“Ina zaa kaishi?…” Shine tambayan datayi masu,
“Inda zaa raineshi zaa kaishi…” Shine amsan da doc ya bata. Bata kara cewa komai ba aka fita da yaron.
Mufida na shiga ta fada jikin mom dinta tana kuka, cikin tashi hankali ta fara tambayanta abinda ke faruwa nan ta fada mata abinda ke wakana,
“Don kishiya kike wannan kukan?… Har ya rainaki?..amma am so disappointed in you …” Inji mom dinta
“Mom I love him ai….” Tafada cikin kuka sosai
“Mtwsss…amma iliminki baida amfani… Kinsan dai yazid yana sonki…so kawai kija hankalinshi…you know mu bamu bin boka ko Malam amma namiji yayi kadan ya wulakanta mu…don haka ki dauki kishiya as zero behind a decimal point… Kinji ko?…”
“Yes mommy… Yace nan zai barta”
“Kar ki yarda….ya tafi daku tare…karki yarda ya gama dake sannan ya dawo kanta…kowacce halinta ya ficeta….kuma zan kira Hajiya hannatu ta kawo maki sabon kayan harka…kawai ki kwantar da hankalinki kiji ko?…”
“Yes mommy…” Ta fada tana lafewa jikin uwarta.
Shima yazid shaidawa su mom da dad yayi kan zai bar dija Kano suma sukace Sam basu yarda ba ya tafi dasu.
Akauyen kam da aka kawo lefe ba karamin surprise sukayi ba don tunda suke basu taba ganin abu Irin wannan ba, duk garin taruwa sukayi suna kallon lefen nan fa maganar Hajiya karama ya zama gaskiya don ji suke ina yarsu ta samu irin wannan abun arzikin. Wasu ma cewa suke da ansa biki don ko bakomai zasu ci shinkafa.
Ada suna son a kai dija gidan mijinta straight from the hospital amma yanzu an sake shawara kan a maidota gida ta shirya sai a kaita dakinta. Wani kawunta aka aika ya tambayo yaushe zaa sallameta nan aka shaida masu ranar asabar da safe.
~Saturday~
Da wuri doc ya sallami dija inda wasu sis din amminta suna jiran a sallameta, sunajin doc ya ce ya sallameta suka fara shirya kayanta. Bayan sun gama suka tsaida taxi suka shiga da dija da kayanta, sanyi dija taji don gani take kilan an fasa auren cos ammi ta fada mata daga hospital zaa wuce daita amma gashi an kama hanyan gidansu ammi. Ba karamin dadi takeji ba zata kara ganin amminta. Suna isa ta fito tana tafiya ahankali sannan tana daga gaban riganta don kar ya gogi inda akayi mata aiki. Tana shiga cikin gidan duk suka rungumeta wai suna murnan ganinta, baki ta washe don ta mance rabon da taji irin wannan farin cikin. Inda ammi ke zaune taje ta zauna gefenta. Gani ayi ai gidan ciki da mutane har wayanda ba cikin gidan suke zaune ba. Kowacce sai kallon ta suke, sadda kanta kasa tayi don she was thinking saboda cikin da akayi mata ne yasa duk aka zuba mata ido. Baban ammi ya kira ta ta tashi tana biting bottom lip dinta saboda zafin inda aka yi mata aiki. Tana shiga yasa ta zauna nan ya fara bata advice kan rayuwa.
.abangarensu yazid komai is ready, part din dija kaman ba yar gidan talakawa ba don few things mufida zata nuna mata,komai looks wonderful and beautiful. Karfe biyu motoci hudu suka kama hanyan gidansu ammi, cikin motan Salem wata matace mai kyalliya dauke da kit guda biyu, daya na kayan aikinta sai dayan na kayan da hajjya karama ta saya a sakawa dija.
Yazid rike Salem yayi yace
“I promised babu mai hanaka auren Maryam sai Allah…” Yayi assuring dinshi sounding very firm. Dariya kawai yayi ya shiga mota suka bar gidan tare da sauran wayanda zasu dauko amarya.
Yazid kira doc yayi ya umarceshi daya rubuta Mashi drugs din dija zai saya anan haka akayi. Daga pharmacy ya wuce gidansu mufida don daukarta. Yana shiga falon gidansu gabanshi na faduwa amma to his surprise da gudu mufida ta fado jikinta,
“My baby…” Yafada yana. Kallon yanda babu sauran damuwa tattare daita
“Yes sugar….”
“Am happy you are OK?…”
“Yes sugar… Nayi tunani kuma naga babu komai cikin dunyia….after all who are we to question the will of Allah…” Bata idaba ya kama bakinta ya fara kissing dinta forgetting ba gidansu bane. Sai da suka zama both breathless sannan ya saki bakinta
“I love you…”
“Love you too…”
“Now baby kije ki shirya muje gidanmu muyi like 3 rounds kafin a kawo sister dinki….” Yafada sounding very naughty, fari tayi da idanuwa sannan tace
“Yes baby…anything for you…” Tafada tana juyawa tare da gada Mashi kugu, dariya yazid yayi yana cewa
“Nasan yau kasheni zakiyi….”
Karfe biyu da rabi su Salem suka is a kofar gidansu ammi, da gudu yara suka shiga cikin gidan suna
“Sunzo da motoci da yawa….sunzo da manyan motoci….” Nan gida ya hargitse, gaban dija faduwa yayi ta fashe da kuka, ba komai take tsoro ba illa abinda yazid yayi mata, ba wai tasan shi aka aura mata ba amma kawai tasan ko ma waye yau sai yayi mata irin abinda yazid yayi mata. Kara fashewa tayi da kuka suka hada ido da ammi, harara ammi ta watsa mata nan take ta hadiye kukan, daman ta sakata dogiwar Riga. Sallama matar dake kwalliya tayi aka amsa mata, daman already matan gidan sun fara shirin raka amarya da suka ga luxury cars.
Matar Neman amaryan tayi aka nuna mata, nan ta baje kayan aikinta ta fara tsara mata kwalliya within few minutes dija ta Chan za from dijan kuaye to khadija yazid, ( remember no body is ugly… Inji psquare????) baki duk yan gidan suka bude suna kallon yanda ake transforming dija zuwa wata. Bayan an gama makeup aka saka matadoguwr Arabian gown mai dauke da hijjab.
[6/22, 5:56 PM] ᴬᴮᵁᴮᴬᴷᴬᴿ ˢᴬᴸᴱᴴ: ????????????????????❤
NA CUCE TA
????????????????❤????
®Zuwairat (ummummaryam)
3⃣5⃣
_Follow me on:_
*Wattpad @ummumaryam29*
*Email:Zuwairat.nuhu@gmail.com*
*IG: zuwairatummumaryam*
*Website:Www.ummumaryam.com*
*And also join my new Facebook group: Zuwairat ummumaryam and Zuwairat ummumaryam page.*
*Snapchat: ummumaryan29*
Bayan an gama aka saka mata shoes da suka hau da sky blue Arabian gown dake jikinta. Perfumes matar ta fesa mata sannan ta tattara kayanta cikin bag tace
“Amarya kinyi kyau….” Tafada tana fiddo waya daga cikin pause dinta, pics tayi mata sannan ta fita daga dakin, ita ai dija sai feeling so weird don gani take kaman an damkar mata buhun cement a face dinta don nauyi taji fuskanta yayi mata.
“To ki tashi mu tafi….” Wata yar uwan ammi ta fada mata, jiki ba kwari ta mike idanuwanta cike da kwalla amma basu zubo ba, wurin grandparent dinta aka kaita suka karayi mata adua sai wajen amminta nan dija ta dinga kuka kaman ranta zai fita, tana kuka tana dafa maranta. Saida ammi ta daka mata tsawa sannan tayi shuru