NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kuma wallahi kar ki bari inji ance kiyiwa mijinki laifi…duk abinda yace kiyi kiyi kina jina?”…” Da Sauri ta daga mata kai

“Allah ya kaddara saduwanmu…tashi ki tafi Allah ya yi maki albarka ya yafe maki kurakurenki….” Jiki na rawa dija ta mike mata na biye daita, suna fita waje mata na tsaye cike da waje wasu sunyi ready zasu bi ta don kashe qarkwatan idanuwansu. Bayan an nunawa dija motan Salem ta shiga baya sai kuka take, sai yau Salem yaga dija, duk da kanta na kasa jikinta ya nuna karamar yarinya ce, murmushi yayi ya kauda kanshi gefe cikin ranshi yana cewa

“Shege yazid….” Salem lekawa yayi a mirror yaga yanda mata ke rige2 shiga mota

“Allah yasa kar su lalata masu mota. Bai Ankara ba wasu mata kusan su uku suna kikarin shiga gidan gaban motanshi, sai ture juna suke kaman wasu awakai, kaman yayi magana sai kuma yayi shuru

“Ki bari ni na kamata in bita ba ke ba…” Inji daya daga cikin su,

“Lallai ma…” Daya ta fada, matar datayiwa dija makeup dake zaune baya kusa da dija ta tabe baki sannan tace

“Haba kubi ahankali mana…ko so kuke Ku lalata masu mota…” Tafada cikin tsiwa da Sauri suka ja baya daya ta shiga. Salem ya fixgi motan suka bar wajen, duk sauran cars na dauke a mutane 8 biyar baya sai biyu gaba da driver. Salem kam yayi deciding bai maidosu saidai ya samo bus da zai maidosu, babu abind ke tashi cikin motan sai sheshekan dija.

Bayan sun gama sukayi wanka tare mufida ta zauna gaban mirror yazid ya goge mata gashi da karami towel sannan ya shafa mai hair cream tare da combing kan, kawai yanayi yana kallon ta tacikin mirror yana aduan Allah yasa this is not a trap don ko kadan babu wata damuwa tattare daita hes wondering how comes don lokacin daya shaidawa mufida halinda ake ciki tamkar zaa kwantar daita hospital, hannunta data dora kan hannunshi ya maidoshi hayyacinshi, murmushi ya sakar mata yana cewa

“Baby I love you… Kinsan wannan shine abinda kikayimin daya fi komai burgeni…thank you.. ” murmushi tayi dukda maganar shi ta bata mata rai wato duk kokarin da take wajen biya Mashi bukatan shi bata burgeshi kaman wannan ba, amma ko kadan bata nuna Mashi hakan ba saboda advice da mom dinta ta bata.

“Baby na zauna nayi tunanin babu komai duniya…sannan banason rabonda ke tsakaninka daita ya aikadani lahira…so kawai Allah ya bamu zaman lafiya…kuma pls promise me you will love and cherished me all the days of my life….” Tafada Mashi cikin natsuwa, hannuwanshi yayi rounding waist dinta daga inda take zaune yayi hugging bayanta,

“Baby I will love you for ever…I wish dukkan mata zasuyi yadda kikayi…su San cewa what will be will always be nor matter what….” Yafada yana kissing bayan wuyanta

“Baby I love you too…” Tafada tana shafa face dinshi dake bayanta.

“Yanzu baby tell me abinda kikeso inyi maki….” Shuru tayi kaman tana tunani for a while sannan tace

“Why not mu bari muje umrah tare….” Dadi yazid ya karaji ya kara rungume yana jin wani irin sonta da kaunarta har cikin system dinshi.

“That sounds perfect my Queen… Yanzu yaushe su Aisha zasuzo?…”

“Zuwa later…”

“OK muyi sallah…kafin ki shirya kafin su zo…and pls my Queen kar ki biyewa duk abinda zasuce….I know them too well….”  Murmushi mufida tayi tace

“Baby don’t worry… I won’t let anyone lead me astray…” Tayi assuring dinshi

Murmushin jin dadi yayi bude closet ya saka jallabiya  ya fita sallan asr.  Itama doguwar riga tasa tayi sallah.

Bayan sun ci abinci tace

“Baby kasan au bazan Iya girkin tarban baki ba…ko zakayi mana order na abinci?.. Tunda am sure basu komawa yau…”

“OK…banason kiyi wahalan shiga kitchen after all I have put you through yau…” Yafada yana dariya, hararanshi tayi  tana murmushi

“Kawai zan sa akawo abinci daga one of the restaurant around…”

“Yauwa.. Thanks… ” tafada tana sauraron doorbell da ke kara,

“I think friends dinki sunzo….” Yafada yana mikewa, bedroom ya shiga while ita kuma taje bude kofa. Wasu age mate dinta biyu ne tsaye daya na rike da beautiful baby gal,

“Ya akayi na ganki haka?….” Daya ta tambayeta tana shiga cikin falon, murmushi mufida tayi

“Ya kikeson ki ganni?…Aisha…” Hararanta Aisha tyi while sitting,

“Lallai ma…yazid dinkine yayi aure amma Sam banga alaman damuwa tattare dake ba…kodai karyane….” Dariya mufida tayi tana cewa

“Yo kashe kaina zanyi?… Ai Allah ya kaddara…kuma j know my hubby loves me…kawai ban bari wata ta tadamin hankali…” Tafada tana zama kusa dasu, Aisha da Zainab kallon juna sukayi suka kwashe da dariya

“Amma ke baki San meye kishiya ba…” Inji Zainab,

“Dalla rabu daita….kilan ma karya take baayi  mata kishiya ba cos nasan halinki….”

“Ai kawai na kwantar da hankalina ne…”.

” nidai har yanzu ban yarda anyi mata kishiya ba….” Zainab ta fadawa aisha,

“To Ku tsaya Ku gani mana…”  Tafada tana mikewa,

“Me zan dan dafa maku kafin ayi ordering abinci… Don bani da komai kasa…” Tafada sounding very free. Aisha da Zainab kallon juna sukayi basuce komai ba don her attitude kaman ba mufida ba.

“Nace me zakuci kun tsaya kallon juna….” Iniji mufida,

“Ke mu mun koshi….” Aisha ta fada mata tana hraranta. Haka suka dinga zolayanta na kan karya take baayi mata kishiya ba ita kuma tana cewa su jira su gani.

Around 5:30 yazid ya kira Salem donjin inda suke nan Salem ya fada Mashi, kallon agogon hannunshi yayi yagan in the next 30 to 40 minutes zasu iso. Bathroom ya kara shiga ya watsa ruwa har yanzu bai yarda dija zata kwana nan gidan yau as his wife ba. Yana fitowa ya saka shadda pure white da black senator cap ya fito falo inda mufida da su aisha ke zaune,

“Ango ango….” Mufida ta fada cikin zolaya, murmushi yayi ya mika mata Hannu, da Sauri ta mike ta fada jikinshi, Aisha da Zainab kallon juna sukayi,

“Ango sai kamshi kake…ni har na fara kishi….” Tafada tana marairace face.

“Baby har zolayata kike?…” Yafada yana kallon eyes dinta, dariya tayi,

“Zan je ordering abinci… Zuwa 6 to 6:30 zasu iso…” Yafada mata

“OK…” Tafada tana gyara zaman hulan kanshi,

“Me da me zaa kawo?…”

“Tunda daga rural area suke akawo rice and stew sai drinks…”

“Kaman plate nawa?…”

“Hmmm akawo dai da yawa…dayayi kadan it’s better yayi yawa…”

“OK love… Ke me zakici?…” Ya tambayeta cikin so da kauna, murmushi tayi don tasan ko ruwa bazata Iya kara sha ba muddin Khadija ta shigo gidan nan

“Baby zanci duk abinda zasuci….” Tafada ahankali, Aisha dake sauraronsu Kara kallon Zainab tayi tare da tabe baki,

“Baby are you sure…nasan baki fiya son rice ba….”

“No baby zanci….”

“OK …I love you…” Ya fada tare da yi mata kiss a forehead dinta sannan ya fita ko kallon inda su Aisha ke zaune baiyiba. Tsaye tayi wurin bata juya ba,

“Kinsan wallahi saida yayi mata asiri sannan yayi mata kishiya…” Zainab ta radawa Aisha cikin kunne,

“Maganar ki haka ne….don nasan ko kadan mufida bazata yarda da zancen kishiya ba….” Itama Aisha a fadawa Zainab cikin whisper, cikin sanyin jiki mufida ta shiga bedroom dinta, ta kwanta kan gado tayi ruf da ciki sai ta fashe da kuka saboda yanda zuciyanta ke zafi da kuna

Bayanta su Aisha sukabi suka tardata kwance tana kuka, ahankali suka zauna tare da dafa mata shoulder,

“Kiyi hakuri…sai yanzu na yarda da gaske kike…” Inji Aisha, cikin kuka mufida ta data kai tana cewa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button