NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“To shikenan… Allah ya shige mana gaba..amma zan dawo gobe koda kin chanza shawara.. Ba don komai yasa na fadi hakan ba sai don dija ta shiga raina…haka nan naji ina sonta tamkar nawa…” Itadai ammi shuru tayi Bata kara cewa komai ba, Ahankali Hajiya ta mike tare da dauka handbag dinta, itama ammi mikewa tayi tana cewa
“Don Allah ki tsaya kici turo…” Dariya Hajiya Aisha tayi
“Aa ..nagode kwarai…” Itama ammi Dariya tayi tana cewa
“Ai Baku Iya cin irin abincin mu dake lami…”
“Sam ba haka bane…Kawai na koshi ne…” Ta fada tana fitowa waje ammi na biye daita har waje, ta wutsiyar ido ta kalli kukan dake tafasa tsanwa shar babu alaman kayan miya ciki. Kallon yaran ukun dake zaune tayi ta bude bag dinta ta Ciro Dari biyar ta mikawa babban cikin su wato binto, durkusawa tayi ta amsa tana cewa
“Mun gode…”
“Haba Hajiya…har da wata hidima…mun gode kwarai Allah ya saka da alkhairi…” Tafada tana raka ta zaure,
“Babu komai… NA gode nima…sai goben…” Hajiya tafada tana fita waje, sai ihun dija ke tashi duk ammi najinta amma tayi banza daita dukda Tasan halin yarta da kwallafa amma saidai ta mutu. Hajiya kallon dija data Dora hannu bisa kai tayi tana Dariya
“Haba dija…ki bar wannan kukan mana…in Bata amince ba to Allah bai kaddara zaki ba..kiyi shuru kinji…” Ta fada tana kallon yanda take Bata baki tana kuka kaman anyi mata mutuwa, kara volume din kukanta tayi dataga Hajiya ta shiga cikin motanta. Da gudu ta shiga cikin gida ta kwanta kasa tana cewa
“Wallahi… Ban kara zuwa talla…”
[3:12PM, 3/20/2018] 鈥�+234 806 125 0020鈥�: 鉂ゐ煉滒煉涴煐ゐ煉氿煉�
NA CUCE TA
馃挏馃挍馃挌馃枻馃挋鉂�
庐zuwairat( ummu Maryam)
5鈨�
Tafada cikin matsanacin kuka tare da kwantawa kasa tana rolling kaman wacce akayi wa albishir da mutuwa, babu Wanda ya tanka mata su binto tsayawa sukayi kanta suna kallon yanda take birgima kasa, ko kallon ta ammi batayi ba har tagama zuba wa su binto miya kan tuwon dake cikin kwano Sannan ta shiga ciki, har lokacin dija NA kwance kasa yaran neighbors sai lekota suke don ba karamin ihu take ba tana cewa
“Ban kara zuwa talla…ban kara zuwa talla…saidai yunwa ta kashe mu gidan nan….” Ta fada cikin kuka, ammi na shiga cikin dakin ta nufi inda take ajiyan bulala ta yo waje, dija dake kwance na ganin ammi da bulala ta tashi tayi waje da gudu tana kuka,
“Shegiya da kin tsaya yar banza….” Ammi ta fada tana maida bulalan. Har bayan sallan magrib dija Bata dawo gida ba tana nan labe gefe daya tana kuka gashi har lokacin Bata bar fargaban abinda ammi zatayi mata ba.
Ammi na ganin Bata dawo ba tasa binto ta nemota, sanin inda take zama in tana kuka yasa binto bata sha wahalan gano ta ba,
“Kizo inji ammi…” Ta fada mata, hararanta dija tayi da red eyes dinta tana cewa
“Ki wuce ki bani wuri…”
“Ammi tace kizo …” Binto.ta sake fada mata, aikam sai ta rarumi takalminta binto NA ganin hakan ta bar wajen da gudu taje ta fadawa ammi yanda sukayi daita,
“Ta shigo Dan kanta…” Ammi ta fada tana shiga cikin daki, har bayan sallan ishai dija da zaune inda take tana kukan bakin ciki, gani take gwara Kawai ta amince tana son dan Musa suyi aure kamar yanda yake yawan fada mata dukda batasan burouban da akeyi cikin aure ba amma ko kadan batason ta kara talla, tana nan zaune Bata ankaraba taji an damketa da Sauri ta daga kai taga ammi, baki ta bude zatayi kuka ammi ta dora yatsanta daya kan bakinta tana cewa
“Wallahi kika sake naji bakinki sai NA lahira ya fiki jin dadi…maza tashi ki shige min gaba…” Amma ta fada tana rike daita don tasan dija da kafan gudu kaman taci kare, da Sauri dija ta mike ra shiga gaban ammi suka taho gida sai shessheka Kawai take saboda yanda tayi kuka, daki ra shiga ta rabe jikin bango tana sauraron abinda ammi zatayi mata, ammi ce ta shigo rike da kwanon tuwo ta ajiye gaban dija
“Maza ki zauna ki cinye kafin ki ci ubanki….” Ammi ta umarceta, babu musu ra zauna ko hannu Bata wanke ba ta fara cin tuwon, ko kai Bata dagaba har saida ra cinye tas saboda sanin halin ammi, tana kamawa ta daga kai ta kalli ammi dake kallon ta, ahankali ammi ta fara cewa
“Yanzu dija kin fi son gidan wasu kan gidan mu?… Kinfi son zama da wasu kan zama damu?…” Ta tambayeta cikin natsuwa, dija shuru tayi batace kala ba, ammi ta cigaba dacewa
“Yanzu kinfison inda zakije a maidaki kaman baiwa?…baki da gatan komai sai yanda akayi dake?… Dija njasan bani da ko sisi amma ban barin wani ko wata ta wulankanta Mani Ku….yanzu tambaya daya nakeson yi maki…kin fison zama dxa wasu kanmu?….” Da Sauri dija ta girgiza mata kai,
“To wane dalili ne yasa kike kuka don NA hanaki zuwa aikatau?…” Ammi ta sake tambayan ta, tana shessheka ta fara cewa
“Ammi….Kawai inason mu dinga samu kaman yanda su hase ke samu…”
“Kinsan halin da take ciki?…” Bata idaba dija ta katseta dacewa
“Ammi babu halin da take ciki..kalli yanda ta koma ranar da ta dawo…Kuma tace min har boko take zuwa…nidai ammi ki bari in je…in babu dadi zan dawo…” Tafada da gaske, ammi.zama tayi tana kallon ta cike da mamakin yanda take magana babu alaman tsoro, kara fashewa tayi da kuka tana cewa
“Dan Allah ammi ki bari inje…in da akwai matsala zan dawo…Kuma ni wallahi inason boko…” Ta fada cikin kuka,
Ammi tsaya kallon ta kawai tayi saida tayi kukan mai isanta Sannan ammi tace
“Amma kinsan cewa ba ni kadai ke da iko da Ku ba ko?…. Dukda yan uwan ubanku basu damu da Ku ba nasan da zaran wani abu ya faru zasu samu bakin magana…” Da Sauri dija tace
“Ai duk suna birni…kawu nanu Kawai ne nan…ammi muje mu fada mashi….” Ta fada har jikinta NA rawa,
“Badai yanzu kike nufi bako?…” Ammi ta tambayeta, sadda kanta kasa tayi Sannan tace
“yanzu..” Tafada tana murmushi,
“Jaira… Babu inda zamu yanzu ..saidai gobe..in bai yarda ba sai ki hakura…” Inji ammi,
“Nasan zai yarda…ai ba damuwa yayi da rayuwata ba….” Tafada cikin jindadi, hararanta ammi tayi Sannan tace
“Je kiyi salla…nasan rabonki da salla tun NA zuhr…” Bata idaba dija tace
“Ai har yanzu ban gama ba…”
“Amma kaman kinyi salla da zuhr
” aa NA duba naga har lokacin bai tsaya ba balle inyi wanka…”$ ta amsa mata kaman ba ita bace ke kwance kasa tana kuka kaman wata yar karama yarinya.
“Je ki kara dubawa…” ammi ta fada mata, da Sauri ta mike ta fita.
Yazid NA zaune kan gado babu kaya jikinshi kafafunshi cikin blanket waya ne hannun shi yana magana kaman mai jin bacci idanuwanshi lumshe,
“Baby I can’t wait…” Ya fada cikin whisper, daga Chan bangaren mufi dake kwance sanye da kayan bacci ta danyi Dariya tare dacewa
“Can’t wait for what?..” Ta tambayeshi, shima murmushi yayi yana kallon erection dinshi yace
“Nothing.. Kawai am eager to be with you…. Gani nake kaman 24 days din nan tamkar 24 months or year…” Idanuwa itama mufi ta lumshe saboda maganar shi ke yawo straight into her system, mika tayi Sannan tace
“Nikam kaman gobe nake ganin 24 days…” Yazid Dan kwantawa yayi yana cewa
“Don baki damu dani kaman yanda NA damu da ke ba…amma ni I feel rike in tariyo time din…”
“Don’t worry… Kaman gobe ne…” Ta fada mashi cikin sanyin murya,
“Hmmm alright… I have been patient for a while.. So 24 days won’t matter…” Ya fada ahankali,
“That’s my love… Shiyasa nake kara sonka….$” Dariya yayi
“Da gaske? Tell me why…” Yafada cikin whisper,