NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Cos you are gentle…” Dariyan kasan makoshi yayi

“Hmmm baby am not that gentle… I don’t want to disappoint you… On our first night…” Ya fada kasa2 yanda ki NA kusa dashi bazaiji abinda yake cewa, kuka karya mufi ta farayi tana cewa

“Ka bar fadan hakan…kana tadamin hankali…” Dariya yayi

“Name…Kawai am telling you kar ki daukine gentle don I might be bad ass…”

“I know you are not…”

“To shikenan…I will try to be gentle as I look…” Yayi assuring dinta, hira suka cigaba dayi for sometime Sannan sukayi sallama, Ahankali ya ajiye wayan, ana kallon joystick dinshi, tunani yake wai haka maza ke ji in suna magana da mata ko matsala gareshi din mostly in har zasuyi waya yana jin muryanta cikin kunnenshi sai ya samu erection, shidai gurinshi yayi aure ko ya huta da wannan matsalan.

Ahankali ya mike ya shiga bathroom ya sakar wa kanshi ruwa Sannan ya dawo ya shiga blanket ya rufe kanshi from head to toe.

The following day tun da wuri dija ta addabi ammi suka kama hanyan gidan kanin marigayin babanta wato kawo nanu

Sallama sukayi ita da ammi suka shiga ba tare da an wani amsa masu ba don ana ganin kaman roko ya kawo su kaman yanda suke zuwa wasu lokuttan in abubuwa suka kakare masu, mutumin dake zaune yana wanke bakinshi da asuwaki ya kallesu

“lafiya tun dugudugu?…” Mutumin ya tambayesu, dija data nufi wurin shi tace

“lafiya lau…INA kwana…” Ta gaidashi tana durkusawa,

“Lafiya…” Ya amsa mata atakaice, ita ammi dakunan Matan gidan ta shiga tana gaidasu suna amsa mata atakaice wata ma Bata amsa ba Sannan ta nufi inda dija ke tsaye gefen kawunta, itama durkusawa tayi ta gaida nanu dake yi mata kallon wulakanci Kuma ba komai ya haddasa hakan ba illa yaso ya aureta bayan mutuwan babansu dija amma taki sai ya tsaneta

“Lafiya…wai me akayi ne?..” Ya tambayeta yana goge hakoranshi, ahankali ammi ta fara fadamashi abinda ke tafe dasu, sai da ta kai karshe Sannan ya kalli dija dake tsaye tana sauraron su

“Ke haka ne?…” Ya tambayeta

“Eh kawu…” Ta amsa mashi cikin sanyin murya

“To shikenan.. Allah ya bada saa…” Ya fadawa dija don ko kadan bayason magana da ammi,

“Yauwa kawu Ameen…mun gode.,..” Ta fada cikin murna sosai Wanda ko kadan Bata Iya boyewa,

“Ammi mu tafi…” Ta fada tana barin wurin da Sauri, itama ammi ta bi bayanta tana tafiya ahankali kawu nanu ya bi bayanta da kallo yana cewa

“Ga mace har mace amma ta bar dukiyanta suna wulakanta babu mai kula dasu…yanzu da ina nan ina morewa amma ta yi min bakin ciki…” Ya fada tare da Jan tsoki, ammi fita tayi Bata kar bin ta kan Matan gidan ba don su har yanzu kishi sukeji suna ganin kaman tana iya amincewa mijin su ya aureta don ta fisu komai da komai,

Dija NA tsaye waje tana jiran fitowan ammi tana fitowa dija tayi saurin cewa.

“Ammi ki bani kudin abun hawa in tafi daura in fada mata kun amince…” Hararanta ammi tayi ta wuceta Bata tanka mata ba, har suka kai.gida dija Bata bar fada mata ta Bata kudi ta tafi daura ba, saida ammi taga zata sha mata kai Sannan ta fada mata Hajiya Aisha zata dawo anjuma, sai lokacin dija ta sake ta fita ta fara gayawa kawayenta zata birni, da sun tambayeta katsina zata? Sai tace

“Kambu ni na wuce katsina.. Kano zani…” Duk saida tabi kusan dukkan gidajen kauyen su ta fada masu zata birni

Ammi kam tunanin yanda dija Bata damu dasu ba Kawai take don ko kadan ta nuna bazatyi missing dinsu ba, sai kuma ta tuna da yarinta ke damunta. Dija wanke faded clothes dinta tayi ta shanya su ko abinci bataci ba, ammi kallonta tayi

“Ke baki ma tunanin halin da zamu shiga in kin tafi…kinsan bamu da komai gidan nan..Kuma da tallan nan muke ci, gashi zaki tafi…” Dija Dan Bata rai tayi Sannan tace

“ammi ki bawa binto ta saida mana…” Hararanta ammi tayi

“Amma baki da hankali… Wannan yarinyan zan bawa tallan fura?…”

“Yo ammi ni ai ban kai ta ba NA fara tallan awara..to ki yi mata awara ta dinga kaiwa tasha….” Ta fada in  I don’t care manner, ji take kaman ta kira Hajiyan ta zo ta dauketa.

Sai bayan sallan asar Hajiya Aisha tazo, alokacin kam dija har ta fidda ranta zatazo ita Kuma ammi tana ta aduan Allah yasa kar tazo sai gata da sallama ta shiga cikin gidan da gudu dija ta rungume ta tana cewa

“Sun yarda..sun yarda…” Ta dinga fada tana rike da Matan, itama Hajiyan riketa tayi tana cewa

“Da gaske?…” Kai akwai dija ke ta daga mata cikin jindadi, Hajiya kam tamkar Tasan halin da suke ciki, kallon ammi dake zaune tana murmushi tana aduan Allah yasa aso yarta tamkar yanda Hajiya Aisha ke son dija.

“Kisa yara su biyoni…” Ta fada mata tana fita, da Sauri su dija da sauran yan gidan suka bi bayanta, bayan motanta ta bude sai ga shinkafa da mai da magi sai su taliya katon da macaroni. Ihu su dija suka fara Sannan suka fara shigowa da kayan da Sauri ammi ta mike tsaye tana kallon su. Nan ta zube kasa tana godewa Hajiya Aisha.

Bayan sun zauna ammi take shaida mata sun yarda ta tafi da dija

“don Allah kisa a kula daita…Dan Allah kisa su dauketa tamkar su suka haifeta…” Inji ammi dake hawaye, kafadarta Hajiya ta dafa Sannan tace

” ki kwantar da hankalin ki…yaran da na kai gidan aikatau sunfi su ashirin Kuma baa taba samu matsala ba…kullum iyayensu cikin gode min suke saboda yanda rayuwan yaransu ya chanza…don haka ki kwantar da hankalin ki…” Kai ammi ta gyada mata. Sannan suka tashi tafiya dija ta dauko old Ghana most go dinta, Dariya Hajiya tayi tana cewa

“Ki bude wannan bag din in gani…” Dan dija ta baje kayanta, banda Dariya babu abinda Hajiya takeyi,

“Kawai ki bar wayan nan..in munje daura sai in Dan samo maki.kaya kafin in kaiki…” Tsalle Kawai tayi ta fita ta tsaya jikin motan tana kallon yan kauyen su da suka taru jikin motan suna kallon ta, Hajiya fitowa tayi ta bude motan dija ta shiga Sannan suka tafi.

[3:14PM, 3/20/2018] 鈥�+234 806 125 0020鈥�: 鉂ゐ煉氿煉滒煐ゐ煉欚煉�

NA CUCE TA

馃挏馃挋馃挍馃枻馃挌鉂�

庐zuwairat(ummu Maryam

6鈨�

Dija ko kallon mutanen batayiba balle ta daga masu hannu kaman yanda suke daga mata hannu, ammi dake kuka Kawai take kallo tana tausaya mata amma in ta tuna yanzu basu da matsalan abinci sai ta samu nutsuwa, har suka iso cikin garin daura Bata ce uffan ba, Hajiya kallon ta tayi taga yanda tayi sanyi farat daya ta saki murmushi tare dacewa

“Lafiya dai ko?…” Ta tambayeta cikin muryan dake kwantar da hankalin mai sauraro, dija daga idanuwa tayi ta kalleta

“Babu komai…” Ta fada muryan ta NA rawa, tunanin yanda komai zai kasance Kawai take, tunda take Bata taba kwana wani wajen ba sai in sun je kauyen ammi.dake bauchi shima tare suke zuwa Kuma su dawo tare, Kawai sai taji Kuma batason tafiyan. Ana kiran magrib suka shiga gidan Hajiya tayi parking motanta suka fito daidai lokacin da wasu yanmata biyu suka fito daga falonta, daya babba ce sai daya kaman dija, dukkan su sanye da kaya ta alfarma, dija kallon su tayi ta fara tunanin ya akayi ita bata tura yaranta aikatau ba sai ta tuna Ashe su masu kudi ne Kuma ita talakace, gaidasu tayi suka shiga cikin falon. Jikinta sai rawa yake don she feels so out of place, yanmatan sai kallon ta kawai suke, Hajiya zama tayi ta dauki wayanta ta kira number yayan Hajiya karama ta shaida mata ta samu yar aikin da suke bukata Kuma ta fada mata zata shigo mata daita gobe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button