NA-CUCE-TA COMPLETE HAUSA NOVEL

“To shikenan.. Allah ya kaimu..” Inji yayar Hajiya karama. Sallama sukayi Sannan Hajiya Aisha ta kalli yarta dake zaune kusa daita tana kallon dija

“BaBy zaki aramin kayanki biyu…zuba uku…” Yarinya Bata rai tayi

“Mom me zakiyi da kayana Kuma?…”

“Zan Bata ne….I promise zan saya maki replacement…” Sai alokacin yarinya ta saki fuskarta, kallon dija data sadda kai kasa tayi Sannan ta kwalawa nata mai aikin kira, nan wata babban budurwa ta fito, dija kallon ta tayi

“Tabdin…wallahi bai kaiwa kaman wannan, ina yar aiki…” Ta fada cikin ranta, y

Mai aikin durkusawa tayi ta gaida Hajiya ta amsa Sannan Hajiya tace

“Ki kaita dakinki..ki Bata abinci taci ta koshi Sannan Dan Allah ki duba kanta in yana bukanta gyara ki wanke mata kisata ta wanke bakinta ta wanke koina NA jikinta zan kawo kaya yanzu…..” Hajiya ta fadawa mai aikinta,

“To …” Kawai yarinya tace Sannan tayiwa dija alaman tazo, da Sauri ta mike ta nufi wajen yarinyan sukayi dakinta, dija bude bakinta tayi tana kallon dakin mai aikin,

“Kam Allah kasa nima a bani kaman quartan wannan dakin Dana haye…” Ta fada cikin ranta.

“Ki zauna…” Yarinyan ta fada mata tare da nuna mata katifan dake kasa, da Sauri dija ta zauna ita Kuma ta fita daga dakin, few minutes later ta dawo da jelof din taliya dayasha kayan miya,

“Wow dadi…Allah yasa inda zaa kaini su dinga cin irin wannan…” Ta saki fada cikin ranta tana aman abun daga hannun ta, nan dija ta apkawa abincin ta cinye tas ta tside kwano Sannan ta ajiye, yarinyan dauke kwanon tayi ta kai kitchen Sannan ta dawo,

“Bude kanki in gani…” Yarinyan ta fadawa dija, da Sauri dija ta bude kanta, kitson kanta yafi wata daya dayi Sannan kanta dilindilin,

“Kambu..da akwai aiki…” Inji mai aikin Hajiya Aisha,

Da Sauri ta fita daga dakin ta fadawa Hajiya Aisha status din kan dija,

“Kina da sauran relaxer?…” Hajiya ta tambayeta,

“Eh …”

“To ki shafa mata kan..don gaskiya bazan kaita a haka ba tunda manyan mutane ne…” Ta fada,  nan mai aikin ta koma  ta bawa dija tsinke ta shigar daita bathroom dinta

“Ki tsaya nan ki kwance kanki..in kin gama kiyi min magana…” Ta fada mata Sannan ta fita ta barta nan tsaye, dija kam tsaya kallon bathroom din tayi tana gani ya ninka dakin su kyau sau goma, dukda babu wasu kayan wanka cikin bathroom din amma tiles din wurin Kawai ya isheta kallo,  da Sauri ta kwance kanta dake gari bisa jikinta daman Zane ne guda six amma ki tsaganta baka ganin saboda tsufa. Lekawa tayi ta kalli mai aikin

“NA gama…” Ta fada mata, budurwa mikewa tayi ta dauki sauran relaxer ta shiga bathroom din, nan ta umarceta data durkusa Sannan ta fara shafa mata, tana shafa wa tana mamakin irin gashin dija, don Bata San dunkule yake ba saida ta fara shafa man, tafi minti talatin tana shafa mata,

“Lallai.. Kina da tsawon gashi…” Ta fada, dija dake neman kuka saboda zafin relaxer tace

“Yanke min ammi take saboda tsawo…” Ta amsa mata muryan ta na rawa, few minutes da gamawa dija ta fara yarfe hannuwanta tana cewa

“Ki cireshi haka nan…wallahi zafi nake ji…” Yanda tayi maganan yasa ta Dariya, nan ta wanke mata kai tas taga yanda kanta ke silky saboda baki da tsawo,.

“Hmm daman mu yan kauye munfi yan birni komai.. Amma wahala bai sa a gane hakan…” Yar aikin Hajiya Aisha ta fada cikin ranta, saida ta gama ta hada mata ruwan wanka mai dumi, dija kam jinta take kaman princess,

“Ni ake hadawa ruwan wanka mai dumi…” gari su kam duk sanyi sai dai kayi wank da ruwan sanyi din baka samun ruwan.

“Ki wanke jkinki sau biyar kafin ki fito…kinji?…” Da Sauri dija ta gyada mata kai. Tana fita dija ta cire wet clothes dinta ta fara dirje jikinta kaman mai dilka da sabulu mai kamshi don ita dadin sabulun Kawai take ji, sai adua take Allah yasa da akwai irin wannan hutun inda zaa kaita. Wanke jikinta tayi sosai har in ta saka ruwa jikinta bai zama saboda yanda ta wanke kanta. tsayawa tayi tana kallon kanta kaman yanda ta saba, tafi hour tsaye har saida taji an Dan buga kofan bathroom din Sannan tayi saurin cewa

” na gama….kayanane suka jike…” Ta fada da karfi,

“Ki daura wannan tawul ki fito…” Ta fada mata, dija tsaya kalle2 tayi tana mamakin meye tawul, jin shuru yasa mai aikin cewa

“Wannan farun kyallen zaki daura….” Sai lokacin dija ta gane ta dauko towel ta daura amma sai ta kasa fitowa saboda yanda bai da tsawo,

“Na daura….” Ta fada, kanta kasa sai gasjinta baje kan shoulder ta, budewa mai aikin tayi ta shigo ta zuba mata makilin a brush ta bata ta nuna mata yanda zatayi dashi.

Atakaice nan take dija ta fito kal kaman ba itaba, Hajiya ta shigo mata da wata doguwar Riga yarta ta Bata, ita kanta hajiya sai da ta tsaya tana kallon gashin dija don ba karamin mamaki tayi ba.

Kallon mai aikinta tayi Sannan tace

“Dan Allah ki Bata shawaran da kike bawa sauran in an kawosu kafin In akaisu gidan aikin su…” Inji Hajiya Aisha,

“to…” Ta amsa mata, fita Hajiya tayi dija ta zumbula rigan da aka bata, nan mai aikin Hajiya Aisha ta fara cewa

“Kina jina?…” da Sauri dija ta gyada mata kai,

“NA farko inda zaa kaiki ba gidan Ku bane…gidan aikinki ne…ki tabbatar kina girmama koda akuyan gidan…” Da Sauri dija ta kalleta, itama kallon ta tayi

“Eh din…dole ki girmama su…babu ruwan ki da abinda baa saki ba…duk abinda akace kiyi kiyi…in ance ki bari ki Bari…banda kwadayi…banda zuwa inda baa ce kije ba…banda shisshigi…banda yayata sirrin uwar dakinki ko na wata…babu ruwanki…banda sata…” Again dija kara kallon ta tayi

“Yo kina mamaki ne?…. To da akwai wata yarinya da Hajiya ta kai saida aka maidota wai tana dauk2….don haka ko kudin su zai dinga yawo kasa babu ruwanki don wani lokacin gwadaki suke…kar kiga babu mai kallonki kiyi abinda baace kiyiba…kiji tsoron Allah a duk inda kike…Kuma kar zaman birni yayi maki dadi ki mance inda kika fito…kinji ko?…” Da Sauri dija ta daga mata kai,

“Sannan babu mai son yar aiki kazama…kiyi wankan ki kafin ki fara aikin gida….don haka ki tabbatar kina mikewa da wuri…ki kula da kanki…Kuma in kina da wata matsala ki fadawa uwar dakinki… Mussanman irin matsalan mu na mata…da fatan kinji abinda nake fada maki….” Da Sauri dija ta kara daga mata kai

“Ke ki bar daga kai.kaman wata kadangaruwa…ki dinga amsawa…”

“To …” Dija ta fada, wasu advice ta Kara Bata sosai kan yanda zata zauna da su batare data samu wata matsala ba, dija taji dadi sosai don sai gata tana cewa

“Nagode…” Labari suka cigaba dayi har bacci ya dauki yar aikin Hajiya Aisha ita kam dija yanda ta ga rana haka ta ga dare. Tun da asuba mai aikin Aisha ta tashi tayi wanka itama dija tayi wanka ta maida kayan ta bi bayanta suka fara aiki tana nuna mata abubuwan daya kamata mutum yayi,

“Ai Kwara wannan da dakan fura…” Ta fada cikin ranta,. Kafin bakwai da rabi sun gama komai har mai aikin Aisha ta kusa ida breakfast. Sai karfe takwas Hajiya ta fito ta sha tea da bread su Kuma yaranta sukaci abincin, mai aikinta ta debo abinci ta kai dakinta sukaci da dija Sannan Hajiya Aisha ta kirata ta fito, wata karamar jaka ta bata

“Gashi da akwai kaya kala uku cikin shi…ki kula dasu kafin su kara maki wasu…” Da Sauri dija ta amsa Sannan suka kama hanyan katsina. Gidan yayar Hajiya karama suka isa, nan ma dija baki ta bude don kyau da girman gidan, matar dake kaman daya da Hajiya karama ta kallesu fuskan ta dauke da murmushi tana cewa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button