Uncategorized

WAYAFI SONTA 12


 P12

 “””Inna lillahi wa inna ilaihir raju’un! Yafurta arikice” afili ya furta lallai wannan yarinya tasaida ranta…yah ALLAH kada kabawa bayinka ikon cutar da ita kodan jahadin datayi…. wayarsa tayi ringing!da sauri yad’aga sbd ganin pravate number ,yasan sune! Yanxun kagani da idonka ko?” Shawara yarage naka…muddin ka wuce gobe baka kawo kud’in ba! Zakaga bbu kyau” bamasan ka tsananta bincike sbd Muna bibiyarka……saurara! Kud’i dai kukeso ko?” Yafad’a murya adake! Eh”sumuke so!all right” amma kada kutab’ata ,bata mgn da gske….hhhhhhhhhhh???????? Ina ruwanki da rashin maganarta Kai yadama! maganar mu ta karshe kadena

bincikar alh buba da yaransa dake hannunka kasakesu…kokuwa gobe muje gdnku muda’kko  mahaifiyar ku ,ko wannan yarinyar mae k’wala k’walan idanu!( Elham) dit DSP yakashe wayar had’e da cillar da ita! Jiyake tamkar yanxun yaga me maganar na ,wlh saiya kakkaryasa..

     Wanka yyi yashirya sbd yaje gun Yusuf! cikin bed room d’in hjy yanufa yasameta zaune kan prayer mat tana azkhar! elham na kwance kan cinyarta..Yadubeta yace hjy Dan ALLAH kirage damuwa insha ALLAH zata dawo,yanzunma binkice zanje nayi ! Ina bukatar addu’arki hjy”

   batare data d’ago kaiba tace ALLAH ya taimaka yabada nassara da sa’a!yace ameen,bara natafi…. uncle Wai inane anty zainab ta tafine?” Hjy tace bata saniba , daddy ma haka…Anguwa taje elham” amma very soon zatadawo…bejira cewar elham ba yafice…

 

   ,,,,, Ahankali zainab ta bud’e Idanunta” hawaye na zuba afuskarta! Taganta ankwan ceta…wata mace da fuskarta ke arufe ta mik’o Mata plate d’in wake da shinkafa da ruwa pure wata! tace gashi  kici inbaki ciba to yunwa zata kasheki abanxa,,

Idanunta ta zaro tana furta Inna lillahi wa inna ilaihir raju’un azuciyarta! Meke damunta Wai komai zaifaru da itane??” Tabbas yanxun batajin me matar kecewa ,batajin komai garin yamata dumm! Kewai dan ubanki bazaki cibane? ” Tafad’a tana zarewa zainab Ido… girgiza Kai tayi ta nuna Mata da hannu ta bata biro dake  gaban aljihunta…. harararta tayi had’e da wurgo mata! Zainab tayi rubutu atafin hannunta,ta nunawa matar! Kamar haka…

   NI! bani ji bana mgn” kitaimaka ki nunamun toilet… tab’e Baki matar tayi,kafin ta nuna Mata ita Kuma ta fice dg d’akin…

 

DSP ne da Yusuf zaune sun duk’ufa agaban computers! Sunata dube  dube had’e da binkice.” Sunyi tsit bakajin motsin kowa!

     Can Yusuf yad’ago Kai da sauri yace ogah me  wannan muryar Yana kiranka da wannan number, 09032665220… ayanzun haka me wannan number Yana bila Dede bakin titi…what! BILIYA….Dole na nemoshi duk inda yake maciyin amanar k’asa” butulu ,! DSP yafad’a Yana huci alamar ransa yab’aci” yyi kwafa yace zanbanbace Masa tsakanin aya da tsakkuwa! Laifi 2 kenan naka mashi dashi…kashe computers d’in nan Yusuf muje”…agaggauce sukaje office yatafo da wasu police amma da personal dressing suka nufi bilah!

Rarraba sukayi “kafin DSP yyi calling number d’in biliya da wani layi…biliya yad’aga yace waye… DSP yacanza murya yace ogah kana Ina ?” Lfy daiko? cewar biliya arud’e! Da matsala DSP yafad’a Yana murmushin samun nassara …zaro Ido biliya yyi yace wanene wai…bama wannan ba ,kayi maza kabar inda kake sbd nasami labarin DSP ALIYU na nemanka…. inna lillahi…bejira cewar mutumin ba! Biliya yakashe wayar,yatashi tsaye Yana dubar karuwan dake kuka dashi ,yace inacikin matsala ,kuje zannemeku….bejirabamsarsuba yyi gaba abinshi….DSP kuwa bayan yaga billiya yadatse Kiran,sai yafito da glass nasa bak’i yasaka,yafito da bindiga” gaba d’aya ransa yabasa billiya na cikin garding d’in dake bakin titin…hakan yasa yacewa police3 kowa yyima kansa position! Da sauri billiya yafito…wani mugun faduwa gaban sa,yyi yadafe k’irji had’e da zaro Ido! Yana neman hanyar guduwa… Sbd arba da yyi  da DSP.” da sauri DSP yaharbesa ak’afa…aka sashi mota suka nufi station dashi,Kai tsaye d’akin da yaran alh buba guda2 suke nan DSP yasa aka saka biliya” gaba d’aya biliya bayason kallon abokan aikinsa sbd kamasa da akayi da cin amanar k’asa! Gefe guda Kuma hankalinsa yatashi da ganin yadda kamanin yaran suka koma sbd duka na tuhuma Amma sunki amsa laifinsu…da Kuma k’ in amsa tambayar da akemusu..murya adake DSP ALIYU ya kalli billiya yace tun bansaka ansab’a maka kamanniba muje kafadamun gsky….sbd ance gani ga wane ya ishi wane tsoran ALLAH !

Amma su sun nuna basason tonuwar asirin uban gidansu ,bacin kiddnaping d’in k’anwata da kukayi ya nuna cewa alh buba da yaransa abinda ake zarginsu ya tabbata k’arara..wata k’ofa ce DSP ya kwank’wasa! Wasu maza…k’atti suka fito,idanunsu jawur…biliya yazare Ido sbd yasan sune  masu tuhuma  da duka ne astation d’in….wasu karafa suka fito dasu aka rirrik’e biliya aka cire Masa bullet yanata ihu sbd azaba…kafin DSP yabada umarnin sucigaba da aikinsu na tuhuma!.

Wani k’arfe ne ,aka azawa guda ya matse Masa hannu…yyi k’ara sbd azaba atake akaifar hannunsa ta fita ta yatsa guda ! DSP yace zaku iya sanarmun da tambayata.. girgiza Kai yaron yyi cikin tsabar wahala da fita kamanni yace ah ah…dsp yace acigaba da azabatar dashi…. yyinda billiya ta Kashi ta d’uri ruwa sai raba Ido yakeyi…agaban billiya aka cirewa ko wanne akaifan yatsu 5 ,sbd ihu da gurnani har muryarsu ta dashe… arud’e billiya yace muje wlh Zan Fadi gsky karka saka amun komai… murmushin gefen Baki DSP ALIYU yyi had’e da cewa kataimaki kanka! Kafin yadubi wasu police yace suje wani cell surufe Masa billiya sai bayan isha’i zai dawo…Bayan fitarsu DSP ,yazama a cell d’in saura su 2″ guda da ake Kira auwal cikin nishin azaba yace gsky Ahmed nagaji da wannan wahalar zanfadi inda suke zaune.. in yaso oga yasa akashe iyayanmu dayasa aka kamasu…damacan ALLAH ya rubuta sai sunmutun..in ajalinsu beyiba to Basu mutuwa! Ahmed ya girgiza Kai yace akwai matsala auwal inmuka fad’i gsky! Wlh danasan hakan zaifaru da sbd kud’in makaranta bazan bi haramtacciyar hanya na biyaba,gashi dududu dubu dari5 nasan na amsa aka kamamu ,munashan wannan azabar da uk’ubar! Gashini gdnmu Dani suka dogara….cewar auwal….cikin jigatuwa…

 

Gurin k’arfe 8:30  pm , DSP yashigo office nasa ya kunna tv din da akamasa  saiti da CTV camera….yafara kallo….duk abinda auwal da Ahmed sukayi mgn akanshi yaji…yagano cewa alh buba yakama iyayensu yamusu bara zana da zai  kashe su insuka fad’i gsky…saidai inhar yasami amsa sg bakin biliya zaisa Adena musu uk’uba ,saisu mik’a case d’in kotu kawai sbd da alama wahalar rayuwa d ason abin duniya yasakasu bin hanyar da Alh buba kebi…

Latso cell d’in da alh buba yake yyi” kawai yaga alh buba yafito da waya ,ya matsa can nesa yaduk’ar da kansa Yana mgn ba’ajin me yake cewa…har yagama Yana murmushi…

Arikice DSP yashiga cell d’in da billiya yake…yaganshi kwance matacce… sannan da alama Wanda yyi kisan yasan akwai CTV camera a cell d’in sai suka dakatar da ita saida akayi kisan tukum suka mayar…arikice DSP yatashi da hanzari ya rufe office d’in yanufi cell dain da biliya yake…atake yasami gawar mutum2 dake waje suna tsare da k’ofar cell….dam k’irjinsa yabuga ” inna lillahi wa inna ilaihir raju’un yake ambata ,yadafe Kai ,idanunsa sunyi jajir ,jijiyoyin kansa duk sun tashi!afili yace yah ALLAH ban karayaba Ina ganin biliya shine masssarar mu ,ashe nayi kuskure…atake yace alh buba ne yayi waya da yaransa sukazo suka kashe biliya…ta Yaya suka shigo?” Bacin station d’in da jamaa…. y’allab’ai akwai matsala wlh! Wani police yafad’a Yana sarawa DSP ALIYU! Kallonsa yyi , police din yace muna masallaci jam’in isha’i wlh da yawanmu !shine akayi amfani da b’ata gari suka dauke  wutar Gurin nan Baki d’aya suka shigo suka kashe biliya da wandan nan…yafad’a Yana nuna gawar mutum2 dake kwance….idanu jajir DSP yace duk bakusan aikinku…zanyi bincike akai in commissioner yadawo anjima Amma Dole da saka hannun wasu na station d’in ,sbd ance da d’an gari kanci gari….wucewa DSP yyi arikice yabar station d’in,gaba d’aya yarasa mafita yarasa ta Ina zai Fara…

 

Zainab kuwa ruwa Tasha ta zauna tayi tana kiyasta irin tashin hankalin da su anty mariya da hjy zasuji insukaga bbu ita!saidai ita Bata nadamar zuwanta nan Gurin,sbd tasan manzon ALLAH (S A W) yace ceton ran mutum guda kamar ceton ran mutanan duniyane ,haka kashe ran mutum guda kamar kashe mutanan duniya ne,ita ko ankasheta bazata damuba batada aure ko d’anta ko y’arta…saidai Iyayenta ,tasan zasu damu…Amma inhar ankashe hjy kocin zarafinta ,DSP da sauran familynsu bazasu tab’a jin dad’in wannan aiki na DSP ba,Kuma dg k’arshe yace zai aje aiki sbd abinda akama mahaifiyar sa,mak’iyansa zasuji dad’i sbd dama haka sukeso,duk d’an sandan daya kasance na gari da wuya yatsira da rayuwarsa lfy, awannan zamanin…bud’e k’ofa akayi  da sauri zainab ta rufe Ido tamkar me bacci…wasu Mata suka  shigo da wata mata! bata numfashi suka  kwantar da ita ,guda na nishi tace munci wahala Gurin satota ,inba Dan zamuyi babban samuba ai wlh bazan siyarda Raina Gurin d’akkota ba ga shegen nauyi sbd tanada kiba….guda tace ke Amma ragguwace wlh yoni ko nid’aya ai ina iya d’akkota” uhummm Amma badaga park d’in ba zuwa nan k’arshen gariba ,ga nisa,inake Ina iyawa…kina ganin mutane Basu cika zuwa nan ba ,sai masu hawa kwale kwale sbd ruwanne k’arshen gari! Zaro Ido guda  tayi tace dallah yimana shiru kina mgn sai wani yaji inda muke kijamana matsala… murmushi gudar tayi tace ah ah wazaiji? Wannan yarinyar bataji Bata mgn Kuma naga bacci take… tafad’a suka fice…

 

 

 Ahankali Zainab tabude Ido jin sun fita azuciyarta tace gara Dana nuna banajin me suke cewa ,ta dubi matar  tayi mata k’uri da Ido tana kallo…kawai taji wayar matar na ringing duk basosai akejin k’arar ba…da sauri zainab ta tashi tahau dudduba jikin matar,har wayar ta tsinke….cikin sa’a taganta ga aljihun doguwar rigar matar ta atamfa dake jikinta…jikin zainab na rawa ta dauki wayar ,taga bbu password….da sauri ta sakata silent ta nufi toilet ta shiga ta rufe…

Gurin taxt massage ta shiga ta rubuta sak’o kamar haka….anty nice zainab wannan wayar ta wata matace aka kawo asume shine Basu lurada wayar aguntaba nadauka,naji suna cewa a inda muke k’arshen garine Kuma k’arshen inda muke ruwane ana hawan kwale kwale ko jirgin ruwa in zaa tafi…kisanar da DSP yanzun…dukda darene..Kar Akira wannan number kotura sako zasu iya zuwa su karbe wayar….tana gamawa ta shiga inda zata sending ta rubuta number in anty mariya ta tura Mata ,aka nuna Mata yajiga ,kafin ta goge sakon…

Ta murd’a k’ofar toilet d’in ta lek’o taga bbu kowa ad’akin da sauri t afito ta maida wayar inda ta d’auka a jikin matar….motsi taji da sauri ta matsa tana addua azuciyarta,gefe guda Kuma gabanta na faduwa…

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

[9/28, 9:09 PM] Mmn fareesa: Wannan littafin na kud’ine! dan girman ALLAH inkingani karki karanta ,kar ki turawa kowa..duk Maison siya yakaranta…yaturo Airtel na300 ko MTN  na 300 ta wannan number 08100084251…bamasan transfer d’in Kati,kiyi pic ki turo…ko Kuma kitura kudin 300 ta account number kamar haka..0089110527 suwaiba Hussaini zakirai access bank!saikiyi creen shot ki turo shaidar kin biya….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button