NI DA DR. SADEEQ Book 1, page 23-24
🅿️23&24
……d’auke kanta tayi da sauri ta fice dg d’akin”hindatu na murmushi tace”.baby bazaki zo ki gaishe da yayan ba?”tab’e baki dr sadeeq yayi beyi mgn ba yana dai mamakin girman yarinyar acikin one month”shifa Inda ba anan bane k’ilan bazai gane taba”itace d’azun yagani tana bacci kenan….yaya muje kaci abincin”hindatu ta katse masa tunani”
Oh yah rabbi!kodai magani kika zuban acikin ne baby?”dg hindatu har ammi murmushi sukayi”
muje naje naci abincin”yafad’a yana yin gaba”da ido ammi tayiwa hindatu alamar karta sanar masa fara samun lafiyarta nada alak’a da Aysha”
dato kawai hindatu ta amsa ta fita”sbd tasan muddin tasanar masa tofa zai hana”
Dr sadeeq na zaune kan kujera cikin nishad’i”hindatu najansa da fira ta zuba masa komai yafara ci….
kat yayiwa cikinsa yana kallon ta yace”.baby girkin yayi d’ad’i”suleiman nakwasar dad’i (mijinta)musammun kinga meat pie d’in da kunun ayar sunyi dad’i fa”a ajiyemun dambun naman anjima zanci,yanzun na k’oshi”
tashi tsaye hindatu tayi tana murmushi tace”. yarinyar nan fa ce duk tayi meat pie d’in da kunun ayar”
D’aure fuska yayi yace”.dama ina wasa dake”wlh yaya harda dambun naman itace tayi”
tab’e baki yayi yace”.ina ruwana ni da ita”meyati maka yaya?”agabanki taganni ta nuna kamar bata sanni ba”kayi hak’uri dan Allah”kiramun ita nasakata wani aiki ma”
Dato ta amsa tana wucewa”shikuma yabar gurin”
Aysha na d’akin hindatu nada(time d’in datake gida)tagama sallar la’asar”tana sanye da hijab nata iya gwiwa”tanaso ta wuce gida”k’asan ranta tana ganin bata kyautaba dabata gaisheda dr sadeeq ba”
Baby kina nan dama?”d’ago kanta tayi tace”. Eh sallah nayi”okay kije inji yaya”zaro ido Aysha tayi”lafiya daiko?”dan Allah banmasa laifi bako?”
meyasa d’azun baki gaishesa ba?”nida bansan da zuwansaba”damafa shine zaizo mukayi girki”
d’an shiru Aysha tayi gabanta nata fad’uwa”kije yana parlourn sa”dato kawai ta amsa hindatu ta fita.
yadawo fa zaizo yafara takurawa rayuwata ko? tafad’a tana turo baki ta tashi ta fita”
Kasancewar dama tuni hindatu ta tab’a nuna mata sashensa”hakan yasa ta nufi can”
Tura k’ofar parlourn tayi”k’amshin turarensa yacika parlourn”yana zaune yana waya da dr habib”
sallama tayi ta duk’a kan carpet ta durk’usa nesa dashi”tayi duk’iyar minti 3 kafin yakashe wayar yana kallon TV”
Ina wuni?andawo lafiya?”tafad’a ahankali batare data kallesaba”
bazan amsaba ki rik’e abinki”ina cewa d’azun kinganni ido da ido”amma ban isheki kalloba”sbd ke kin girma ko?”
turo baki tayi tace”.amma yaya sadeeq tunda katafi katab’a tambayar koda lafiyata?”bayan kuma kaine sanadin zuwana anan gidan….sannan ni bansan zakazo ba”
Okay tuhumata kikeyi kenan?”shiru tayi batace komaiba”
kitashi idan kingama turo bakin kije ki shiryamun kayana suna a troley”
Dato ta amsa tana mik’ewa tsaye”ta nufi k’ofar data gani”tana bud’ewa tashiga ciki.ashe gurin dayakeyin exercise ne”
sarai yaganta ta shiga amma yak’i mata mgn”fitowa tayi ta tura d’ayar k’ofar”anan tagane nan ne bed room d’in sa”barin k’ofar bud’e tayi”
Tafi 30 minit tana shirya masa kayan”bayan ta idar tafito”
satar kallon sa tayi,aikuwa suka had’a ido”amma be hararetaba yadai d’auke kansa da sauri”tana k’okarin mgn wayarta nokia tayi ringing”
Dama tasan anty ke kiranta”assalamu alaikum”ah ah anty yanzun dai zan tafi”ko ki bari sai gobe anty naga marece yayi karmuyi dare”
Duk surutun datakeyi gogan na saurarenta”amma idan zaka kallesa saika zata besan miye takeyiba”
yaya sadeeq nagama zanje gida”shine nace gobe zanzo nan ko asibitin zanje?”
miye zakiyi anan d’in?”asibiti zakije”dan Allah zan biyo koda safe nagaishe da ammin saina wuce”
sosai yaji ta burgesa data kula da mahaifiyarsa”okay bbu damuwa”
tayi mamakin jin kalmar”tunda tasanshi betaba mata mgn bbu hantara da tsawaba”
Ke nawane zan biyaki?”yaya sadeeq kadinga kirana da sunana dan Allah”tafad’a cikin marairaice murya”tab’e baki yayi yace” bazan iya fad’in duk me wannan sunan ba”shikenan amma kasandai ke ba suna bane?”bansani ba ki bani amsata.
kamanta ka bani kud’in wata kafin katafi”
Kenifa anan zamanki nake nufi”bbu komai dazaka bani”mutuntawar da akamun da karramawar da ammi da anty hindatu sukamun yayi basaika biyani komai ba.
Tana fad’in hakan bata jira amsar shiba tafice dg parlourn”
Shiru dr sadeeq yayi yana jin bata tab’a burgesa yarinyar ba irin yau”haushin ta nabata gaishesaba dakeji sai yadena ji”
Motsin shigowar hindatu yadawo dashi tunaninsa”yaya sannu da hutawa”yauwa”kasan wani abu?”ah ah”gsky yaya yarinyar nan tanada kirki”kaga yadda take kulawa da ammi?”
wai da gske kikeyi?”Eh mana”kice ke bakida amfani kenan?”bafa haka bane yaya”wani time d’in zanyiwa ammi abu”sai tace”. itace zatayi”akwai time d’in da har kuka tayi sbd tausayin ammi”
Aidama saurin kukane da ita”
yanzun ma dazata tafi tace”. gobe insha Allah zatazo tagaishe da ammin”Allah yakaimun”yafad’a cikin k’osawa “yazancen wannan mutumin?wai mijin ammi?”
kinsani kike tambaya”nifa yaya wlh mutumin nan ban amince dashiba”kusan sati 5 kenan rabonsa da gidan nan”
wani murmushi dr sadeeq yayi yace”.okay yyi kyau”zanfita baby”
yaya ni yaushe zankoma gidana pls?”kasan mazan yanzun kar wata ta janyemun hankalin miji”
Had’e rai yayi yace”.dashi da mahaifiyarki wakika zab’a?”karki manta yana k’arin karatu”saura wata 2 yagama ai”Allah yakaimu yagaman”
yana fad’in hakan ya wuce ciki sbd ya canza kayansa yafita.
Aysha na isowa anguwarsu "tasami baffa da wani mutum k'ato tsaye k'ofar gidan suna mgn"ina wuninku?"
Da sauri Alh nura yakalli Aysha bbu ko k’iftawa”batare daya amsa gaisuwartaba”ita kuma ta wuce ciki kawai batayi mgn ba”
Mlm idi wacece wannan?”itace wacce nake gayamaka ai”
yanzun kanada wannan amma ka zauna a talauci?”kuma kai gashi abinda ka kamana yak’iyi balle mubaka sallama”
Amma yanzun indai zaka bani yarinyar nan naje na kwana2 da ita wlh 500k zan baka”
zaro ido baffa idi yayi yace”.da gske Alh nura?wlh kuwa”indai ta yarda dani”kamar yaushe kakeso?”
Ko yanzun ashirye nake”okay kafara zuwa tad’i dai sannu ahankali kamar na sati1″ sannan saina sakata tabika”amma farat d’aya zatayi gaddama”
Dg haka sukayi sallama baffa ya wuce gida yana murna.
washe gari da safe”Aysha na gama sallar asuba ta zauna tayi rubutunta a allo ta wanke”sannan ta juye afarar leda ta d’aure.
Bayan tagama shiryawa tafito”Abdul na k’ok’arin tafiya saman adaidaita”
yana ganinta yatsaya yana murmushi”yanata kallonta yace”.kwana 2 Aysha ina kikaje nadena ganinki?”inanan fa yaya abdul”ina kwana?lfy qlau”
masha Allah kin canza sosai da alama matsalarki tayi sauk’i”
Batace komaiba tayi dai murmushin”hakan yyi daidai da driver d’in gidansu dr sadeeq ya iso”
sai anjima zan tafi”ina zakije ?”yafad’a yana kallonta”gun aiki”dg haka tanufi gun motar”
sosai gaban abdul yafad’i”beson yayiwa y’ar mutane mummunar fahimta”Allah dai yasa ba wata hanya Aysha tabiba”yafad’a cikin damuwa yaja nafef nasa ya wuce”
Aysha na isowa suka gaisa dasu ammi tabawa hindatu rubutun”bbu yadda hindatu batayi da ita akan ta tsaya tayi break fast ba”
amma sbd kar dr sadeeq yace”.tayi latti tace musu ta k’oshi.
Asaman adaidaita ta tafi asibitin”saidai koda ta iso office nashi rufe yake”kuma da personal drees tazo”
zama tayi kan kujerun wajen”murtala ya iso yana jawo table nasa”