Ni da Dr. Sadeeq

NI DA DR. SADEEQ Book 1, page 5&6

BOOK ONE 📖

Story & written by
Mommyn fareesa

🅿️ 5&6

Arikice Aysha ta k’wallah razananniyar k’ara”gabanta na wani irin mugun bugawa”

Taheer yasaki wani shu’umin murmushi yana k’ok’arin keta mata doguwar rigar atamfar jikinta”wacce tayi k’uda sosai…

Aysha sbd tsabar tashin hankali tama rasa mafita”tana k’ok’arin ture hannunsa guda daya toshe mata baki”

Hakan yayi daidai da karasowar anty murja tana jijjiga k’ofar”shigowarta gidan kenan”

cikin fad’uwar gaba taheer yyi saurin cika Aysha yana cewa”ke wlh kika sanar mata da wani abu”rufemun ke zansaka police suyi….Aysha kina ina wai?”kizo ki bud’emun mana”

cewar anty murja tanajin fad’uwar gaba”tana tunanin kodai da matsala ne?”

Aysha na kuka ta d’auki hijab nata”taheer yayi saurin barin parlourn ya wuce d’akin da zainab keta kuka ya d’auketa”

Aysha na bud’e k’ofar suka had’a ido da anty murja”gabanta nata fad’uwa ta kalli Aysha ayamutse ga kuka tanayi”idanuwa ajawur da gefen fuskarta”sbd marin da taheer yamata.

Lafiya meke damunki Aysha??”ina zainab d’in?”kuka Aysha tasaka tak’i mgn tana k’ok’arin rab’awa ta wuce ta gefen antyn.

Antyn ta rik’eta tana kallonta tace”.bakiji menace miki ba?”kifad’amun mana”ina zainab?”

zaman wannan y’ar iskar yarinyar yak’are agidan nan”tanacan tana barci tabarmun yarinya tana kuka kamar zata shid’e”

Cewar taheer abayansu yana rik’e da zainab dake kuka”yawani d’aure fuska kamar gaske”

anty ta kallesa ta amshi zainab tana cewa” Aysha barinman yarinya kikayi tanata kuka?”

Tsaki taheer yaja yace”.dole tayi kuka sbd namareta akan cutarmun y’a datayi”

Ki wuce ke kuma kimata wanka kotayi bacci”batun raino na hana dg yau”

yana fad’in hakan yajuya yabar parlourn”yyinda Aysha kanta ak’asa batace komaiba hawaye nabin kuncin ta.

Aranta tana godewa Allah daya kawo mata d’auki”ba’a rabata da martabarta ba.

Anty na k’ok’arin mgn”Aysha ta juya aguje tana kuka ta fita”ko takalminta bata koma ta d’auka ba.

Anty murja kuwa ta kasa yarda da abinda taheer yasanar mata”

Tasha alwashin da safe zataje gidansu Aysha ta tsareta tamata bayanin meke faruwa kawai….

Aysha na fitowa tasamu inwa ta zauna tanata kuka….. k’arar mota taji agabanta”

Tana d’ago kanta taga wasu matane ke sauka dg cikin nafef”

Ashe abdul ne yasaukesu”kuma yahango wata kamar Aysha”hakan yasa ya Ida nufota”

Adaidai Inda take zaune yayi parking”sake d’ago kanta tayi suka had’a”

Da sauri tayi k’asa da kanta”fitowa yayi dg cikin nafef d’in”yana atsaye yana kallonta yace”.Aysha meye kikeyi anan ?gashi kina kuka kuma”

babu komai gida zanje”to tashi muje nakaiki”zanje dakaina”

shiru yayi yana k’are mata kallo yace”.garin yaya hijab naki ta kece?”kuma ina takalmin ki?”

kuka tasake fashewa dashi tace”.nidai ka k’yaleni”

d’an Jim yayi”sai kuma yace”. taso muje nakaiki gida”batace komaiba ta taso tashige cikin nafef d’in”

Abakin wani shago na siyar da takalmi yayi parking”

wane size kike sakawa?”35″tafad’a Ahankali”fita yyi yaje yasiyo mata”bayan yashigo yaturo ledar takalmin”nagode k’warai ta fad’a tana amsa.

gurin masu d’inka hijab yawuce”Aysha na kallon gurin tace”.dan Allah yaya abdul kabarshi haka”takalmin ma nagode wlh”

Bece komaiba yasauka yanufi gurinsu”bejimaba yadawo da hijab acikin leda sabuwa dal”d’inkin zamani”

gashi ki canza data jikinki sai muje nakaiki gida.yafada yana tsaye yamik’a mata”

ganin dama ta jikinta kawai gareta”kuma taji jiki itama”saita amsa tanata masa godiya”

shiga ciki yayi yaja motar”meye kikeso nasiya miki?”babu komai wlh”hakanma nagode k’warai yaya abdul”

babu godiya tsakaninmu Aysha”ina tausayin rayuwar dakikeyi agidan baffanki”Allah yakamiki k’arshen abin”

Ta amsa da amin”tana saka hijab d’in”sannan ta zare wacce take ajikinta ya gaggar”

suna shigowa farkon layin tace”.asauketa”beyi mgn ba yasauketa”tafita dg ciki tana masa godiya”

yatafi cike da tausayinta”

Asoro tasami fiddausi zaune kan tabarma”awara da lemo fenta agabanta da yaji tanaci”tana latsa wayarta me malatsai”ko kallo Aysha bata isheta ba.

ciki Aysha ta wuce batacewa fiddausi komai ba”

D’akin da ake ajiye shirgin kaya”anan ta wuce taje tayi alwalah tayi sallar azahar”

ga yunwa na k’wak’ularta tayi tagumi tana tina irin gatan datake samu agun mahaifinta abaya….


washe gari da safe gurin k’arfe 7:45 am Aysha na kwance ad’akin”kan y’ar yololuwar tabarma taji sallamar anty murja”

baffa idi be gidan tun asuba yafita”fiddausi kuwa bama agida ta kwana ba”tanacan yawonta gun mazan banza.

Goggo sa’a na d’akinta tana baccinta”hankalinta kwance”

tashi tsaye Aysha tayi tana dafe cikinta dake ciwo sbd yunwa”

Fitowa tayi tana amsa sallamar anty murja tace”.lah anty shigo dan Allah”

shigowa cikin d’akin tayi”sbd ganin babu dad’i ta nuna k’yamatar d’akin yasaka tace”.Aysha muje soro mgn zamuyi”

Dato ta amsa tasaka hijab nata suka fito asoro”dama soron nada girma”

kujera y’ar tsugunne ta ajiye mata”ita kuma ta zauna kan siminti”

Bayan gama gaisawa anty ta kalleta bbu wasa afuskarta tace”.

Aysha dan Allah banisan kimun k’arya”kifad’amun gsky tsakanin ki da Allah meya faru jiya naganki awannan yanayin??”

Aysha namatsar k’wallah tashiga sanar mata da abinda yafaru tsakanin ta da taheer”

Ajiyar zuciya anty murja tasaki tace”.na yarda Aysha”sbd kece me raino ta 2 dakika sanar mun haka”amma zanbar taheer da halinsa “wataran zan kamashi dumu dumu”sannan nad’auki mataki”amma kiyi hak’uri kinji bazaki koma zuwa gidan ba.

Amma yanzun anty bansan yazanyiba?”kingadai halin danake ciki”yanzun rabona da abinci tun jiya wlh”yanzun zama gidanma fitinane aguna”

yanzun sai kiga baffa yadawo yace”.dubu kaza yakeso nakamishi”

Aysha kin riga kin b’ata komai agun yiwa dr sadeeq rashin kunya”

ko jiya dana baro asibitin naji za’a d’auki sabbin cleaners”da baki masa rashin kunyaba saina kai sunanki”

wlh zaki samu alkhairi”kullum muna tare zan dinga biyanki nabaki zainab raino”sannan abaki albashinki na aiki acan”

Abinda nasani abaya ana bawa cleaner albashi awata 25k ne”k’ilan yanzun yakai 30k”

Dan Allah anty muje yanzun nabashi hak’uri”tafad’a tana kuka”

Hmmm bakisan waye dr sadeeq ba”duka asibitin shakkarsa akeyi wlh”

Laifi kad’an ko kuskure kayi sai a koreka”ina gudun kada muje nikuma yakoreni.

Anty insha Allah bazai korekiba”muje k’ilan adace”idan be hak’ura ba”saina dawo na nemi wani abu”ko kuwa na gudu nakoma gun dangin mahaifiyata.

sosai taji yarinyar tabata tsausayi”ta tabbatar dan Allah zatayi”idanma yahad’a da ita yakora saita nemi aikin awani guri”

sbd tasan dr sadeeq beson shishshigi da katsalandan”yanada kafiya,kuma besan raini.

wata leda ta fiddo dg cikin hand bag nata tace”.ungo kici sai muje”hannu na kirma ta amsa”

dankali ne da k’wai aciki”bara na wanko baki dan Allah anty”

dato ta amsa Aysha tabar soron”bbu jumawa tadawo ta zauna agabanta ta cinye tas”

Ciki ta koma ta wanke hannunta ta sanya sabbin takalminta da hijab ta fito.

suna fitowa suka hau adaidaita suka nufi A&A INTERNATIONAL HOSPITAL”

gaban Aysha nata dukan tara tara”takasance cikin k’ila wa k’ala”akoreta ko a d’auketa aikin”

suna fitowa dg nafef suka wuce cikin asibitin”abakin office d’in dr sadeeq suka tsaya”anty na kallon Aysha tace”.zauna nabaki zainab saina shiga ciki wajensa”

dato ta amsa ta zauna kan kujerun da ake zama bin layin ganin likita”anty tasakko zainab ta mik’awa Aysha “

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button