NI DA DR. SADEEQ Book 1, page 7&8
BOOK ONE 📖
Story & written by
Mommyn fareesa
🅿️7&8
da sallama anty murja tashigo cikin office d’in”dr sadeeq na zaune kan kujera yana danna laptop dake gabansa”kasancewar be fara duba patient ba”
gaba d’aya office d’in k’amshin turarensa yakeyi”
batare daya kalli wanda yashigo ba ya amsa sallamar can k'asan mak'oshi"yana jiran murtala sakatarensa yazo"yaji dalilin dazai bari kowa barkatai yashigo masa office.
Dr barka da safiya”ina kwana?”lfy “ya amsa cikin k’osawa be kuma kalletaba”
dama dan Allah wata bewar Allah nazo ne marma alfarma agunka dr”shiru yayi beyi mgn ba”
cikin kirma tace”.aikin goge goge dan Allah za’a temaka abata”naga jiya an…..kije bbu damuwa idan tazo kikawota”
Ai tare muke da ita”okay anan office nawa kawai zata dinga kulawa da tsaftacewa”ina fatan tanada tsafta?”
eh batada kazanta sunanta Aysha…… what?”yafad’a yana d’ago kansa yajefeta da wani irin kallon dayasaka tayi k’asa da kanta”gabanta na fad’uwa.
wannan yarinyar marar tarbiyya dana ganku da ita a bank jiya kike nufi?”yafad’a cikin cool voice yana tsareta da narkakkun idanuwansa”
Dan Allah dr kayi hak’uri tana cikin wani hal….get out of my office now!
yafad’a atsawace”yana tuna yadda yarinyar nan tadinga gaya masa mgn jiya bata duba girmansaba.
I’m sorry sir!banza yamata yana huci”ta juya ta fita”
tsaki yaja.....sai kuma yamik'e tsaye zumbur sbd wani tunani da yayi"
bud’e k’ofar office d’in yayi yafito….anty murja na fitowa”Aysha ta kalli fuskarta tasan bbu sa’a”
Anty be aminceba ko?”Allah yasa be korekiba”anty murja na k’ok’arin mgn sukaji muryar dr sadeeq abayansu yana cewa ina yarinyar take?”
K’asa da kanta Aysha tayi k’irjin ta nabugawa”bata yadda ta kallo direction d’in dayake ba”
anty murja ta nuna ta tana cewa gata nan dr”
Tabiyoni tafara aikinta”yana fad’in hakan yajuya yashige office nashi”
tashi kije Aysha”amma dan Allah ki kiyaye abinda zaije yadawo”kinga dai mutumin nan yanada murd’ad’d’an hali”
Jikinta na rawa tace”.to anty”kindai bashi hak’uri ko?”wlh ina tsoron kar yadakeni”ke bazai miki komai ba”kije karkiyi laifi”anjima zanzo anan na nuna miki ward d’in danake.
dato Aysha ta amsa jikinta asanyaye ta wuce office d’in”
da sallama tashiga”kanta ak’asa ta jingina jikinta da bango”gabanta nata fad’uwa”
Dr sadeeq yawani had’e rai”fuskarsa bbu rahama ko kad’an”be kuma amsa sallamar taba”
Aysha tayi tsayuwar kusan minti 15″bece mata komai ba.can tad’ago kanta tana yatsina fuska tasaci kallonsa…..caraf suka had’a ido”wata uwar harara ya wurga mata”
dan Allah kafad’amun meye zanyi?”inata tsayuwa kak’i amsa sallamata”kanata hararata mena maka kuma?”
sosai dr d'in yayi mamakin halin yarinyar"amma be nunaba afuska"juyowa yayi yana yatsina fuska yace".da alama bakida tarbiyyar girmama manya ko?"baki iya gaisuwa ba sai rashin kunya"
To bari kiji na d’auke ki aikine sbd nagyara miki tarbiyyar dakika rasa”sannan saina koreki sbd bakida ajin yin aiki nan.
Karki zata tausayinki naji"ah ah"hasalima natsaneki"zan kafa miki dokokina dole kibisu kuma"
kan Aysha ak’asa tana tunanin wane irin mugun mutum ne wannan?”cikin rawar murya tace”. zanbi kowane sharad’ine indai bazaka koreniba”
Tsaki yaja yace”. k’arfe 7:am tamiki a office nawa”ki gyaramun ko ina na ciki”ki kuma goge bakin area d’in office nawa”
arana sau 3 zaki gyara"idan kinzo 7:am sai 2pm time d'in tashinki yayi"idan kuma zanjima anan kema dole kijima anan"
banason kallo da shishshigi”and last one shine dole idan nashigo kiduk’a har k’asa ki gaisheni”sannan kuma idan nakiraki saikin duk’a inkinzo”mgn idan zakimun aladabce zakimun”ko kuwa ranki yayi mugun b’aci”stupid girl kawai….
nifa gsky inada tarbiyya ta”abinda kamana ajiya kasan kashiga hakk’in mu..monzon Allah S A W yace….ke!
ciwon kai kikazo kisamun da surutunki ko aiki kikazo kimun?"
Last warning bansan surutu”kuma kika koma mgn ina mgn zaki sani”
Allah yabaka hak’uri nidai”tsaki yaja yace”.sai d’oyi kikeyi”kitabbatar kinyi wanka gobe kafin kizomun nan”
Uffan Aysha batama ceba”zuciyarta namata zafi akqn rashin mutuncin da ake mata” in bacin mutuwar mahaifinta da zalincin baffanta “akwai wanda ya isa yamata hakan?”
bakijine?”yafad’a cikin tsawa”da sauri ta d’ago kanta tana zaro dara daran idanuwanta farare tas.
Ina jinka dan Allah”okay raini yasaka kikamun banza?”ah ah wlh”ni ban raina kowaba”
bece komaiba yacigaba da abinda yakeyi”ganin yashareta yasaka tadinga k’arewa office d’in kallo”
mik’ewa tsaye yayi yace”.idan kingadama ki gyaramun office d’in ki wanke toilet”nabaki 30 minit zanshiga meeting”
Be jira amsar taba yafice yabar mata k’amshin turarensa”
Tab’e baki Aysha tayi tace”.almasifatu”tana fad’in hakan ta d’auki tsintsiya da faka tashare office d’in”
Toilet ta wuce ta d’akko mopa tayi mopping”sannan ta d’akko wani towel k’arami, ta goge table da fridge d’in dake office d’in da TV”
toilet d’in takoma acanma ta wanke tas”sbd duk tasan yadda ake amfani da komai.
air frishner tagani saman table agefen wasu littattafai”hakan yasa ta je zata d’auka” taga daman wasu kud’i a ajiye gefe”
Tab’e baki tayi ta d’auki air frishner d’in”azuciyarta tace”.ko yana nufin ni barauniya ce zai wani kama ajiye kud’i.
tana cikin fesawa dr sadeeq yashigo cikin office d'in"
Angama y’allabai saime kuma??”ke karki koma kirana da haka”kije kitambayi sunana”
kome mutum yayi laifi ne”tafad’a k’asa k’asa”meye kikace?”turo baki tayi tace”.nima sunana Aysha “
Tsaki yaja yana k’arewa office d’in kallo”yashiga toilet”
Fuskarsa ad’aure yafito yace”.ke wawiyar inace?”dallah tashi kisake wankemun toilet”kihad’a da tiles na jikin bango”
wlh Allah nagaji”kabari sai anjima”ba hutu kikazo yimun anan ba”aiki kikazo yi sbd haka idan bazakiyiba kibari”
Amma idan kika wuce 2 minit bakije ba”bakin aikinki “dan Allah kayi hak’uri”tafad’a hawaye na zubo mata afuska”
Ke get out of my office now! yafad’a azabure kamar zai daketa.
Aguje tabar office d’in tana kuka”yaja doguwar tsuka yaja kujera yazauna.
Aysha na fitowa suka bangaji juna da dr habib dazai shiga office d’in”
D’ago kanta tayi suka had’a ido”sosai yakafeta da ido”sbd yatuna yarinyar jiyace”
dan Allah kabashi hak’uri yamayar dani aikina”yace nafice masa dg office”
D’an shiru dr habib yayi sbd yasan kafiya irinta abokin nasa”
kinga kiyi hak’uri kidena kuka”zansaka yamaidaki insha Allah”jeki zauna”
yafad’a yana kallon ta”aransa yace”.masha Allah tanada kyau”
wucewa tayi gun kujerun dake wajen”murtala sakatarensa da zuwansa kenan”yakalleta yace”.bewar Allah lafiya daiko?”harararsa tayi tace”.ina ruwanka dani?”tab’e baki yayi bece komaiba.
Dr habib kuwa yana shiga ya ajiye masa wasu files agabansa”
Pls kasaka hannu nayiwa wannan matar aikine”okay dr sadeeq yafad’a”bayan yyi sighning yamik’a masa file d’in”
Amsa yyi kafin yace”.abokina me yarinyar nan keyi anan?”kaga banason tambaya”nace taje tabani waje”tazo tana damuna da mgn”
Cleaner d’ina ce ba wani abu ba”idan sokakeyi kaji”dama kuma na d’auketa ne sbd na azabtar da ita”
Akanme?”bansaniba”amma agabanka jiya tamun rashin kunya ko?”
Amma abokina ai wannan yarinya ce”kacemun fansa zaka d’auka kenan?”amma hak’uri zakayi”naga sai kuka takeyi sbd ka koreta”
haka tace”.maka?ah ah nifa banmata mgn ba”kawai dai naganta can zaune tana kuka”
Tsaki dr sadeeq yayi yace”.ko kukan jini zatayi saita koma wanke toilet d’in nan”
Dariyarsa dr habib yab’oye yace”.kabidai y’ar mutane ahankali gsky”idan nak’i fa?” Ah ah abokina maida wuk’ar”
nizan wuce kadawo da ita bakin aikinta dan Allah”uffan dr sadeeq bece ba”yad’auki talephone yakira murtala”
Katuromun wannan yarinyar dake zaune”dr habib yafice yana dariya aransa yace” zamuyi kallon dramer a asibitin nan kuwa.
murtala yakalli Aysha yace”.both yace”.kije yana kiranki”
batace komaiba sbd haushi taji murtalan nabata sai wani kallonta yakeyi”
Office d’in ta nufa” ta murda k’ofar ta shiga…✍️
Mom fareesa🖊️