AHUMAGGAH 6

_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence_
_6⃣-the few,the proud♡_
Kofar nasa nabi da wani irin razanannen kallo gaba daya naji bana jin dai dai yau ne ranar da nafara iya koyan spelling doom a rayuwa ta .
Da gwiwa na hade kaina cikin damuwa don bayan kukan da naci sosai hankali na yayi matukar tashi.
Ga kafata inda na buga yana min zafi haka dai na mike ina dingisawa har naje site din nana A ko zan xan samo mafita.
Nazo nan ma nayi tambaya akace min wai She is not around.,sai nasa a duba min ita urgent,
gurds ne yace min najira anan maybe tana chan cikin hall din da za’ayi meeting din ne tana inspecting masu shirye shirye .
I waited patiently
Ina ta waige waige dai,Kirji na sai bugu yake ina duban time. 5 minutes more, gurds bai dawo ba kawai sai bi bayan sa.
Tafiya ta kawai nake yi Banga kowa ba sai wata katafaren gate dark brown shima acikin gidan yake
nan na shiga straight zuwa bakin wani daki danaga sojoji anata kaiwa da kawowa
Luckly enough babu wanda yace min cikan ki.
Haka nayi ta ratsa cikin hall din ban ganta ba sai na shiga wani shashi mai fadi da kyau duk an shake shi da kayan duniya.
Wani makeken super huge metal frame pHoto na gani abango wanda ya sani dakatawa ina zuba musu muzurai
Its bold and clear
nagane shi,Lallai wannan mutumin dana taimaka ranar akan hanya shine ajikin hoton
Sai kuma jahan Aarah agefen sa,a gefenta kuma naga wata kyakkwar mace kafin nan naga gogan nawa dukan su suna murmushi.
Murmushin mutumin kawai na kalla sai naji Tuni kyawawan halayen sa yasa ni wondering,toh indai har shine mahaifin wannan mr temper din abun zai bani mamaki,toh meyasa shi yake da saukin kai da taushin hali?
wato ashe har zaka iya haifar da acikin ka kuma halayen sa su banbanta da naka?
Even jahan has neva been rude to me matar akwai yawan murmushi
Toh meyasa shi kuma dansun baida saukin kaine ne? Abu kadan kayi masa zai zafafa masifa Ko dan yaga ni bakomai bace kuma bazan iya sa insa da shi ba
Dan karamin tsaki nayi kamar wacce bata hankalin ta m shiga bambami
I just hate to be mistreated in kashe ni zaiyi kawai ya kashe, amma nikam nagaji da fitinan sa
…ko kadan Bansan na furta hakan a fili ba.
Ji nayi an dafa ni slowly,sai danaji gaba na tayi wani irin Rasss,a bazata na jiyo,sai naga nanah A itama tana duban hoton danake kallo tana murmushi Batare da ta kalle ni ba ta mika hannu tace
Kinga wannan? Tayi nuni da fuskan alhaji hamood mufaddal clive
Sai ma girgiza kai sideways
i knew she heard me sarai,anma ban san me take shiirin yi ba sai nayi shiru ina binta da ido
nan dai ta gaya min matsayin shi a duniya wanda ya dada shuka min ruwan tsoro araina,haka ta dingayi har ta sauko bayani kan blood Sister khaldun sa’ood mai suna SUBAYA,nana A tace min itama tana chan saudi arabia tana zaman aure achan.
Datayi nuni da oga nah sai na dada bada hankali na sosai tace
Zakiji anace mashi KHALDUN but SA’OOD shine asalin Sunan shi.
KHALDUN wani inkiya ce daya gada wajen iyayen shi da kuma wajen yan uwansa ,da awajen aikin sa ma’anan sa yana nuni da mutum ne mai TSAWON RAI.
Jahan Aarah tana matukar kaunar jin kowa yana ce masa khaldun fiye da asalin sunan sa wato sa’ood (ma’ana happiness) duk dama akan iya hade su waje guda,Tare da ma’anan sunan na shi,in an hada KHALDUN SA’OOD yana nufin,.
the ETERNAL HAPINESS wato farin ciki mai daurewa.
Tace min as u can see,khaldun shine dan jahan na farko probably shi ne babban da namiji A gidan nan baki daya.
Sai Ta dan jawo ni kadan dan ban iya wani kyakwan motsi ba, nan ta nuna min wani old black and white theme pics shine ajiki tun yana karami,i keep staring at the pic i can even swear that ban taba ganin kyau kamar nashi ba, i saw him smilling gaban wata katon cake an rubuta happy birthday khaldun sa’ood,
It was his 10th birthday Akwai kuma date ajikin hoton,sai naga daga lokacin zuwa yanzu na fahimce cewa he is just 27years old now
Hnm Nasha mamaki matuka ganin gwarjini da kasaita irin nasa gani nake kamar ko dan 50 yrs ma albarka.
Nanah A bata fasa ba sanda ta ajiye ni da kyau kafin ta gaya min matsayin sa.
Tace min This 27year old khaldun sa’ood,is a bonified marine soldier.
Tace kinsan su waye marine corps?
Na girgiza kaina cikin fargaba fuska ta agwabe kamar zan yi mata kuka nan ta min bayanin su.
‘Tace the USMCs or the marines ko kice royal force, suna daya daga cikin 5 basic military unit a duniya wanda aka kafe shi tun daga depatment of defence 1775 a united state.
In na fahimci nana A ta tana nifin a duka kafafen military force guda biyar da muke dasu a duniya kowanne daga ciki na da naval/marine infantry force unit ajikin sa amma babu tantama marine corps su suke da largest and world most powerful forces and millitary superior regard.
Tace Darajan su yafara ne Tun daga kan training dinsu da ake kira Pt test, marksmanship training and their all round readiness.
Tace min duk duniya suka dai ake iya musu wannan horon, shiyasa ma ko wani marine zai iya rikidewa ya zama kowani irin soja,amma babu wani nau’in soja a duniya da zai iya kwatanta dawo wa dakan sa marine not even their closest acomplice wato naval force.
Nana tace min Suna nan ko ina a duniya kuma Ba karya,thy have the reputation of being the toughest millitay arm in the world.
Rundunar marine guda 50 ya fi na sauran sojoji guda 100.
An san su da taurin rai da iya sanin makaman aiki dan haka suna da jiji da kai,a duk da dama aikin su yawanci a hade yake da navy amma kuma training guda ukun nan ya banbanta su da kowa a duniya.
Tace min khaldun sa’ood Tun yana karami dan shekara 12 aka kaishi academy na National oceanic and atmospheric adminstration comissioned inda PHS comissioned daga US suka dauke shi suka tafi dashi marine coast a cahn kasar south korea.
Anan ya yi training dinshi cikin jarumta, nan ma yayi aiki da thailand marine units ya rike matsayi kalala when he was just 21years.
daga nan mai kankat USMC
Suka dawo dashi united state for four years yana musu aiki a under ground as in a Sea war machine operation.
Alokacin har ya gama 4years din nan ko iyayen sa ma basu sake saka shi a idanun su ba
Tace kwananan Khaldun Sa’ood ya samu karin girma daga matsayain sa na colonel zuwa BRIGADIER GENERAL Dai dai da matsayin rear admiral of the lower half a cibiyar navy force shiyasa yanzu mostly kullum zaki ganshi a gida .
shi yake jagorantar bada cikakken command na da karan sojojin yaki dubu hudu a filin daga in yaki ya tashi.he is now a high ranked royal marine aikin shi bai wuce kullum yayi comanding wayannan 4,000 troops din ba,wanda aka fi sani da four batallions.
Ai kuwa nana A nayin shiru naji
Wani hadarin zufa ya keto min,jiki duk sai yayi sanyi Kamar wacce aka cire ni a deep freezer haka na kangare ina fidda ido waje ina kallon bakin nanah A,a kwakwalwata ina maimaita ma kaina dukannin bayanan ta.
Inner voice dina ne naji yana cemin so What did you expect now?Yau kinji shin wanene shi ko?
He is a bad ass comander in control of 4000 batallions, so Why wont he be hard and mean fisabillahi?
Da matsayin shin nan Ai abunda yake min ma kadan ne…. dik sai nagama scolding kaina fargaba kamar zai kashe ni.
Bantaba sani haka Allah zai qaddara a rayuwa ta har na fado a matsayin mai kula da privilaged personel kamar khaldun sa’ood ba
Sai dai Wani mummuman tsoron sa da fargaba ne ya kama zuciya ta sosai yanzu..
Gashi dama idanuna gaba daya sun rine tsaban kukan dana ci dazu.
Sai nayi jimmm karamar mai jimamin mutuwa
Nan Nanah A ta juyo tace meya ne kuma,wai ma me ya kawo ki nan ne lpya kuwa bahiyya?are you ok…tana dada dafa ni tana bani close look ina dan kauce ido na
Tana sake cewa bahiyyah daga nan
Bansan lokacin dana fara mata hawaye ba.
Lpiyar ki kuwa?
Hankali tashe ta dago ni..
Tace Yaya?
Meye ne,wani ya miki wani abu ne kike kuka
Nayi saurin girgiza kaina cikin kuka nace mata na shiiga uku
“Tace kin shiga uku why?banamsa ba na cigaba da kuka tohh kar na sake jin kin fadi haka .
Cikin razannan shesshekan mai hade da fargaban sanin shi din wanene a duniyan nn na furta..nana To ya zanyi,nidai ina jin tsoro.”I just ruined his shirt is he going to kill me?ni gaskiya zan gudu agidan nan nanah A pls help me escape.
Na dada sautin kuka na in cewa
…nikam na shiga uku ina yarfa hannu a rikice..
Mikewa nana A tayi tana kallo na Tun kafin ta bude baki
Saiga gurd ya shigo a hargitse
dana dube shi sai naga ma ashe wanda Ya bani kayan san dazu ne
Kana ganin fuskan shi gaka tashin hankali danko gaishe da nanah A bai tsaya yi ba naji coarse voice dinsa yace min kece bahiyyah?.
Na gyada masa kai
Toh maza kije khaldun yana neman ki da gaggawa.
Murya na narawa nace khaldun?
Yace eh,sai ziee hawaye suka saulo min..Sai ga soldier yabi ni da kallon tausayi.
Wani kukan na dada fashewa da shi na daura hannu a akaina..
Zai juya nanah A tace mishi dakata
Wai Meyafaru ne,sai ta dubi time 10 saura minti 5 tace min bahiyya dama baki gama dashi bane kika fito nan muke ta surutu?watoh
Baki kammmala aikin ki bako
A rude nace nafa kammala nanah its just that …sai nakasa cigaba
..
Gaba daya na damar da ita da rudewar danayi sosai Tsaban ta nuna ta yarda da ni
Bata tsaya ma jin me zanje agaba ba ta kalle gurds din cikin masifa tace
what is the problem?meyasa yake neman ta..are you sure shiya aiko la
Ko dai kunga kyakyawar mace zaku fara irin bazan halayen kun nan to wannan dai ba yar aiki bace.
Kanshi a kasa Yace
Kiyi hakuri Nanah A ba haka bane,Ai ta bar mopping duck ne abakin kofar dakin khaldun shi kuma yafito yana sauri zai fito ya karbe wani set din kayan sawa dayace na kawo
..tsantsi ya debe shi saura kadan ya zame kasa ya fadi..
A cewar gurds badon yayi saurin tare shi ba daya buga kansa akasa
Salati nana A tayi tana toshe baki cikin mamaki tana kallo na,nikuwa duk na birkice ina taro hawaye masu ban tausauyi,vike da samuwa Tace ma gurds where is he now,baiji ciwo bako?
Gurds yace yanzu dai yana daki dan har ya buga kafar sa he looks ok amma da alaman kafan tana masa zugi, he has cancel all meetings for today shine yace na kira ta.
Ji nayi jini ya dauke a jiki na,A Kasa na sulale kamar mai shirin kurma ihu kirji na dukan tara tara..
Duk da na naga alaman tausayawa a fuskan nanah A amma bai hanata dakewa tayi min fada ba.
Tace ai lin kyauta
Toh Kije maza ki same shi..ta nuna min hanya ranta adan bace.
A sadade na mike ina kuka ina tahowa site dinsa
10 minute ina knocking kafin ya bani izini na shigo
Gaba daya jiki na yayi lagwas sai sum sum nakeyi,sai da na taho face to face dashi ma kfin nasake tsinkayo kamannin sa da soldiern.
Yana zaune Ya juya kansa kafafun sa amike akan tebur yana tattabawa
Daga nan Ban iya sake kallon sa ba kuma ko rusunawan ban samu karfin gwiwar yi ba na dai tsaya ina murde murde da yatsun hannu na.
Wani shiru ne ya ratsa wajen.
Yana sane da abunda nake amma ko kallo na baiyi ba,Sai chan dai yayi magana chan Kasan makoshi naji yanacewa i believe you know what you did..
Na sauke kaina a sanyaye A sulale na taho na yi kneeling kusa dashi, hawaye na bin kunci na dan
Ban san dawani kalma zan fara bashi hakuri ba ga wani mummunn tsoron sa da ya shake min wuya.