NOVELSUncategorized

KWARATA 58

???? —— 57

    Muryar Al ‘ Ameen naji yana cewa daga duniyar mutuwa ka dawo bayan ka mutu kuma kowa ya sani , Bello yace wallahi nine ubanta ni na haifi abuna ku baku lura da kamin mu ba shi wancan ai uban riƙonta ne , cikin shashsheka ta wanda yasha gudu harya gode Allah ya ɗaga murya cewa ki tsaya mu tafi gidan Sultana , muryar wani daban naji shima cikin haki yace kai kuma neman me kake mata ?


      Allah ya kama bakin Bello yace wasu ke harinta kuma kasheta zasuyi shi yasa zan tafi da ita in ɓoyeta , shi a tunanin shi wannan wayau ne , domin gani yake idan ya kamani ko wani abu ya sameni baza’a zargeshi ba , a gajiye na kurɗo ta wani siririn lungu na sake bullowa bakin get in makaranta mu , kai tsaye na hawo titi yayin da Al ‘ Ameen ya ɗauki wani irin lafiyayen dutsi ya saitani ya jefoni da ƙarfi , na tafi tangal² zan faɗi kafin in gama saita kaina ya sake dan ƙaromin wata jifar ,

     Jama’a suka fara kai ׳ lafiya ? Al ‘ Ameen baya saurarar kowa gaba ɗaya sukaci gaba da jifata kamar muslmin da yayi ridda yayin dana raba tsakiyar titi biyu na kasa gaba na kasa baya , tsayuwar da nayi ne na kasa tafiya saboda jifar dasu Al ‘ Ameen sukayi min suka samu nasarar riƙeni sukaci gaba da dukana wai na basu wahala yayin da suka kasu gida biyu wasu suka riƙe Bello suna kai ɗan iska kaine ka ɗaure mata ƙugu take abinda taga dama ko ?

Kai tsaye yace Eh , saida suka bashi kashin bala’e ko motsi baya iyayi sannan suka ɗaureshi suka jefa banza mota kamar kare , lokacin da aka kai Bello mota aka dawo neman Al ‘ Ameen aka farayi amma tuni yayi layar ɓata babu wanda yaga ta inda yabi ya wuce.

      Gaba ɗaya hankalin kowa ya koma wurin Dikko dake zaune cikin mota yana kallonmu , a tunanina ni bai ganni ba , dan haka ina ganin sun juya hankalin su ya tafi wurinshi nima na samu sa’ar ɓacewa daga wurin , cikin ƙanƙanin lokaci na isa gida jikina sai ciwo yakemin ina zuwa wanka nayi da ruwa masu ɗumi , bayan na fito na canja kaya naje na zuba abinci naci nayi kwanciyata ,

      Gaba ɗayansu wurin Dikko suka nufa cikin farin ciki dan ba saboda Dikko suka saki Sultana ba sundai tafi maularsu ne kawai , kuma shi kullum ranshi a haɗe yake shi yasa baka iya gane a wane irin yanayi yake farin ciki ko damuwa ,

      Sudai umarni kawai aka basu su kamo Sultana saboda haka basu san komai game da ita ba , sundai ga Dikko kawai sunzo su gaishi dan sun san zasu samu kuɗi ne a wurinshi shi yasa suka saki reshe suka kama ganye , suna isowa suka fara kirarashi irin dai yadda “yan maula sukeyi , kallo ɗaya yayi musu ya ɗauke kanshi yana so yaga ta ina Al ‘ Ameen zai ɓullo ,

      Shi kuma Al ‘ Ameen bayan wasu mintuna a tunaninshi Dikko ya tafi dan haka ya fito daga maɓoyar shi , fitowar da zaiyi yaga Dikko dan haka baiyi gigin komawa wani wuri ba ya nufi mota da gudu ya shiga yaja ya tafi a haukace , da gudu Dikko yabi bayanshi dan yayi alƙawari yau da Al ‘ Ameen da An mata babu abinda zai hana ya tabbatar da baƙin ciki a zukatansu ba , 

     Abinda yasa zai ci mutunci Al ‘ Ameen saboda yadda yaga yana jifar An mata ya wulaƙanta mishi “Yar matanshi kuma shima sai ya wulaƙanshi ko da kuwa haka zaiyi sanadiyar gogewa farin ciki daga rayuwarshi har ƙarshen numfanshin shi , in banda ƙasƙanci “Yar mata ma zai jefa ? Kuma saman titi kowa yana wuce yana gani sai kace ta aikata wani babban zunubi….?

     Ita kuma yau zai nuna mata shi cikakken mai zuciya ne in bata san haukarshi ba yau zata sani kuma zatayi baƙin gani da dana sanin saninshi tunda yana tausaya mata bata sani ba , ya ɓarar da farin cikinshi da komai ya zauna tare da ita dan dai ya sama mata farin ciki da natsuwa , yabar matarshi ya taho wurinta shi zata maidai baisan abinda yakeyi ba , zuciyarshi kuma sai ƙara tunzurashi takeyi tana hasko mishi irin balbalin azabar da zai horar da ita da ita.

       Ai jima yayi bazai iya bin Al ‘ Ameen ba saiya fara da An mata , wani irin mahaukacin burki ya taka ya fara ƙoƙarinyin kwana saman tsakiyar titi yayin da mutane suka fara kaucewa dan kar ya gogar musu abin hawa , aiji yayi ma bazai iya tsayawa ɓata lokacin yin kwana ba , da ribos ya fita daga titin yana kai ƙarshe ya juya sitiyarin motarshi ya yanki hanyar goruba , yanda yake tuƙin ne yasa hankalin jama’a ya tafi wurinshi , yayin da wasu ke cewa ko lafiya wancan wasu kuma na cewa ai shi dama haka yake wannan iskanci babu abinda ya dameshi da rayuwar da wani zai shiga shi kanshi kawai ya sani dan Allah ya basu damar duniya shi yasa basu san darajar kowa ba , a , a gaskiya sun san darajar mutane shi dai kaɗai keda wannan halin , waye wai …? Wani ya tambaya.

     Dikko ne ai shi kaɗai keda wannan baƙin halin mahaifi shi ba haka yake ba , wasu kuma cewa sukeyi ai ɗan iska ne , yayin da wasu kuma suke cewa aini burgeni yakeyi ko nine matashin da na samu irin damarshi saina fishi iskanci kasan su kuɗi jigo ne masu nuna isashshen iko ku barshi yayi Allah ya bashi gara yaji da ƙuruciyarshi wata rana ko ance yayi shekaru sunfi karfinshi baya iyawa , wani yace gaskiya izzar kuɗi da ƙarfi take muma Allah ka bamu masu amfani dan idan kana da kuɗi ji kakeyi kai kafi karfin kowa ka taka wanda kake so ka murje wanda ya shiga gabanka , magana dai ce ta kuɗi su zasuyi bayani kuma da kansu kuɗin zasu baka hakuri kuma ka haƙura , niko dai nace hmm ita dai rayuwa duk abinda mutunci baiyi ba rashin mutunci bazai yi ba , idan an ciza dai a busa dan ita duniya bata da tabbas yanzu takeyin ka anjima ta barka , idan ka raga sai ta raga maka dan duk abinda kake tunani kafi karfinshi sai a wayi gari ya gagareka Allah dai yasa mu dace ,

     Bansan ta inda ya biyo ba kuma banji shigowar shi ba ina kwance dan har na fara bacci saboda gajiya , bansan yadda akayi ba kawai dai na farfaɗo naga ana ta riƙe Dikko yana wata irin zabura yana magana da turanci saidai inji yace An mata sai yace Momy yace Dady , 

   Jini na gani a jikina bansan ta ina ya biyo ba , duk inda na shafa fuskata jini ne bansan da ina da ina ya fasamin ba , tunda nake ban taɓa ganin irin masifa ta Dikko ba ɗan bala’e ne na ƙarshe duk taron abokanshi sunfi su nawa amma wallahi girgiza ɗaya yakeyi ya zuddasu sai su sake riƙoshi so kawai yake ya iso wurina amma sun san idan ya sake riƙeni tawa ta ƙare ,

     Ciƙin ɓacin rai yaci gaba da magana da hausar shi irin kamar bata riƙe mishi baki sosai ba wata irin magana yakeyi , kuma ba irin ta yare ba wata irin murya dai gareshi cikin sanyi yakeyin magana ko yana fushi maganarshi bata canjawa yarinyar can saboda ta ɗaukeni ɗan iska har marina tayi , yana nuna inda na mareshi yaci gaba da cewa idan aka buɗe min fili da irinki dubu duk wanda nayi ma duka ɗaya ya tafi bazai sake dawowa ba har abadan abada ko kina ganin tsoronki nakeji ? So hauka ne ? To ki sani bani na ɗora ma kaina ba Allah ya jarabceni kuma kema idan ya juya alƙamin sa akanki naki ya ƙare ƙaramar yarinya dake babu abinda ke cikin kanki sai wawanci da ƙuruciya , ke banda ƙaddara da hukunci Allah har kin isa kisha inuwa ɗaya dani ina ɗaga miki bakya gani tou yau ƙaryarki ya ƙare saina raba gangar jikinki da ruhinki , badai ina cewa kada Allah yasa kiga fushina ba ko ? Yau yazo kuma bazai tafi ba kin bani ׳ ya ƙarasa maganar yana nunani da ɗan yatsa , kwacewa yayi daga riƙon da sukayi mishi ya fita ,

    Wani abokinshi da naji yana cema Yazeed yace ke An mata kike baki kyautawa abinda kikeyi ba’a rayuwa haka yana ƙoƙarin kare miki mutuncinki da martabarki bakya gani , tunda yace karki je dole sai kinje ,  yace miki bayajin daɗi yaji wani abu zai faru dake ai sai ki tausaya mishi kamar yadda yace miki jarabta ne daga Allah kiji tsoron jarabta ya dawo kanki , ke da kinsan halin DK da kuɗi idan yace kar kiyi wani yace kiyi zakiji tsoron fushin shi , Allah ma ya rufa miki asiri da mutane a gidan yau da kin gwamce ma aya zaƙinta ,

    A tsiwace nace dan naje kawai sai ya dakeni ko ni baiwa ce ne ? Da mamaki Yazeed ya kalleni yace tou ai da yake yanzu zai dawo sai ki tambayeshi abinda yasa ya dakekin yama iya saka suna da yace miki An mata… “Yar ƙaramar yarinya dake sai tsattsaga masifa Dikkon ne ma dai² dake.

     Dama nace kaine dai² ni ? Dariya yayi yace ai riƙon mahaukaci sai sarki , nice mahaukaciyar ? Yace ah ah karin magana ne ni na isa ince miki mahaukaciya ai ke da ss kikayi kama sarkin bincike , dariya sukayi tare da tafawa suka koma palo sukaci gaba da kallon boll insu.

Wallahi Allah yau sai an faɗamin abinda yasa ba’asan An mata a gidan nan , laifin me tayi muku ne wai ? Momy tace na tsani yarinyar nan Dikko idan zakayi rai kayi rai idan zaka mutu ka mutu dan ubanka bansan yarinyar nan kuma har abadan duniya bazan taɓa santa ba , kuma har gobe har jibi ina nan zaune akan bakana sai an kamo min ita kuma saina wulaƙanta mata rayuwa kamar yadda nayi alƙawari bazan fasa ba ,

       Haba Momy wai me tayi miki haka da ciwo don Allah ? Me tayi min ma kake tambaya ko ? Tou ubanka tayi min kaji ko ? Momy bana so ayi abinda za’azo aji babu kyau ki sauƙaƙa zafin ƙiyayyarki akan ta kafin aji wani iri wata rana , ko wata ranar tazo banajin komai kuma babu abinda zai faru idan wanda ya mutu zai dawo naga yadda zakayi ka auri karuwa ina numfashi ,

Wai waye yace karuwa ce ? Abinda kowa ya sani duniya da mutane sunyi mata tofin Allah barbaɗe , murmushi Dikko yayi mai ciwo yace duk bakin daya tofawa An mata Allah tsine insha Allah saiya tofa mata albarka babu daɗewa ,

      Momy tace mahaukacin banza ka taɓa ganin albarka ta sauka akan tsinuwa ? Ko ka taɓa ganin iccen da tsawa ta faɗa ma ya sake tofowa ? Ai tsawa so ɗaya take faɗawa icce ya mutu shikenan ya gama rayuwa a duniya dai , juyawa Dikko yayi bai sake magana yana tafiya cikin yanayin mai wahalar fassaruwa ,

      Yace gaskiya ne nine tsawar da na sauka akan An mata , kuma Allah zai taimakeni ita bazata mutu ba zata rayu cikin farin ciki kuma zatayi ganye tayi rassai zata zama alfahari a wurinki Momy idan har na auri An mata zaki sameta mai biyayya , ajiyar zuciya ya sauke dakel tare da lumshe idanuwanshi a bayyane yace Allah dai ka taimakeni a gano min inda mahaifiyarta take da wuri in miƙata cikin aminci da salama.

     Harya taho bai samu nasarar ganin Al ‘ Ameen ba amma ya ja mishi layi zasu haɗu komai daɗewa kuma wallahi yadda ya jefi “Yar matanshi sai yayi mishi wulaƙanci na kafa tarihi marar gogewa a rayuwa.

       Da tunanin Sultana ya isa gidanshi baiji daɗin abinda yayi mata ba amma ya zama dole ya koya mata tsoronshi dan idan harya aureta da wannan taurin kan nata matsala za’a samu , dole ta yadda shine a samanta kuma dole ta koyi bashi girma idan dan tana ganin murmushin shi zaisa ta rainashi zai tsare girmanshi bazai ma sake mata wasa ba tunda ita bata da wayau ,

     Cike da tsantsar sha’awar kasancewa da Jiddah ya shiga gidanshi , shi baisan abinda yasa idan harya haɗa jiki da An mata yakanji yawan buƙatar kasancewa tare mace ba , dakel yayi wanka yana fitowa ya samu Jidda zaune a gefen gadonshi tasha wanka na ɗaukar hankali sai zabgaga ƙamshi takeyi mai tada hankali duk mai wata “yar guntuwar sha’awa ,

     Cikin bariki ta fara mishi sannu da zuwa dakel ya ansa dan rabi da kwata hankalinshi baya nan ya tafi wata duniyar , yau tafiyar safe kayi my excellency ? Kallonta yayi tare da tambayarta ina naje ? Murmushi tayi mai ɗaukar hankali tace Abuja mana , waye yace miki ina Abuja ? Ai naga kwana biyu baka nan nasan kuma idan kana gari ina zaka je bayan gani ta ƙarasa maganar tare da “yar karairaya dai ta matan da suka san hannunsu wurin iya tattalin miji ,

      Wani irin kallo yayi mata mai tayar da tsikar jiki cikin salon tafiya da hankalin mace yayi magana cewa Ey to miye ? Yayi maganar tare da miƙa mata hannunshi , tasowa tayi bayan ta bashi hannun nata saida ya sumbaci bayan hannun sannan ya buɗe tafin hannun yayi tsini da harshenshi yayi mata wata irin lasa a tsakiyar tafin hannun nata ya ƙare da sumbatar inda ya lasa ciki tako mai nuni da yayi rashinta , lumshe idanuwanta tayi tare da sauke ajiyar zuciya cikin yanayi mai nuni da saƙonshi yazo.

      Jiddah fa ba’a baya ba shima Dikko jajirtacce cike da kulawa da junansu suka shiga masayar soyayyar ta hanyar ƙoƙarin dasawa junansu farin ciki irin na ma’aurata daga baya aka koma saman gado domin doguwar tafiya dole saida guziri , suma dai sunyi ma kansu guzirin gado , a sama aka caskale yadda ya kamata saida Dikko ya tabbatar ya kore duk wata tsohuwar ƙishirwar dake tattare da ita sannan shima ya samu natsuwa , amma wani abu da Jiddah tazo dashi shine ,

      Kai tsaye ta nunawa Dikko kwalbar da bokansu ya bata cike da rashin wayau tace Yaya da Allah ka ɗan taimakamin , idonshi a rufe yana samanta bai sauka ba yace wane irin taimako ? Wani magani ne zan haɗa kuma da sinadirin namiji ake amfani dashi dan Allah ɗan kaɗan zaka zubamin anan ta miƙa mishi kwalbar , jin kwalba a hannunshi yasa ya buɗe idanuwanshi yace wane irin magani ne ake haɗawa da najasa dan tsabar ƙazanta ,

      Nidai don Allah , tou ke me zai hana baza kiyi da naki ba tunda kece kike ra’ayi , ai na namiji akace , um umm aini ba namiji bane ba , nidai haka nan don Allah murmushi Dikko yayi a rashin shi yace kila wani fahami aka bata ta jiƙamin a soɓo mata ni sharrinku ai sai in rubuta littafi tunda cikinku nayi rayuwa , kallon agogo yayi ya jinjina kanshi yace da 15 yanzu zan koma 20 duk masifarki lokacin ya tafi bazai dawo ba , wato harma na namiji , 

     Jiddah taci gaba da dan Allah dan Annabi , banza Dikko yayi bai mata magana ba , saida lokacin daya iba ya cika ya sauka daga saman gadon ya nufi toilet , bayan mintuna 30 ya fito , ƙananan kaya ya saka bayan ya feshe jikinshi da turare ko inda Jiddah take bai kalla ba ya ɗauki wayoyinshi ya fice.

       Yana fita ta ɗauki wayarta ta kira Al ‘ Ameen ta rattafa mishi yadda sukayi da Dikko , faɗa yayi mata cewa haba ranki ya daɗe ya akayi kikayi wannan kwaɓar kinja ma kanki nayi imani da girman Allah mai gida ya taso ki gaba da bin bincike kinja mana kuma ki rubuta ki ajiye wallahi ko ruwan gidanki bazai sake sha ba , ke kina wasa da mai gida ? Wai kin kuwa san yadda yakeji da rayuwarshi ? Kai gaskiya kin ɓata wallahi mi yasa kikayi haka ???

     Jiddah tace no ka gane Al ‘ Ameen wannan ba damuwa bane ba idan haggu taƙi kawai mu dawo dama , ka bari saura sati ɗaya na fara period sai in zuba kawai ka kai mishi , tunda malam yace idan akayi amfani da jinan al’adata sai yadda nayi da Yaya , sperm in nashi ne yace idan anyi amfani dashi za’a goge mishi ko wace mace daga zuciyarshi saini ɗaya…

Ba haka Al ‘ Ameen yaso ba kawai dai yace to , bayan sun gama waya da Jiddah ya kira Mardiyya tana ɗauka yace Doughter zan shigo kaduna zuwa cikin sati na gaba yaushe kike fara al’adarki ? Uncle meya faru ? Boka yace a kawo sperm in mai gida tou naso ace an samu amma matar tashi wata aljihun gefe ce ta kasa , wai dan wawanci irin na sakakkin “ya “ya kawai taba mai gida kwalbar wai ya zuba mata maniyinshi kiji hauka da ɓacewar hanya , dariya Mardiyya tayi tare da cewa Uncle ni zanzo in kawwo ƙarshen film in nan haka nan ,

      Al ‘ Ameen yace karki zo dan in faɗa miki yauma nemana yake saboda tsigaggiyar yarinyar nan , yanzu dai yaushe kike fara naki jinin ? Mardiyya tace jiya na fara , Al ‘ Ameen yace tou zan shigo kadunar gobe in ansa in kaiwa boka , dan dama nama boka bayani akan ki zai haɗa maganin kinga idan akayi sai a kawo ma Jiddah sai mu samu tayi mana amfani dashi wurin ba mai gida , tana jiran taji soyayya sai kawai tajita a out… Cikin jin daɗi Mardiyya tace na gode Uncle Allah ya kawo ka lafiya yace amin my doughter ki gaishe da Yaya saina zo , zataji sukayi sallama.

     Wallahi ni ba Babanta bane ba , wani irin mari aka wanka mishi harsai da haƙorinshi na ƙurya ya fita , cikin kuka yace wallahi ranka ya daɗe ɗiyar abokina ce , wani ne yakai mishi duka a ciki tare da cewa idan tafi ƙarfinka batafi karfin hukuma ba , Bello cewa yakeyi wallahi ranka ya daɗe ba “yata ce ba , saida sukayi ma Bello lullusar fitar hayyaci sannan suka wurgashi a cell suna cewa idan ka kawota sai mu fitar dakai.

      Nayi ² na tuna abinda ya faru dani ban sani , na kasa sanin ta yadda akayi Dikko yayi min wannan dukan har yajimin ciwo ba tare dana sani ba , ko dami ya dakeni ? Duk yajimin ciwo fuskata kuma duk sahun mari ne lallai duk yadda akayi bugun bala’e yayi min tou meya ɓata mishi rai haka …. ?

        Dakel nayi sallah isha’e kafin in tashi daga inda nayi sallah masarar ta lulluɓeni kasa komawa nayi saman katifa duk jikina ciwo yakemin na kasa wani ƙwaƙƙwarar motsi gaskiya nasha azaba ta ban mamaki a ranar nan !

        Tunda na kwanta ban iya wani isashshen motsi ba har gari ya waye , haka na tashi jikina yayi tsami dakel na iya yin wanka nayo alwallah dan yau na makara tunda na kwanta sai 8:39am na farka ,

    Bayan nayi sallah ko mai ban shafa ba na saka kayana na fita palo , kamar jiya yauma yana zaune a inda ya zauna jiya ko inda nake bai kalla ba ya ƙaddara ma baisan Allah ya ajiyeni ba , daga nesa dashi na tsaya nace ina kwana ,

        Bai ansa ba , kuma bai kalleni ba hankalin shi nakan wani littafi yana dubawa , wuri na samu na zauna kamar an sani na zame gefen hijabin nace duk wanda jamin ciwo anan ban yafe mishi ba , kuma tafiyata zanyi tunda bansan abinda nayi maka ka dakeni ba , na ƙarasa maganar ina kuka ,

     Ba tare daya kalleni ba yace An mata zo nan , tashi nayi na tafi kusa dashi ina kuka , wuri ya nunamin na zauna , cikin tausayi ya kalleni yace nine baki yafe mawa ba ? Ni badai nake ba , to dawa kike bayan dagani saike a palon , aini ba kai nake jama Allah ya isa ba , to kin yafemin ni ? Kaina na ɗaga alamar Eh , yace kiyi haƙuri ni bana iya sarrafa fushi bansan abinda yake damuna ba idan nayi fushi saina sauke ki daina ɓatamin rai kinga dai ina sanki bana so kina shiga rayuwa mara kyau , kowa dariya yakemin wai An matar ma da nake taƙama da ita abida batajin magana kuma bata so na , kinsan me nake cewa ?

     A , a , na bashi ansa , kyakkyawan murmushin shi yayi tare da tsareni da idanuwanshi masu ɗaukar hankali yace ai nasan zaki faɗa ya ƙarasa maganar yana min hararar so , murmushi nayi cikin jin daɗi na gyara zamana ina kallon kyakkyawar fuskarshi gaba ɗaya sai naji masassarar da nake ji babu , yace ko nayi ƙarya ? Girgiza kaina nayi alamar a , a ,

    Shi kuma yaci gaba da cewa ni ko nace zanyi fushi dake wallahi ƙarya nake bazan iya ba , da kinsan yadda kike da mutunci da daraja a wurina da kin daina wahalar da zuciyata da taki , kina ta fama da wahalar dakon so bayan nasan yanzu idan har zamu rabu sai kinyi kuka , tafiya zata iya riskata a ko wane lokaci zan tafi na barki da tunanina babu dare ba rana , zaki kasa bacci dare zai miki nisa wurin kwanciya zai miki girma zaki ga rana ta daɗe bata faɗi ba yayin da kika tuna Dikko baya tare dake , kawai ki daina wani ɓoyewa ki faɗi abinda ke cikin zuciyarki nidai tuni na faɗi nawa , ya ƙarasa maganar tare da miƙomin ɗan yatsan shi mu shirya , dan kinsan jiya na ɓata dake….

       Miƙa mishi ɗan yatsana nayi ya lanƙwashi shi da nashi yace faɗamin me yasa bakya so na ? Shiru nayi yace amma ai kina so na mi yasa kike ɓoyewa ? Rufe idanuwana na nayi yace yi haƙuri An mata faɗamin matsayaina a wurinki me yasa kike min wasa da zuciya , 

      Cikin kuka nace a wata rana kayi magana akan idanuwa na , to wannan ranar tayimin naji kamar in rungumeka a wannan ranar sannan nace ina sanka ,

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());        Wata irin ajiyar zuciya ya sauke da sauri tare da dafe dai² zuciyarshi da duka hannunshi biyu ya kwantar da kanshi saman kujera tare da lunshe idanuwanshi yace me yasa baki faɗa ba a wancan lokacin An mata ?

        Shashshekar kuka nayi tare da cewa saboda ina tsoron kada na rasa ajina , sauko kanshi yayi ya kalleni yace wallahi Allah babu ranar da ajinki ko wani mutuncinki da zai rage a idona ko a zuciyata , ki taka yadda kike so ina tare dake tsakanin rayuwa da mutuwa , waccan ranar kinji kamar zakice kina so na , yau fa ? Yauma kinajin kamar kina so na…………?

        Su Yazeed ne suka shigo palon , cikin zaulaya yace An mata an shirya kenan a dai² lokacin daya iso yaba Dikko hannu suka tafa , bayan sun tafa Dikko yace aimu bama faɗa ko An matana ? Jiya ma sheyɗan ne yazo kuma mun koreshi bazai sake dawowa ba ko ? Shiru nayi zan tashi ya riƙoni tare da turani saman kujera shima ya dawo kusa dani ya zauna su Yazeed suka samu wuri suka zauna , 

       Yazeed yace zakaje ko ka fasa ne ? Ya tambayi Dikko , ɗan gyara bakinshi yayi ya riƙe leɓonshi na ƙasa dana sama yace gaskiya banajin zanje , a , a kar kayi haka kayi haƙuri ko daga ƙarshe ne muje ai yafi bamu je ba , kallona Yazeed yayi yace ai kema zakije ko “Yar mata , dogon kallo Dikko yayi mishi sosai sannan ya kalleni tare da nunamin inda makullin mota yake yace jeki ki ɗauko abinci a mota , saura idan kinje ki ƙara gaba….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button