HEEDAYAH 14

Baffa ne ya bude kofar parlon Kaka da sauri jin ihun da Heedayah ke yi ya shiga, shi ma shigowarsa gidan kenan daga masallaci an idar da isha, Kaka
ce ta danneta sai shafa mata wani magani kamar rub take a kafan da ke ciwo, Baffa ya bude baki yace “Meye haka kuma Baaba?” Kaka dake ta hada xufa
tace “Toh sai a biye mata tana dingishi baxa a san na yi ba, so ake ta dawo gurguwa ga makanta abun ya taru ya ma d’a na yawa? da wanne ake son ya
ji, a hankali fa nake mata amma da yake munafuka ce algunguma dubi tonan asirin da take min kamar warce nake yankawa” Baffa yace “Don Allah ki
kyaleta Baaba, ba tana shan magani ba, a hankali xai bar mata ciwon ai” a fusace Kaka tace “Maganin banxa maganin bature, ka san daga wani kasa aka
kawo min wnn din da nake shafa mata, ku dinga kallona kamar ban san me nake yi ba, toh naki kyaletan sai ka kwace ta ai” Ita dai Heedayah bata fasa
ihun da take tana kiran Abba ba, aka bude kofa Sudais ya shigo parlon da sauri shi ma daga masallacin yake, Bude baki yyi yana kallon kakar tasa,
tace “Kai ka ji ubanka da wani magana Sudess, daga taimako fa xai min rashin kunya, ita kuma yar banxan magani fa nake shafa mata….” Sudais yace
“Toh kaka ba ke kika sa ta wanke wanken ba, ai sai bari har lkcn da kafar yyi niyyar warkewa ya warke da kansa, ynxu hakan da kike mata idan kika
sake ji mata wani ciwon fa?” Kaka ta tura Heedayah a fusace tace “Ni dai Allah ya isa wllh, ya xa a dinga cewa ni na sa ta wanke wanke, ga yarinya
dai da bakinta ko bata da ido ai sai ku tambayeta ta fadi gaskiya mana, kawai kawai an mayar da ni karamar mutum a gidan nan sbda ana bani abinci a
kwano…. Ban da xalunci me xai sa in sa makauniya wanke wanke idan ba ita ta bukaci yin hakan ba da kanta??” Juyawa Baffa yyi ya fita daga parlon,
Sudais ya jira har ya rufe kofar sannan yana nunata yace “Ke dai kawai baki son gaskiya, ki yarda kawai kin kusa karya yar mutane kin sa ta wanke
wanken da kika tara an kwana biyar….” Kaka ta fashe da matsanancin kuka tana jawo dankwalinta xata yi hankici da shi, Sudais ya daga Heedayah
suka fita parlon ya kulle mata kofarta yana murmushi, Heedayah dake dingishi tashin hankali a fuskarta tace “Plss ka wuce da ni wajen Abba kar ka
dawo da ni nan” kallonta yake bai ce komai ba har ya isa stairs, daukarta yyi ya wuce sama, dai dai xai ajiyeta sai ga Ummarsa ta fito daga part
dinta, tsaye tayi tana kallonsa da mamaki fuskarta, yace “Sannu da gida Umma…” Bata amsa ba tace “Ka sameni a parlona yanxun nan” daga haka tayi
wucewar ta, bangaren Aunty ya shiga yana rike da Heedayah, Aunty dake xaune saman darduma ta idar da sllh tace “Ta ya kaka ta yrda ka fito da ita,
daxu da rana kiri kiri taki yarda in fita da ita, wai ba ruwanta yar amana…” Sudais yyi dariya yace “Ae tana can na barota tana kuka” Aunty tace
“Kai dai baka gudun abun magana koh Aliyu?” Ya xaunar da Heedayah saman kujera yace “Danneta fa tayi tana ta ihu wai magani take shafa mata a
kafar” Dariya Aunty tayi ya juya yace “Ina xuwa Umma na kirana…” Tace “Amma xaka dawo ai” yace “Ehh xan dawo” daga haka ya fita, Dawowar da bai
yi ba kenan har sha biyun dare yyi, Heedayah har ta gaji da tambayar Aunty ko ya dawo, Aunty ta kai ta bathroom dinta tayi fitsari sannan ta
kwantar da ita saman gadonta nan da nan bacci ya dauketa, yaranta kuma suna dakinsu dama… Aunty na kwance har ta fara bacci ta ji ana kwankwasa
kofar bedroom dinta, ta mike ta kunna wutan dakin tana kallon agogo ta isa kofar ta bude, Baffa ta gani tsaye kafin ta ce komai yace “Yarinyar nan
na nan ne?” Da mamaki Aunty tace “Tana nan har tayi….” Hango kaka da tayi tsaye bakin kofar parlor tayi kicin kicin da fuska ya sa tayi shiru,
Baffa yace “to fito da ita” Aunty bata ce komai ba ta juya ta koma dakin, sai a sannan ta girgixa kai ta shiga tada Heedayah, tana rike da hannunta
har sannan tana magagin bacci suka fito parlon, Kaka tace “A bani amana sbda ance maku ban san girman amana ba xa ku cuceni ku dauketa, to uban me
xata maki a nan din banda gulma Hauwa? wllh Umaru kasa bacci nayi, gani nake kawai Allah na fushi da ni, idan Amadu ya ji wnn me ku ke son ya
daukeni? To ba ruwana a maido min da abata….” Baffa dai bai ce komai ba, Kaka ta warce hannun Heedayah a na Aunty ta fice daga parlon Heedayah da
har baccin ya fice a idonta jin muryar kaka ta dinga bin ta kamar xata yi kuka, Baffa ya girgixa kai yana kallon Aunty yace “Toh Allah ya kyauta”
dariya tayi tace “Halan har ka fara bacci” yace “Nayi bacci mana dama” daga haka yyi mata sai da safe ya fita. Kaka na shiga bangarenta ta kulle
kofar tace “Gantalallen yaro kawai in sake ganinsa a parlona idan ban ja Allah ya isa ba” furan da ta rage ma Heedayah ta dauko mata ta ajiye
gabanta tace “Gashi nan baxan shanye ban baki ba kar Allah ya tambayeni, duk da mugun halin ki” Heedayah ta ta6a cup din a hankali ta kai baki ta
fara shan furan kamar xata yi kuka. Washegari juma’ah da safe Mami ta xo tafiya da Heedayah, Kaka ta kwaso kayanta da ta wanke ta linke su fesss
tace “Sai kin sa ido sosai kan yar nan, shegen son jiki ne da ita kamar mage, baxa a fake da makanta ba a cuceta….” Mami tace “Toh mama” Kaka
tace “Toh har yanxu baki saka ranan tarewar bane ke kuma? Ba a fa wasa da igiyar aure” Mami tace “Yanxu haka can gidan xa mu wuce gaba daya” Kaka
tace “Toh alhmdllh, kin dai ji duk nasihar da na maki ranan ai ko, yanxu haka matar na can ta dawo, bbu ke bbu ita” Mami tayi murmushi tace “In sha
Allah” sai kusan sha daya suka bar part din Kaka tare da Heedayah….. Horn Mami tayi dai dai gate din gidan Barrister Ahmad, mai gadi ya bude gate
din ta ja motar xuwa cikin gidan tayi Parking a space din yin hakan, Da taimakon ta Heedayah ta fito a motar, tana rike da hannunta suka nufi
entrance din shiga main parlor, Shuraim ne xaune balcony din da system a gabansa, tun daga nisa da ya kallesu ya dauke kai ya ci gaba da abinda
yake a laptop har suka iso balcony din, Mami bata kallesa ba tace “Take off ur shoes Heedayah” Heedayah ta fara cire takalmin kafarta, Mami ta
ajiye su gefe, ita kam dama bata cire nata ba da shi ta shiga tana bude jakarta don fiddo wayarta dake ring, ta daga ta kai kunne, Hajiya Amina
mahaifiyar Sudais ce parlon da Mumy sai Hajiya Sadiya da Hajiya kyauta, kallo daya Mami tayi masu ta cikin siririn glasses din idonta still holding
Heedayah’s hand ta nufi bangarenta tana cewa “Ai court ma baxata bada bail dinsu ba, their case is different, baxai yiwu ba ma, so kar ku ji komai,
pls hold on I will call you later” tana fadin haka ta katse wayar ta fiddo makullinta don bude bangarenta wanda aminiyarta da sister dinta suka xo
tun jiya suka yi gyare gyaren da ya kamata, tana shiga ciki rike da Heedayah ta kulle kofar. a hankali Hajiya Sadiya tace “Tabdijam, lallai kina da
aiki babba a gabanki Maryam, idan baki yi hankali ba wnn farar matar dai kwace maki gida ta shigo yi, ke kin ji wani kamshi da take xubawa kuwa,
kalli fa ko kallon arxiki bata mana ba sai xancen kotu da bail take, da takalmi ma ta shigo parlon don rainin wayo…” Hajiya Maryam da taji kamar