SULTAAN HAUSA NOVELS

SULTAAN 1

???? S U L T A A N

Mss Flower????

FITATTU HUƊU????

ALHAMDULILLAH! AFTER A SHORT BREAK I’M BACK WITH ANOTHER AMAZING STORY, DIFFERENT FROM ALL U’VE READ AND WHAT I HAVE WRITTEN, DIFFERENT JOURNEY FULL OF EXCITEMENT, FLOWERS AND THORNS

FIRST CLASS WRITERS ASSO…

       *01*

DISSO, YAMANIYYA

Disso ɗan ƙaramin gari ne da ke cikin wani yanki na ƙasar Yamaniyya, gari ne mai ni’imtacciyar weather,garin bai da zafi ko da kuwa lokacin zafi ya kama ko don bishiyyun da suka yi wa garin ƙawanya, ga kuma ruwa mai girman gaske wanda ya haɗa hanyoyin sassa da dama na duniya, mafiya yawancin mutanen da ke zaune a wannan gari musulmai ne sai dai sun fi riƙo da al’adunsu sama da addinin, mutanen wajen yawancinsu mafarauta ne dalilin dazukan da suka zagaye garin mai cike da albarkar namun daji, yayin da wasu suka kasance masunta masu kamun kifi da namun cikin ruwa, suna taɓa kiwon dabbobi irinsu shanu, tumakai da sauransu sai dai matasa ne maza da mata suke wannan aiki. Jama’ar garin kyawawa ne na sosai don kyawunsa har akan rasa taƙamaimai su wanne ƙabila ne, za ka yi tsammanin Indiyawa ko larabawa ne in ba sun yi magana ka ji harshensu ba, haka fatarsu ba fara tarr ba ce kamar Indiyawa da fararen larabawa ta fi yanayi da hasken ƴan ƙasar Ethiopia, gari ne mai matuƙar tsari wanda duk mai girma ana ba shi girmansa yayin da bawa ya kasance marar galihu, tsananin azabtarwa ta yi yawa.

Garin ya yi lufff dalilin hadarin da ke haɗuwa a sararin samaniya, ga iska mai cike da ni’ima da sanya zukata shauƙi da ke kaɗawa tana haɗawa da saka bishiyun da suke cike a garin rangaji, bakin tafkeken ruwan kyawawan ƴammata ne suna wanka cike da shauƙin yanayin yayin da tulunsu na ɗibar ruwa ke bakin ruwan sun ajiye, wasa suke suna ƙyalƙyala dariya don hirar wanda ya zame musu tamkar numfashi ce suke yi wanda ya zame musu hankaka, sun kasa gane gabansa bare bayansa.

Cike da taku na nutsuwa yake tafiya, bayansa ɗauke da ƙatuwar barewa, yana tafiya yana fito yayin da fuskarsa ke fidda wani annuri alamun yana cikin nishaɗi duk da kuwa ba ya dariya ko murmushi, mugun sai in abu ya ɓaci, miskili ne wanda ya fi mahaukaci ban haushi na sosai, za ku kwana ɗari ɗaki guda amma magana ƙwara ɗaya don ta shi ne ba za ta taɓa haɗaku ba, ba ya taɓa shiga harkar da ba ta shafesa ba, idan kuwa ka shiga ta sa gonar lallai sai ka gwammaci rungumar mayunwacin zaki da wannan kuskuren, ba ya hayaniya ba kuma ya son magana, ga shi da hali na riƙau muddun kai masa ko za a tashi duniya sai ya maka ramuwar gayya, kaifi ɗaya ne in har ya furta ta zauna ko me za a yi ba zai canza kalami ba, kyakyawa ne na ajin ƙarshe a ɗan ƙaramin garin shi ne farko, ko mace ta yi kaɗan ta gwada masa kyawun fuska, namiji ne a tsaye don sura da ƙirarsa kana gani ka san irin ƙarfafan mazan nan ne, batun ƙarfi kuwa sai ya watsar da sadauki goma a filin dambe, namiji duniya ke nan, namijin gaske, ga shi da mugun farin jini da kwarjini, duk da kasancewarsa bawa ɗan bayi izzarsa da mulkin da yake zubawa har ta zarce ta ƴaƴa masu ƴanci, mugun farin jinin mata garesa sai dai ko kallon kirki ba su ishesa ba, sam ba ya da lokacinsu, shi da zaku shekara ma ba ka ga ƙwayar idanunsa ba don kullum a ƙasa suke, Sultaan ke nan al’amuransa na rayuwa sun saɓa da na sauran jama’a, bawa mai farin jini, duk wani maƙiyinsa sai dai hassada don bai san da zamansa ba ma bare ya ɓata masa. Ɗauke kansa ya yi ko da ya kawo saitin da ƴammatan ke wanka, har ya gifta ya ji wata murya ta yi kiransa, ɗan dakatawa ya yi ba tare da ya juya ba

Hannunta ta ɗora kan bayansa tana shafawa ta juyo zuwa gabansa tana kafesa da kallo, sarai ya santa tun suna ƙanana ta gallazawa rayuwarsa, fita ɗari shiga ɗari sai ta kirasa ɗiyar aminin uban gidansu ce, da murmushinta ta ce “ka yi babban kamu”

Bai ce uffan ba bai kuma kalleta ba, ba don tana ita ba, ɗiya ga aminin uban gidansu da sai dai ta hangi wucewar rigarsa ba kuwa zai dakata don wani ba yanda yunwa ke nuƙurƙusar ƴan hanjinsa.

“Ɗago idanunka ka kalleni, na maka alƙawarin farin cikin duniya muddin ka bi umarnina na yau kawai” ta ƙare idanunta kan ƴammatan da duk hankalinsu ya dawo kansu, suna jiran ganin yanda za ta kaya tsakanin Laila da Sultaan da ta dage musu ya furta mata kalmar so a daren jiya, bai ko yi gezau, bai kalleta ba bare ya bi umarninta, a hankali ya fara ƙoƙarin raɓawa ya wuce ta gefenta, hannu ta saka cikin fushi ta riƙesa ta kafesa da idanunta da suka yi ja ta ce “wai me kake ji da shi?, Bawa ƙasƙantacce ni za ka gwadawa girman kai?”

Ƙoƙarin janye riƙon da ta yi mai ya fara don shi kansa har ya fara ciwo wannan hayaniya da ta cikasa da shi, caraf ta riƙe D ɗinsa ta ce “sai na murɗe lalataciyyar abar in ga da uban me za ka yi tunƙaho har a kiraka da sunan namiji”

Take fuskarsa ta yi ja, idanunsa da ke ƙasa sun masifar canza launi, jijiya ta fito masa raɗau a saman kansa, a fusace ya janye hannunta ya watsar da ita saman yashin da ke ƙasa ya wuce batare da ya ce mata uffan ba.

“Namiji a tsaye amma ta ciki fanko ne, bai da maraba da mace, hoooo!” Ta ce cikin ɓacin rai, ganin ya ƙi ko dakatawa bare ya saurareta ga ƙawayenta sun fara dariya ya sa cikin ɗaga murya ta ce “ƙasƙantaccen bawa, zan sa mahaifina ya siyeka ranar Lelu in kuma sa a maka tsirara a ɗaureka a bishiyar cikin gari kowa ya ganka, na ga ƙarshen izza!” Ta ce cikin ɗaga murya

Duk da ya ji ta, ya yi banza da ita don ya san barazanar banza ce, yarinyar ko kusa ba ta burgesa tuntuni, ga ta da surutu kamar Aku, ga shishigin masifa, ga rashin kamun kai. ” LELU!” Ya furta tare da jan dogon numfashi, in akwai abin da yake tsoro bai wuce wannan rana ba, ga shi kwanaki biyar kacal ta rage ta zo musu. Da wannan tunanin ya faɗa gida bakinsa ɗauke da sallama

Zaune ya samu ƙanwarsa Halime saman tabarmar kaba tana saƙi da kwarashi, da hanzari ta ajiye ta kama masa ya sauke barewar bakinta da fara’a ta ce “yau zan ci nama har na ƙoshi”

“Ina Ama?” Ya tambaya

“Ba ta dawo ba” ta ba shi amsa tana nufar randar ruwansu, ta ɗebo masa a ƙoƙo ta kawo ta ajiye saman tabarmar kabar da ya zauna, sannan ta koma ta ɗebo madara fara ƙal daga randar da suke ajiyewa, a cikin tasa da sanyinta ta ajiye masa tana cewa “sannu”

Bai tankata ba ya ɗauki madarar ya kafa kai, bai sauke ba sai da ya ji cikinsa ya ɗauka sannan ya cire bakinsa ya goge ya sha ruwa yana cewa “Alhamdulillah!”, Kallon Halime ya yi da ta kafesa da idanu ko ƙiftawa ba ta yi, matsananciyar damuwa kwance a fuskarta, duniya in da abin da ya tsana bai wuce abin da zai taɓa rayukan mutane uku ba, Ama,Aba da ƴar ƙanwarsa Halime, hakan ya sa ya dubeta ya ce “me?”

Hawaye suka zubo mata ta share sannan ta dubesa ta ce “saura kwana biyar, ko mu samu ƴanci, ko mu tarwatse bautar gobe ta fi jiya, ga dafi a zuciya, ina cike da tsoro da zullumin wannan rana, gani nake nasara ba ta mu ba ce a wannan karon musamman in ka yi duba da lalurar da ta samu Aba”

Ya shaƙi wata iska wadda har ɗacinta ya ji a maƙogwaro, shi ɗin ma a matuƙar tsorace yake, musamman in ya duba yanayin jikin Aba da cututtuka suka yi wa rubdugu a halin yanzu dalilin tsufa, bauta ba ta yi ba, musamman irin wannan, ya yi tirrr, ya tsine wa wanda ya ƙirƙiri gasar Lelu don tsagwaron zalunci ce, ya sani ko su yi nasara ne, ko a yi nasara akan su, abu ɗaya ya riƙe shi ne duniya babu wanda zai…

Leave a Reply

Back to top button