TUBALI Page 1 to 10
“In sha Allah zan iya”.
Da sauri ya kalleta.
Kai ta jinjina alaman.
“Yess zan iya”.
Kai ya jinjina kana yaci gaba da cewa.
“Sai umarni na karshe, dole a nemishi, ya zama next 2 week’s dashi za’ayi hira. Kinga kenan yau saura kwana goma kenan.”.
Asiya ce dake masifar son amsar ragamar program ɗin daga hannun Jannart.
Ta gyara zamanta tare da cewa.
“Sir waye ne shi? A ina yake?”.
Cikin ɗan ɗaga sauti yace.
*”Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara ne”*
Da sauri duk suka fara kallon juna, cikin kaɗuwa Aisha Lawal tace.
“Sir Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, shifa…”
Hannunshi ya ɗaga mata tare da cewa.
“Na sani, shi ba mutum ne kamar kowaba, ra’ayin shi da banne.
Ko BBC bata taba samun nasarar yin hira dashi bako!?”.
Da sauri kab suka amsa da.
Yess! Yesssss!!”.
Ajiyan numfashin ya sauƙe tare da cewa.
“Toh wannan itace nasararmu in har an samoshi.
Zai zama mujallar Arewa ce zata taɓa fidda hirarshi da hoton fuskarshi kana, Arewa 24 TV ce zata taɓa haska fuskarshi da surar jikinshi bayan sunanshi daya zama sananne a Africa baki ɗaya.
Wannan shine zai ƙara ɗaga darajar shirin.
Shin Jannart zaki iya? Ko dai kai tsaye asa Asiya?”.
Da sauri Asiya tace.
“Sir Ni zan iya, tunda bani da wani tsaron nuna isar cewa ni ƴar wanice, aikina shine isata”.
Mafi akasarin mutanen wurin ido suka zuba mata ganin yadda take mgna tana watsawa Jannart harara.
Ita kuwa Jannart glass din idonta ta gyara tare da ɗagowa jin shugaban nasu na cewa.
“Jannart zaki iya ko dai yanayin tsaron da mafahifinki ke baki bazai barkiba?”.
Cikin sanyi da danne fargabarta tace.
“Sir zan iya in Sha Allah. A bani kundin bayaninshi”.
Ajiyan zuciya Salman ya sauƙe jin cewa ta amsa zata iya, baya son rasa abokiyar aikinsa sabida yana jin daɗin aiki da ita.
A’isha Lawal kuma ajiyan zuciya ta sauƙe.
Shi kuwa MD’n su, wani file mara girma ya tura gaban Jannart tare da cewa.
“Gashi sai dai babu komai nashi a ciki, sai sunanshi, da sunan Company’s ɗinshi, da garuruwan da suke. Da Hospital’s ɗinshi. Da kuma foundation ɗin sa, mai suna Mainasara Foundation.”
Jin yayi shiru ne yasa ta ɗan kalleshi kana a hankali tace.
“Ba phone number ɗinsane, ba picture dinsa? Ba address ɗin sane?”.
MD ne ya ɗan gyara zamanshi tare da cewa.
“Toh Jannart ai da akwai waɗannan abubuwan a ciki, toh da bazaiyi wuyar samuwa ba kuma da bazai zama mutum na musamman ba, kunsa duk abinda yake killace shine special.”
Sai kuma ta juyo ta kalli mai kula da shirin nasu dake cewa.
“Babu number sa, ba hotonsa ba adireshinsa. Kana ko akwai number sa, ko sau 1000 zaki kira da layuka 1000 ma-ban-ban-ta bazata shigaba, sabida yana amfani da App ɗin nan da in dai bawai yayi saving number ki a wayarsa bane, kiran bazai taba shigaba.
Kuma koda ya ajiye ya shiga, zaki kira a ƙalla sau goma bazai amsaba, sai dai ace mikin ki ajiye mishi voicemail.
Sabida yawan aiyuka da uzurrukan da mahaifinshi ya ɗaura masa yasa bashi da isashen lokacin kansa ma, da yawan mutane suna matuƙar jinjina masa da mmakin kwazonsa, sabida aiyukan sun mishi yawa, kana matashine a tsakiyar dattijai.
To shiyasa bai cika samun lokacin amsa kiraba.
Sai dai a ajiye mishi saƙo, so nanne zakiji muryarsa, idan abinda ke tafe dake mai mahimmanci ne, kuma kinyi hikimar faɗa mishi number ki to shida kanshi zai kira”.
Mafi akasarin su ajiyan zuciya mai nauyi suka sauƙe.
Cikin karaya Jannart tace.
“My Aunty to Ina kikaji duk wannan bayanin?”.
Dariya Hajia Rabi’ah tayi tare da cewa.
“Jannart yar jaridar gaske wato, tuni har kin fara binciken tun yanzu a kuma kaina”.
Murmushi tayi tare da gyaɗa kai.
MD kuma kai ya jinjina sabida gamsuwa da hikimarta da nitsuwarta wurin aikinta.
Cikin girma Hajia Rabi’ah tace.
“Toh gsky nima wurin PA’nsa na samu wannan bayanin.
Ba kuma wurin PA din kai tsaye ba.
Akwai ɗan yayata, abokin ƙanin PA’n nashi ne, so nan naji wannan.”
Cikin sauri ta miƙawa Hajia Rabi’ah wayarta tare da cewa.
“Samin number ɗan yayar taki”.
Murmushi tayi ta amsa tasa mata number.
Kana tace.
“Sunanshi, Mahmoud”.
“To” tace kana ta adana number.
Shi kuwa MD’n gyara zamanshi yayi yaci gaba da tsara musu sauye-sauyen programs ɗin nasu.
Sai kusan ƙarfe shida saura suka tashi a taron.
Suna fitowa, mafi akasari suka kama hanyar parking lot ɗinsu dan daukan ababen hawansu.
Wani irin kallo mai cike da tsana Asiya ke bin Jannart dashi lokacin da suka fito, a take Escort ɗin ta suka miƙe suka mara mata baya.
A hankali ta ɗan juyo jin Aisha Lawal na kiranta.
“Jannart! Jannart!!”.
Juyowa tayi tare da bin tsakiyar hanyar da suka buɗa matan.
Da sauri A’isha Lawal ta iso, cikin sanyi tace.
“Zaki iya?.”
Cikin jin tsoron rasa aikinta, ya zama dole taita zaman gidan da yafi na kurkuku muni da zafi.
Tace.
“Na’am A’isha zan iya, in sha Allah. In ban iyaba naci gaba da zaman gida, Yah Junaid zai k’arasa kurmatani da marukan da yake yayyarfa min a cikin ko wani mintuna, wurin aikin nan shine duniyata, shine TUBALIn ɗan y’ancina, ya zanyi sakacin rasa aikina”.
Cikin rauni da ƙara yin ƙasa da murya Aisha tace.
“Okay Salman yace ince miki in sha Allah zaku iya, kuma zai roƙi a baku cikekken dama, da zai biyoki sai ya tuna waɗannan kattin dake zagaye dake wanda suke shirye da ilkata duk wani na miji in yazo kusa dake”.
Kai ta jinnina kana sukayi sai anjima.
Wasu dalla-dallan motoci ne guda, uku.
Ta tsakiya itace a baya.
Ta baya kuma ƴan tsaronta, hakama na gaba.
Tana baya a zaune.
Yayinda driver’n ta ke janta.
A haka suka nufi gida tana mai jin tsoron me zata riska a gida, kasan cewar ta wuce lokacin dawowarta.
Anguwa ce mai zaman kanta Janbulo tsit anguwar ba hargitsi, da hayaniya, da kwata kamar ba cikin kano ba, sabida manya-manyan gidaje ba irin gidajen kanawa mitsi-mitsin nan ba.
A bakin wani tamfatsetsen gida mai ɗan karen girma da kyau, suka tsaya tare da danna hon.
Jiki na rawa mai gadi ya buɗe musu.
Nan suka ratsa cikin gidan.
Suna isa parking space ana kiran sallan magriba.
Wanda yayi dai-dai da fitowar Alhaji Idi Sale Dakata daga cikin gidansa tare da zaratan samari uku Junaid Azeez Abdul a bayanshi.
Da wani mutum wanda suke kama da juna Barrister Kabir Saleh Dakata kaninsa kenan.
Wata iriyar sassayar ajiyar zuciya mai nauyi ta sauƙe fahimtar Yah Azeez zai koma wurin aikinsa dan taga ana sa kayansa a mota, alamun ana idar da salla zasu wuce Airport dashi.
Murmushi Barrister Kabir yayi tare da cewa.
“Masha Allah, Ammina kin dawo kenan”.
Da sauri ta matso kusa dashi tare da kaucewa mugun kallon da Yah Junaid ke watsa mata, cikin sanyi tace.
“Eh Abba na dawo, ina Aunty Dija”.
Ta k’are mgnar tana kallon fuskar Yah Azeez d’in da yakeyi mata kallon mai cike da tausayawa,
Barrister Kabir kuwa wanda ta kira da Abba Cikin kula da tsananin tausayinta da danne wani abu can ƙasan zuciyarsa yace.
“Suna ciki shiga bari muje masallacin”.
Da sauri tace to.
Kana tayi cikin gida su kuma suka nufi masallaci…
*Ethiopia Addis Ababa.*
Wani kyakkyawan matashine mai wani irin tsabtaceccen kyau mai masifar ɗaukar hankali, matashine mai jini a jika.
Wani irin kimtsestsen taku mai cike da nagarta, nitsuwa, kamala, haiba, yakeyi, yana mai fitowa habarar wani kyakkyawan Asibitin.
(Tikur Ambess Teaching hospital Addis.)
Yayinda wasu manyan likitocin da ƙasar Ethiopia ke ji dasu ke biye dashi a baya, kana da Nurses.