TUBALI 1-END

TUBALI Page 1 to 10

               *AYSHA ALIYU GARKUWA*

“Hausa ya keyi fa ko?”. Cike da kaɗuwa Sulaiman yace.

“Eh abinda ya ban mamaki kenan.” 

Sai kuma ya kalleta jin tana cewa.

“Koda yake ba mamaki  wani ne ya rubuta mishi, tunda kaga ai yace.

Ethiopia Addis Ababa to Nigeria kano State. Kanawa zan zo muku.

Wata ƙil wani ne ya rubuta mishi”.

Komawa yayi da baya ya jingina bayanshi da jikin kujera. 

Numfashi ya ɗan fesar tare da cewa.

“Kai Sumayyah gsky da mamaki fa.

 Kalli Comments ɗin mutane fa da amsar da yake basu.”

Ya ƙare maganar yana shiga  comments section ɗin ƙasan video’n da ya saka a shafin nasa.

Inda wani Abis Fulani yake cewa.

“Eyyeh Riyyam-nsra a Nigeria, kanawa nama fatan isa lfy”.

Cike da mamaki Sumayyah ta kalli amsar da ya baiwa Abis Fulani.

“Ngd aboki na”.  da alamun musabaha.

Sai kuma tayi ƙasa ganin inda wani.

Ahmad MG ya fara mgn da zaro ido alamun mamaki tare da cewa.

“Riyyam-nsra da yin Hausa, ko mafarki nakeyi”.

Dariya yayi tare da bashi amsa.

“Noh Ahmad zahiri ne”.

Tofa wannan abun yasa comments ɗin mutane zubowa kamar ruwan sama domin shi dai ɗan ƙasar Ethiopia ne, kalarsa, harshensa, cimarsa, rayuwarsa, komai na canne, bai taɓa koda maganar Nigeria a shafinsa ba, sai gashi yau kuma yayi video cewa zaizo Nigeria, kuma yana rubutu da hausa yana kuma karantawa.

Cikin kaɗuwa Sumayyah taci gaba da bin comments ɗin mutane na farko-farko da ya iya basu amsa sabida yawan mutanen.

Cikin mamaki tace.

“Lah kalli tambayar da wani ya mishi.”

Amsar wayar Sulaiman yayi.

Ya fara duba saƙon da Imran yayi mishi.

“Riyyam-nsra kasan Nigeria ne? Ko Ka taɓa zuwane? Ko wannan ne zuwan da zakayi na forko?”.

Alaman murmushi yasa tare da cewa.

“Nasan abu da yawa kan Nigeria”.

“Da sauri yace gaya min kaɗan daga ci.”

“Ok kamar me kake son in gaya maka”.

Da sauri yace.

“Ka iya taken ƙasa. Ko rantsuwar al’ƙawarin ƙasa.”

Cikin lumshe ido, Riyyam-nsra dake kwance a ɗakinsa.

Ya rubuta mishi amsa, da bari in baka amsar a video.”

Take kuwa ya tashi zaune yayi taken ƙasarmu Nigeria ƙasarmu ta gado kana da rantsuwar al’ƙawarin ƙasa.

Wannan video da ya saki 

Yayi matuƙar jan hankali al’ummar Hausawa duniya baki ɗayansu more Especially ƴan Nigeria bama ya kanawa.

Da sauri Sulaiman ya fara rubutu.

A karo na forko a rayuwarsa da zaiyiwa wani comment a TIKTOK.

Rubutu yayi cikin harshen nasara.

“Hey Riyyam-nsra you knew much about Nigeria you are a patriot”.

Yayi mgnar da gayya ne dan ya gano ko dai ɗan Nigeria ne basaja ne da karya yasa yake ciwa ɗan Ethiopia ne, wata ƙil karatune ya kaishi can.

Murmushi yayi tare da rubuta mishi amsa.

“Baƙon Nigeria dai mai kishin Nigeria amman ni ɗan Ethiopia ne.

Sai dai Nigeria ƙasar babban abokina ne da mukayi karatu tare a US.”

So daga ganin wannan video, akai ta cewa.

“Haba shi yasa mana.

Nasir Ahmad ne wanda shine abokin nashi ya fito, yanata mishi tsiya a nashi shafin. Nanfa aka gane sanadin zuwansa da kuma inda ya koyi Hausa ras.

Ɗan gajeren tsaki Sulaiman yayi tare da cewa.

“Wadannan yaran gaba ɗaya TIKTOK ta haukata mana matasa wanda sune TUBALIn al’umma sai gashi kuma muɗin ma suna shirin haukatamu”.

Dariya Sumayyah tayi tare da cewa.

“Dama haka ai Rayyern ɗin ke ce maka, in baka dena biyewa social media ba, zaka rasa lokacin kanka”.

Kwaffa yayi tare da rufe datarsa kana yace.

“Nima fa Ibrahim ne ya sani fara wannan abun sabida, kamannin Rayyern da wannan yaron.”

Daga nan sukaci gaba da hira kan kamanninsu.

Washe gari da safe ranar talata.

Gidan Alhaji Idi Sale Dakata.

Su kusan shida ne cikin falonshi.

Wanda huɗu daga cikin manyan yan kasuwane masu faɗa a ji masu juya sule ta koma million ɗaya ko tako wanne irin halin ƙaƙama ko talaka zaiji daɗi haka ko bazai jiba.

Biyu daga ciki kuma ƙusoshin gwamnati ne masu ƙarfin iko daga ta jiha zuwa ta ƙasa.

Alhaji Yawale ne ya gyara zamanshi tare da cewa.

“Yaron nan fa yanayi mana illa ba tare da mun ankare ba.

Gaba ɗaya ya rarake tubalin da mukayi tsawon shekaru muna ginawa muna samun wuri na jawo mana wuri.”

Cikin tsananin takaici Alhaji Abdu Tababa ne yace.

“Tun-tuni nake gaya muku haka.

Mu kauda yaron nan a doron ƙasa shine kawai mafi sauƙin mu.

Kunaga yadda kasuwan cinsa ke haɓaka,  kamfanonin sa suna bunƙasa daga Arewacin Nigeria har ya koma kudanci ya kafu.

Uwa uba yanzu duk ƙasashen  Afrika yanada rassai.

 Ya maida kayan abinci da araha tamkar ruwan sama cikin damuna.

Duk inda ka shiga a kasuwannin Mai-nasara race, ke cike.

A farashi mai sauƙi ta yaya za’ayi a saurari kayan kamfanonin mu”.

Ɗaya daga cikinsu ne ya miƙe tsaye tare da cewa.

“Ni tambaya ta a kullum ma shine

menene Tubalin kasuwancin yaron nan?

Yaushema aka haifeshi? Sa’an yaran cikin mune fa!

Ta ina ya samu Wannan tarin dukiyar da har ya samu damar razana mana kasuwanci ya raunata mana Company’s.

Yaushe yayi ginin duk a lokacin ɗaya menene Tubalin dukiyarsa da matakan ikonsa!?.”

Ya ƙare maganar yana kallon Bala Tambari wanda shine shugaban tsare-tsaren ginin masana’antu a gwamnatance, dole sai yasa hannu za’ayi gini  ya za’ayi ka bashi izini da damar yin gini a duk inda yake so a ƙasar nan”.

Cikin takaici Bala Tambari ya fesar da numfashi tare da cewa.

“Tsohon yarjejeniya ne, yana da dukkan abin buƙata, yanada sa hannun da suka gabaceni kuma kan tsari suke.

Naso in ƙalu balanceshi.

Tun shekaru biyar baya lokacin da ya fara gina babban campany dake Nan birnin Kano wanda yanzu yake gab da kammalashi so naga komai da hujja yakeyi.

Yaron shegen taurin kai ne dashi, gashi da ɗan banzan tsaurin ido.

Kana mgna zai tsira maka waɗannan siraran idanun nashi masu kama da soyayyan gujjiya, tsakar idon ka ya baka amsa da hujjar da baka isa kayi mgna ba”.

Dr.Lukman ne ya fesar da iska a baki tare da cewa.

“Ni ta ko ina ya tosheni

A fannin likitancin gaba ɗaya yana bi yana rarake privet Hospitals.

Ɗan banzan komai na asibitinsa mai sauƙi kuma ga kula ya za’ayi aje irin namu asibitocin.”

Alhaji idi Sale Dakatane ya miƙe a fusacen shina kana yace.

“Nifa gaba ɗaya ya ta’azzara min campany na na shinkafa.

Sannan kafin kace ka motsa sai ka samu ya toshe ko ina.

Hegen yaro mai jajayen kunnuwa.

Yana nan tamkar Wahainiya, samun ganinshi ma ya zamewa mutun aiki.”

Dr Lukman ne ya ɗan sauƙe numfashi tare da cewa.

“Cikin satin nan zai dawo Nigeria yanzu haka yana Ethiopia yaje, shugaban kasar can da kanshi da manyan likitocin sune, suka karrama shi.

Sabida taimakon da yayiwa wasu daga cikin mutanen ƙasar Ethiopia cikin Airport kan hanyarsa ta zuwa US, dan karramashi a matsayin ɗan kasuwan da yafi ko wanne sauƙin farashin kayan masarufi.

Kaga yana tafi kuma yazo wai kuma Ethiopia zasuyi mishi wata karramawar.

Yaro kamar ɗan ruwa, komai yasa kai sai Nasara”.

Bala Tambari ne, ya kalleshi tare da cewa.

Toh yanzu dole kai zaka nema mana zama dashi.

Yana dawowa muna buƙatar shi mu gwada sayan farashinsa.

Muyi mishi tayin harƙallarmu yasan irin ribar da muke shigarwa, wata ƙil zai amince mu haɗa hannu in kuma yaƙi tabbas zamu gina mishi gadar zare.”.

Da sauri Alhaji Idi Sale Dakata yace.

“Uhumm ai In Kuma yaƙi amincewa mu haɗa hannu.

Toh lokacin wasan zai fara, dan in taurin kaine da gsky da samun ƙarfin iko bai kai.

Mai-gaskiya da wasu ba, da muka gama dasu shekaru ashirin da biyu baya ba, danni cinnaka ne ban bar na gida Bama, bare shi baare.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7Next page

Leave a Reply

Back to top button