TUBALI Page 1 to 10
Haka dai suka tashi a taron nasu.
A nufin sai ya dawo su zauna dashi.
A cikin gidan kuwa. Jannart ce ke
Tsaye a kitchen, inda take sanye da wani half gown mai masifar kyau wanda ya d’an bayyana fararen legs d’inta, rigar irin mai kauri da kama fatar jiki dinnan ne, wanda hakanne kuma yasa had’add’iyar Surar jikinta dan bayyana, kasancewarta y’ar gayu, Tabbas Jannart macece mai matuk’ar son fashion, shiyasa hatta suturun da take sawa ya banbanta da sauran na y’an Nigeria, saboda sometimes tafi yin shiga irin na wasu daga cikin larabawa, ko kuma shigar mutanen turkey????????.
Tsaye take a kitchine din cikin kuma nutsuwa take aikinta.
Yayinda Mom ke tsaye a gefenta.
Cikin kula Mom ta kalleta tare da cewa.
“Jannart kamar Yayanki ne ke kiranki”.
Cikin bugawar zuciya tace.
“Yah Junaid!?.”
Da sauri tace.
“Eh shi dai”.
Bugawa zuciyarta ya kumayi, tare dajin wani iri acikin jikinta, saidai kuma babu yanda ta iya, haka ta juya cikin sanyi ta nufi falon.
Can tsakar falon ta hangoshi tsaye, saurayi ne, mai murd’addiyar Surar jiki da kuma tarin gashi akansa irin busu-sun nan, duk da cewar kyawun nasa bawani na zarce hankali bane amma baza’a tab’a k’iransa da mummuna ba, wata riga
marar hannuce ajikinsa, sai kuma wondon dake jikinsa wanda ya tsaya masa iya guywa.
Bisa alamu kuma yanzu ya tashi daga bacci.
saboda yanda idanunsa sukayi jazir.
Kallonta yayi, tare kuma da d’an cije labb’ansa, still Cikin binta da wani irin mayataccen kallo yace.
“Kije ki share min ɗakina”.
Fuskarta ta d’an b’ata cikin kuma tsanar shiga ɗakin nashi tace.
“Yah Junaid breakfast nake haɗa mana”.
A fusace ya juyo kanta cikin takaicin abubuwan dake haɗe mishi a kanta ya yarfa mata wani irin gigitaccen mari a kan kunneta na dama, saida ya bada wani irin sauti ƙauuuuu! Da ɗan karen ƙarfi.
A gigice tasa tafin hannunta ta tallabe ƙuncin ta.
Yayinda wasu taurari suka fara gilma mata a gani.
In da sabo yaci ace fuskarta ta saba da marukan Yah Junaid Wanda tun tana yarinya take shansu gashi sanadin su, kunnuwanta sun samu matsala jinta ya raunata.
Wasu irin hawaye ne masu masifar zafine suka silalo mata.
Ba tare da tace komaiba ta juya ta nufi ɗakin shi.
Ta yaya zuciyarta zata samu sauƙin ɗan uwanta da take bata da wani sama dashi tunda shine suke uwa ɗaya uba ɗaya amman yafi kowa tsanarta a duniya.
Ba shaƙuwa ko tausayawa a tsakaninsu.
Sannan mahaifinsu babu ruwanshi ko a gabanshi Junaid zai daketa babu ruwanshi sai yayi kamar baya wurin ma.
In Mom tayi mgna ya gwatsaleta yace babu ruwanta sunfi kusa.
Wannan ne ya ƙara tsananta zubda hawayen ta.
A haka ta fara tattara mishi falon da gaba ɗaya ya birkitashi.
Shigowa yayi ya zauna yana mai Binta da ido, duk inda tayi.
Wani irin abu yakeji a kanta.
A hankali ya miƙe yabi bayanta lokacin da ta shiga Bedroom.
Da sauri ta juyo jin shigowarsa.
Gefenta ya matso fuska a murtuke hakan ne yasa bugun zuciyarta ya ƙara tsananta.
Har kana iya ganin yadda numfashin ta ke fita da yanayin tsoro.
Fuska ya kuma murtukewa.
Kana yace.
“Munafuka, sai kace da gaske haka kike tsoron maza, ji yadda kike tafiya ba bra kina wani karkakaɗa ƙirji irin ke gaki ƴar iska mai son maza ko?.”
Idanunta ta rumtse da k’arfi cikin kuma ƙunan ran ƙazafin da Yah Junaid ke jifarta dashi murya na rawa tace.
“A’a”.
Cikin haɗe fuska ya daka mata tsawa tare da cewa.
“Toh meya hanaki sa bra?”.
Murya na rawa tace.
“Dr. Lukman ne yace in daina sa bra, sabida matsalar numfashin da Athsman ɗina ke jamin. In nasa ya matse min ƙirji sai numfashina yayi ta shaƙewa”.
Wani irin dogon tsaki yaja tare da cewa.
“Ubanki zanci in baki dena raina min hankali ba, matse ƙirjin da ƙatti keyi bai shaƙe numfashin ba sai saka bra ne zai cushe miki numfashin.”
Fice min da gani!!”. Ya k’are maganar a tsawace.
Jin hakanne kuma yasa da sauri ta juya ta fita, hawaye na zubo mata sabida raɗaɗin marin daya yarfa mata da zafin kalaman zargi da yake binta dasu.
A falo ta samu Mom da sauri ta faɗa jikinta.
Cikin sakin sassayan kuka tace.
“Mom ki gaya musu wlh ni ba yar iska bace, Meyasa Mom Meyasa Ya Junaid ke jifana da mugayen maganganu, shifa yaya nane..”
Jawo hannunta Mom tayi suka zauna bisa kujera, a hankali tasa tafin hannunta tana share mata hawaye cikin yin ƙasa da murya tace.
“Na sani Jannart kuma Allah ya sani, ke ba ƴar iska bace. Yaushe ma kika samu sakewar rayuwar duniya kullum kina cikin takunkumi.
Ko ina zakije da masu gadinki.
Na rasa wannan masifar tsaron na menene kina girma ana ƙara killaceki kamar abun rashin gsky.”
Cikin shessheƙan kuka tace.
“Mom shi Yah Junaid gani yake, su masu tsaron nawa dasu nake iskanci.
Daddy Kuma gani yake in ya cire masu tsaron da wasu zanyi iskanci.
Wlh na sani Mom bawai dan tsaron lfyata bane yasa Daddy ware min masu tsaro.
Shima zargina yakeyi ko Mom?”.
Jin yadda numfashin ta ke fitane yasa mom gyara zamanta kana ta fuskanceta da kyau.
Allah ya sani tana son Jannart tamkar ƴar cikinta.
Amman duk yadda zatayi bata burge Alhaji Idi da Junaid, gani suke kamar so take Jannart ta lalace ne don ba ita ta haifeta ba.
Cikin kula da tausasawa uƙubar da suke shayar da ita tace.
“A’a Jannart Daddynku baya zarginki, shi ya bada masu tsaronkine sabida larurar ciwonki, kina buƙatar makusanci a koda yaushe, tunda abu kaɗan ke tada miki athsman ɗin wanda kinga tun da yana nimoniya, kina girma yana canzawa ya riƙa har ya zama asman shiyasa yake tsananta kulawa a kanki.
Sabida abu kaɗan ke tada miki shi.
Kuma Yah Junaid ɗinki yana sonki.
Ɗan uwa, uwa ɗaya uba ɗaya ya wuce wasa.
Sun haɗa da son da Mamanki zatayi mikine da tana raye”.
Cikin zubda hawaye tace.
“Mom kin bani son da ya kamata uwa ta bawa ƴarta, ni banyi maraicin kyakkyawan tarbiyar uwa ta gari ba.
Kawai dai basa so nane”.
Cikin kafeta da ido Mom tace.
“Jannart ki yarda dani, tashi muje kici abinci”.
Cikin nitsuwa tasa hannunta ta share hawayenta kana ta miƙe.
Dinning area suka nufa.
Suna zama Daddy ya fito da hakama Junaid da Abdul.
Nan suka zauna sukayi breakfast.
A hankali ta sauke numfashi ganin Junaid ya miƙe ya bar wurin.
Sai kuma ta ɗan kalli Alhaji Idi Saleh Dakata.
Cikin takatsantsan da girmamawa tace.
“Daddy Ina son zanje gidan Aunty Rabi’ah akwai wani aikin da zamuyi a can”.
Ido ya ɗan zuba mata.
Ita kuwa da sauri tayi ƙasa da kanta.
Tana tasbihi cikin ranta, da addu’ar Allah ya ɗaurata a kanshi.
Juyawa yayi ya fara sauƙa kan steps ɗin tare da cewa.
“Kada ki daɗe.
Kuma ƙafarki ƙafarsu Sunday.”
Cikin sabo da hakan tace.
“Toh”.
Kana ta miƙe ta nufi ɗakinta. Mom kuma ta fara tattara kan table ɗin.
Wanka tayi cikin nitsuwa da kuma sauri-sauri.
Tana fitowa, ta zauna ta tsane jikinta kana ta busar da tattausan suman kanta.
Ta shafa mishi mayuka, sannan ta tubkeshi.
Mai ta ɗan shafa kana ta Murja farar hoda, tare dasa man baki.
Sosai tayi kyau duk da bata cika kwalliya a fuskarta ba.
Wasu tattausan riga da wondo pallazo farare ƙal ta zaro,
Sai wata doguwar riga budaddiya mai igiya a tsakiya.
pantie tasa, kana ta zira dogon wondon daya kasance yayi tightin fatar jikinta.
Dole sa bra baya cikin jadawalin rayuwarta sabida larurar ciwonta.
Sai dai takan sa rigunan su ɗan matseta.
Rigar ta zura irin mai wuyanan nane wato, high neck, naɗe wuyan tayi ta gyarashi.