Uncategorized

MATAR UBA 3

 ????????????????????????????????          *MATAR UBA* 

????????????????????????????????

       _(A True Life Story_ )

            *Short story* 

 “`Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)“` 

Follow me on Wattpad @milhaat

Join my group on Telegram

https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0???? *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* ????????️

 _(‘Kungiya d’aya tamkar da dubu)_ _____________________________

*MATAR UBA*  Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.

Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK*  much Love.

CHAPTER 3

????????????????????????????????????????????

………… “Maza ku daina kallo na ku wuce ku cire uniform d’in Nan kusa wani Kaya, kun tsaya Kuna kallo na da ido kamar na mayu.”

Ba musu suka haura sama Tace “Minti biyu na Baku ku kifo Kar ku wuce Nan, Wai mummy zamuje makaranta da wani kud’i za a biya muku? Mtssws” bayan sun fito ne ta d’aura musu talla.

Sun dad’e a yawon tallaan sai wajen karfe uku suka dawo gida.

Karb’an kud’in tayi Tace “Masha Allah Ashe Kuna da amfani” Nan ta Shiga irga kud’in sai taga naira hamsin da bakin sa ya d’an gutsire ta kalli kud’in dakyau Tace “Toh wannan Kuma waya cinye?”

Basu ce mata komai ba sai kallon junan su kawaii suke.

Tace “banda rashin hankali ma Kuna ganin kud’i ba kyau ku karb’a, ku Shiga Ciki Ku huta,idan Allah ya kaimu gobe tunda Kun sayar da wannan duka zamu sayo wasu”

Kallon Juna suka yi cikin Rawar murya Asiyah Tace “Mummy yunwa muke ji”

“Yunwa kuke ji?”

A tare suka amsa da “Eh yunwa muke ji”

Gyara Zama tayi Tace “Kuna nufin yunwa yunwa na cin abinci?”

Suka amsa da Eh.

Langwabe Kai tayi Tace “Allah sarki kun ga abin da nake fad’a muku Kenan Nima tun jiya banci komai ba”

Anisah Tace “mummy na kasa fahimtar abinda ke faruwa mun talauce ne ko me?”

Yar karamar dariya tayi Tace “Eh mun talauce Amma Alhamdulillah tunda muna raye, to yanzu ya zamuyi Kenan tunda Kuna Jin yunwa?”

Kallon ta kawaii suke suna rarraba idanu, Murmushi tayi ta sa hannu ta d’auko naira hamsin d’in Nan da ya yage tace “me wannan zai saya Mana muci tunda Allah ya had’a Ni da monkeys?”

Anisah Tace “Mummy Dan Allah ki Kira Daddy muyi magana dashi”

Tashi tayi Tace “Kina nufin na Kira mijina? Baku girma bane ta yanda zaku Rika fita Kuna neman kud’in da zakuci abinci? Wato na Kira shi?” tana maganar tana nuna kanta.

“Eh please call our Daddy he promise us that we will never lack anything”

A tsawace Tace “would you shut up your dirty mouth,I should call him kuce Masa me? Idan Kika kuskura Kika sake fad’a min magana makamanciyar wannan Anisah sai na karya ki”

Anisah Tace “But mummy…”

Katse ta tayi a tsawace tace “Get out from here useless children” tana maganar had’e da ture robobin da suka dawo dashi.

“Ku d’auki robobin Nan ku fice min daga gani”

A tsorace suka bar pallon.

A garden na gidan suka zauna Asiyah Tace “Anisah Dan Allah na roke ki wata alfarma?  ya kamata ki daina tan kamata idan tana magana”

“Meyasa kikace haka?”

“Sabida zata kashe mu wataran idan Kika cigaba da Mata Haka”

Murmushi tayi Tace “To Asiyah me banbanci mu da matattu, ba abinci, ba zuwa makaranta muke ba, ba kayan sawa kin San duk ta Kona Mana su,ba Uwa ba uba, har yaran da suke gidan marayu sun fimu da komai, to me Kuma ya rage? A raye muke dai Amma ta kashe mu”

“Na San da hakan Anisah Amma ya kamata ki d’auki magana ta Kinga nice gaba dake ko?”

“To shikenan zanyi yanda kikace”

Asiyah tashi tayi tace “Yauwa ko kefa Tashi muje muyi sallah muyi Shirin zuwa islamiyya”

“Gaskiya ni bazanje ba jiri ma nake ji Ina sallah zanyi bacci”

“To shikenan Nima baccin zanyi kawai.”

Ganin ta nayi ta fito daga kitchen hannun ta rike yake da plate, fried rice ne aciki da cinyoyin kaji manya manya, d’ayan hannun Kuma kwalin Hollandia ne, Kai tsaye dinning table ta nufa tana ajiye plate d’in wayan ta ya Fara ringing tana picking ta amsa da “Hello qawata”

Bayan sun gaisa Tace “Ke dai Bari kawai qawata nayi duk yanda zanyi Amma shiru kike ji na rasa meyasa ban haihu ba sai faman bauta nake wa yan iskan yaran Nan.”

Tana d’an yi shiru da alama tana Mata magana Wanda Ni na kasa ji sai ji nayi Tace “Ai wallahi Ina haihuwa Zan Kori monkeys d’in Nan a gida na, Kema kin sanni ai wallahi ba ruwana da inda zasu je suma mutu Mana”

“Okay to shikenan ki gaida min ‘yarki” kashe wayar tayi ta cigaba da cin abincin ta, suna shigowa suka tarar da ita ta na yagar nama ganin suna kallon ta banka musu wata muguwar harara had’e da fad’in “baza ku bar Nan ba?”

Da saurin gaske suka bar gun, a Haka suka kwana da yunwa sai Ruwan da sukayi ta Sha.

Yau ma tun safe suka fita don sayar da lemo da pure wata.

Wata bakar motar na gani kirar Benz tazo ta gifta su.

Cikin motar wata yarinya sa’ar su Asiyah tana kallon su Asiyah cike da mamaki  Tace “Mom ya akayi na ga su Asiyah suna tallah?”

Murmushi tayi ta Maida hankalin ta sosai Kan tukin da take, sai Tace “Toh mene ne aciki don sunyi tallah akan su aka Fara ne?”

“Toh Amma Meyasa Ni bana yi”

A tsawace Tace “yimin Shiru Allah ya raba ki da tallah, Suma d’in kaddara ce kuma Kar naji kin sake fad’in Haka, kuma kar ki fad’awa kowa kina jina ko?”

“Toh bazan fad’a ba”

Shafa kanta tayi Tace “Yauwa Yesmiin  ‘yar Albarka,Bari nayi sauri nayi dropping d’inki a makaranta Kar ki makara ko?”

Tace “To mommy”

Sai yamma liss suka gama sayar da komai da komai babu abinda ya rage, a galabaice suke tafiya Asiyah Tace “Anisah har yanzu zazzab’in Bai sake ki ba?”

Cikin kasala Tace “Eh jiri nake ji, ji nake kamar zan fad’i”

“Sannu bari na rike ki, mun ma kusa Isa gidan” rike ta tayi suna tafiya Kan ta Ankara Anisah ta zube a kasa, ihu Asiyah ta Fara yi tana kuka tana neman taimako dake a GRA suke unguwan Shiru ba kowa ta dad’e a Haka Kan ta hango wasu Samari su biyu da gudu suka nufota, d’aya daga cikin su yace “Me ya same ta Haka?” Cikin kuka tace “Suma tayi”  chaak ya d’aga ta yace “Ina ne gidan ku?”

Tace “Yana chan ba nisa daga Nan” da gudu suka kaita gida Amma sukayi rashin Sa’a Baraka ta fita yawon gantalin ta da ta Saba, Asiyah ta musu godiya har parlor suka aje ta Kan suka tafi.

Ruwa ta d’ebo a roba tana sawa tana Kama Mata jiki don jikin ta yayi zafi sosai suna cikin hakan ne ta dawo tana ganin su tace “Ita Kuma wannan me ya same ta?”

“Sannu da dawo wa mummy ba ta da lafiya ne ya kamata akaita asibiti?”

Hard’e hannayen ta tayi ta ce “Asibiti? Kuma ana bukatar kud’i?”

Tace “Eh ai ya Zama Dole?”

Harararta tayi Tace “Dole? Cancer take dashi ne?”

Murya kasa kasa tace “A’a.”

“Good to bani da kud’in kaita asibiti”

“Toh mummy Dan Allah ki ara min wayar ki na Kira Daddy”

A tsawace Tace “bazan bayar ba, harda wani ya Zama Dole to ta mutu Mana ina Ruwana Kun ma ci Sa’a ban d’auke ku naje na sayar daku ba, useless children”

Tana maganar tana haurawa sama.

Cikin kuka Anisah Tace “So take na mutu”

Asiyah Tace “Shhhh Karki ce Haka baza ki mutu ba Allah ya baki lafiya tashi Muje ki kwanta a d’aki.”

Dakyar ta d’aga ta dake ratar shekarunsu kad’an ne Asiyah shekarunta Tara Anisah Kuma Bakwai sannan Anisah ta d’an fi Asiyah kauri, upstairs d’in su na da tsawo da kyar suka haura sabida gidan babba ne kud’i ya zauna anan.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button