TUN KAFIN AURE Page 21 to 30

Senator Rufai dai bai iya basu amsa ba ya fito ya shiga mota kafin a tayar Junaid ya fito da gudu ya shiga shima. Yana zama senator yace sai ka kwatanta wa Bulus hanyar gidansu yaron. Yaron kuma Alhaji? Ba nema min auren zaka yi ba? Junaid just do as you are told kaina har ciwo yake. Ba gobe ne daurin auren ba? No sai saturday.
Alh Bashir ya sake gaishe da senator sai yayi mamakin ganin da kansa ya taso ya bashi hannu. Bayan sun gama gaisawa yace ni sunana Rufai Bukar. Ranka ya dade ai tuni na ganeka ni sunana Alh Bashir. Senator ya kalli Junaid dake zaune kan kujera ba zaka gaishe shi ba. Nan take ya sauko ya gaishe shi. To nasan zaka yi mamakin ganina tare da dana a gidanka ba tare da an sanar da kai ba. Haba ranka ya dade ai nasan dole ce ta sa. To akan maganar yarona ne Junaid… ..haka dai senator ya labartawa Alhaji komai na halayyar dansa da Hafsa da ya gani yana so. Ikon Allah kawai yake fada sannan yace idan na fahimci inda zancen ya dosa so kake Saifullahi ya hakura kenan. Hular kansa ya cire ya dago kai idanunsa da kwalla Alhaji ina tsammanin Allah baiyi maka jarabawar haifar dan da….kai Junaid ku fita. Suna fita ya cigaba da magana wadda sai da hawayen da yake kokarin boyewa suka zubo. Junaid yaro ne me hazaka tun kuruciya amma yanayin aiki da jindadin kudi yasa na sangarta shi. Yaronnan ya janyo min magana fiye da yadda baka zato ga shaye shaye ga….da dai sauran aikin sabo. A bisa amana nake fada maka sirrina Alhaji wallahi wallahi mulki da kudi jarabawa ne sosai daga Allah. Ban farga da munin share lamuran yarana ba sai da naji waazi daga bakin wasu malamai kamar su Daurawa, Kabir Gombe dasu Dr Sani Rijiyar lemo. Nasan nayi barna mara iyaka har ina tsoron ranar mutuwata. To a yau bani da burin daya wuce yaron nan ya shiryu ina ganin wannan zai zama sanadiyar samun rahma a gareni. Da gaske mutumin nan kuka yake Alhaji Bashir ya fada a ransa ganin hawayen senator. Naji dukkan bayaninka ranka ya dade amma yarinyar ba tawa bace. Na sani kuma nasan haramcin nema akan nema. To idan haka ne ko zaka yarda na kira mahaifinta dashi yaron. Ai mai nema ke bi kayi mana jagora gidansu kawai.
********************
Baffa don Allah ka yafe min nasan nayi kuskure wanda bana fatan sake maimaitawa. Hmm Hafsatu kenan ki sani kaza tana taka danta ba don bata sonshi ba sai don ta koya masa hankali. Hakika muna cikin wani zamani da ake tallata zina kamar kayan miya, wanda bai siya ba ma kallon banza ake masa. Amma ina so ke da ku ma…ya kalli Amira da Anisa lallai ku tuna wutar Allah mai radadi ce kuma baya bata da kadan. Sai ka aikata abu ka manta ma dashi watarana ya dawo ma lokacin da baka tsammani. Ki je na yafe miki Allah Ya yi muku albarka. Da farinciki suka tashi dukkansu balle ma Hafsi zuciyarta fes fes. Suna fita Alh Bashir ya kira Baffa ya sanar dashi zai zo gidansa da baki nan da lokaci kadan idan yana gida.
Batul Mamman????
TUN KAFIN AURE????17
Sakin baki Baffa yayi yana kallon Alh Bashir, Senator Rufai da Saif. Wane irin rainin hankali ne suka zo masa dashi. Gyara zama yayi ya kalli Alh Bashir…yanzu kana nufin ranar asabar da wani zaa daurawa Hafsa aure ba da Saifullahi ba? Wai ni Alhaji me kuke nufi da ni da iyalina ne? Akan hoton da yaron nan ya sa Hafsa taje suka yi babu abinda banyi mata ba karshe kuma sai kawai kace min daban yana son aurenta kuma ka amince. To kai ma ka amince ne? Ya tambayi Saif. Sunkuyar da kansa yayi kasa. Shi kam kunya tasa har zuci baya son auren nan don bazai juri haduwa da mahaifinta yana tuna ranar da ya kama su a mota ba.
Zuciyarsa har neman tafasa take don a yadda yake ji a ransa ko gyada aka dora masa a kan kirji tsaf zata soyu. Ina amfanin dan cikinka ya dauko maka abin kunya. Ba don hoton nan ba sam bazai damu ba idan Saif ya fasa auren Hafsi. Senator Rufai da yake gefe yana kallon abinda ke faruwa a falon yayi dan gyaran murya don ya fuskanci kwata kwata kudinsa da mukaminsa baiyi wa Mal Aminu kwarjini ba. Kallon da ya yiwa Baffan hafsi yasa yayi shiru…malam tun a gidansu munyi magana dasu yaron yace indai ka amince to zai iya hakura da ita. To a wane dalili ne wai zaku mayar dani karamin mutum irin haka? Ko don ba ‘yarka bace shine zaku rinka juya min ita kamar waina. Bakin Baffa har kumfa yake yana magana ba karamin bacin rai ya shiga ba kila kudi senator ya basu shine suke neman yi masa wannan cin kashin. Senator Rufai yayi masa bayanin halin da dansa yake ciki da tsoron karin lalacewarsa sai baffa ya kada baki yace wato lalataccen danka kake so ya shiryu sanadiyarta ko? Idan kuma abin ya faskara ya dora min ita akan turbar lalacewa fa? Haka yayi ta fada karshe yace ni dai gaba daya na fasa bawa kowa Allah Ya hada kowa da rabonsa.
Abin da senator yake ta kokarin boyewa game da jikinsa ne ya faru don kuwa yana tashi kirjinsa ne ya fara ciwo sai jiri ya debeshi ya fadi. Baffa ko kallonsa baiyi ba don a tunaninsa na karya ne tunda yaga kudi bai dauke masa hankali ba. Saif da Alh Bashir kuwa da sauri suka yi kansa Alh Bashir a tsorace yace haba Aminu taimaka mana. Idan mutumin nan ya mutu a gidan nan wallahi duk sai an daure mu ko a yanke mana hukuncin kisa.
*******************
Alh Bashir da Mal Aminu ne tsaye gaban gadon da aka kwantar da Senator Rufai bayan yasa iyalinsa sun dan basu wuri. Da kyar yake maģana yace nasan a dalilina kun sami sabani amma bisa amana zan fada muku sirrina. Hakika duk wata kujerar iko a kasar nan is addictive maana idan aka hau ba’a son sauka indai ba ta sama za a hau ba. Magudin siyasa da hadamar kudin talakawa duk munayi. Ina tsammanin ma shiyasa Allah Yake jarrabarmu da lalurori da kala kala da ‘ya’ya marasa da’a. Yasa hannu ya share hawaye. Ina matukar son Junaid ganinsa nake tamkar mahaifina saboda kamaninsu. Duk abinda ya zama a yau laifina ne saboda yadda na sakar masa yake facaka da kudin talakawan kasar nan. Tun farkon abin mahaifiyarsa ta fara hanawa ni kuma ina ta ganin kamar lokacinsa ne. Maganar tasa sarkewa tayi saboda tari Mal Aminu ya rirrike shi. Sai da abin ya lafa ya cigaba da magana. Muna cikin wani lokaci da yaran da ka tsaya da kyau wurin tarbiyarsu ma baci suke balle wanda aka sakewa. Masifu sunyi mana yawa duk a dalilin nesanta kanmu da mukayi daga Allah da koyarwar Annabi SAW.