TUN KAFIN AURE Page 21 to 30

Mal Aminu ya dan tabe baki don shima sheda ne akan rashin adalcin kasarnan da yadda yake ganin tarbiyar yara yanzu a matsayinsa na malamin sakandire. Ji yayi senator ya rike masa hannu wanda hakan ya dan tsorata shi. Sati biyar kenan da likita ya tabbatar min da cewar inada ciwon zuciya kitse ya lullube ta. Babu wanda na fadawa sai ku biyun nan da na hadu daku a yau. Likitan ya tabbatar min ko dai na cigaba da rayuwar shan magani ko na mutu. Subhanallahi Alh Bashir ya fada.
Batul Mamman????
TUN KAFIN AURE???? 18
Hakika mutuwa abin tsoro ce musamman ga irinmu masu aikata sabo muna sane. Kamar yadda na fada a gidanka Alhaji waazi naji yayi matukar razana ni. Ina tsoron mulki yanzu, ina tsoron kudi, ina tsoron haduwa da Allah akan laifukana sannan ina tsoron samun kamasho daga laifukan Junaid tunda laifina ne abinda yake yi. Akan yarinyar nan ya dawo gida da guduwa yayi. Akan ta yayi min alkawarin shiryuwa shiyasa kaga na dage. Idan har na mutu yana wanan rayuwar kabari zai min kunci. Kuka ne yaci karfin senator sai dai su uku mazan akwai hawaye a idanunsu. A wannan zamani hanyoyin dulmiyar da bayin Allah akwai yawa ga bayyana sabo saboda rashin tsoro. Mal Aminu yace zan amince amma sai anyi masa gwaje gwajen cutuka saboda lafiyar Hafsa. Ko sau daya kada yazo gidana sai na tabbatar da lafiyarsa sannan zaa fara maganar aure. Abu na karshe zamu rubuta yarjejeniya kai Alhaji ka zama shaida duk ranar da ya koma ga miyagun halayensa bayan aurensu kun amince kotu ta raba auren idan yaki shiryuwa. Na yarda na amince kawai senator yake fada. Ba zai iya fada musu mugun mafarkin da yayi yaga kansa cikin wuta yana ta shan azaba ba a dalilin dukiyar da suke wadaka da ita. Abin tamkar gaske ya gani. Mutuwar abokinsa washegarin mafarkin wani wanda yayi gwamna karo biyu sun shiga sun fita ya zama minista shi ya kara tada masa hankali. Gawar abokin nasa bakikkirin kamar an shafa gawayi gashi yaransa suna ta murna harda party ranar da yayi bakwai wai giwa ta fadi. Sosai ya tsorata har baya iya baccin kirki. Uwa uba kuma yaga yadda hukumar kama masu watanda da arzikin kasa su cinye a cikinsu tasa mutane a gaba. Wannan tonon asirin ma na duniya ya ishi bawa mai tsoron Allah.
*******************
Kuka take sosai a daki tunda Baffa ya sanar da ita abinda ke faruwa. Duk gidan al’amarin bai musu dadi ba Mama tana ta mita. Hafsi tayi fushi sosai da Saif da ace wani abu ma ya faru tsakaninsu haka zai fasa auren karshe duk wanda ta aura yaci mata zarafi. Yanzu duk farincikin da take baffa ya yafe mata ashe hoton nan bazai fasa jawo mata sabbin masifu ba kullum.
Ummati ce ta shigo da sallamarta Hafsi ni fa ban gane zancenki ba a waya. Rungume aminiyarta tayi tana kuka tana sake mata bayani. Ummati ta kalleta yanzu shi dan sanatan kin ganshi? Ke wa yake ta tashi ko sunansa ma ban sani ba. Ai kinji dadi Lawal baizo kun yi naku hotunan ba. Wannan hoto bai zo min da komai ba sai sharri. Ummati rarrashinta kawai take tana tuna yadda Allah Yasa ta auna arziki bata riga tayi hoton ba. A da suna wa abin kallon wayewa sai dai yanzu sunyi karatun ta nutsu. Duk wani hani ko umarni a musulunci akwai alkhairi mai kyau a tare da shi.
*******************
Da sassafe Junaid ya tafi asibiti. Sam daren jiya baiyi bacci ba tunda Hajiyan Dangi ta sanar dashi yadda mahaifinsa yayi dasu Baffa. Ya tabbatar ba wani abu Baffan ke tsoro ba sai HIV da sauran dangin cututtukan da ake kamuwa dasu ta wannan hanyoyin.
Batul Mamman????
TUN KAFIN AURE????19
Kwanaki uku kenan tana binsa yanzu ta gama gano gidan da yayi masauki abinda ya rage mata yadda zata sami damar yi masa abinda bazai taba mantawa ba har abada. Idan ka bari motar nan ta bace mana bazan biyaka ba yau…dreban taxi din ya kara gyara mirror din gaban mota yadda zai ganta da kyau. Mace har mace sai dai babu alamun mutumci a tare da ita. Kallonta yake yana hadiyar yawu saboda irin shigar da tayi ta matse dukkan jikinta ga kamshi kamar wadda tayi wanka da turare. A bakin gate din wani asibiti yayi parking inda yaga motar da suke bi ta shiga. Tafiyarta kamar da gayya don ta tada hankalin maza…a zuciyarsa dan tasi Allah Ya isa yayi mata shi ba aure ba kullum yana yawo da ita a gari.
Junaid ya kara kyau saboda shaye shayen da ya dena yan kwanakin nan. Bayan sun gaisa da likitan ya sanar dashi irin tests din yake so ayi masa wanda suka hada da HIV da hepatitis. Haka ya zauna aka debi jinin yasa kida a kunnensa yana jiran result. Ba karamin farinciki yayi ba ganin komai is negative. Tabba ba kowacce mace yake muamala da ita ba kuma yana amfani da hanyoyin kariya amma dai gaskiya ya tsorata. Ana bashi result dinsa wani tsalle yayi da ihun murna. Yana fita Tilly ta fito daga inda ta boya tabi layin ganin likita. Da kyar da salon bugun ciki taji abinda ya kawo Juni asibitin. Allah Ya kama ka Juni boy sai ka gane baka da wayo a hannuna.
******************
Baffa da Mama sun yanke shawarar Hafsi ta tafi gidan kanwar mama dake aure a Funtua har sai yaji makomar Junaid. Haka ta tafi ba musu ita duk abinda zai sa su manta da laifinta na baya nema take shiyasa suka yi shawara da ummati kan cewa bazata musa musu zancen auren dan senator Rufai ba. taso kwarai taga ko waye Junaid dinnan sai ta hakura ganin iyayenta basa yi mata zancensa.
A gajiye Tilly ta shiga gidan aminiyarta Rosie. To mutanen banza daga ina kike tun safe ba hi ko hello. Harara ta galla mata Ke ni bani abinci kizo muyi magana akwai gist fa. Rosie ta washe baki hala kin samo hanyar bi ta kan wannan shegen dan sanatan? Fadi ki kara Tilly ta amsa tana fari da ido. Yanzu dai cikina is empty.
Wata gyatsa tayi me kara sannan tasa kafa ta ture plate din abincin can gefe. Tana sakace hakori tace Rosie yar mutan Gaya kina ji na. Ni da tun dazu na matsu ki gama cin abincin, to ya akayi? Nan ta bata labarin yadda ta bishi asibiti da test din da yayi. Ni bansan me ya faru dashi ba these days amma naga baya zuwa wuraren shakatawa. Da na yanke shawarar na biya doctor din su fada masa yana da HIV to sai nayi tunanin kada yaje wani ya sake aga negative. Tunda ta fara magana Rosie take dan tunani. Ke banza magana fa nake. Ki fada min yadda zanyi ya aureni mu kwashi namu national cake din. Ai ki kwantar da hankalinki sister. Ki bani two months kawai sai muje gidansu. Two months kuma? Yi min bayani mana. No ki bari idan har naga titin da nake so mubi mai billewa ne zaki ji komai. Ke dai ki cigaba da sa ido don mu tabbatar da inda yake ko yaushe.
*******************
Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah. Senator Rufai ya mayarda Alh Bashir wani abokin shawara don har yau Mal Aminu bai gama sakewa dashi ba. Alh Bashir yasha fada masa idan har suka dage zasu iya sawa ya aikata alkhairi a ragowar tenure dinsa. Shi kuwa Junaid a kano ya cigaba da zama wurin Hajiyan Dangi ya rage shaye shaye sosai. Har mamaki yake bai taba ganin Hafsi da idanunsa ba amma sai bin dokoki yake saboda ita kamar wanda aka asirce.
Saura sati uku bikinsa da Hafsi ta dawo kano. Baffa kam sai da yaga result din tests har daga asibitoci biyar ya gamsu tare da bawa Junaid damar yazo ganin Hafsi.